Menene singular da plural?
Kalmar singular ta na nufin abu guda daya tilo. Singular daga kalmar single ta ke. Plural kuma ya na nufin abu mai yawa wato sama da daya, sannan kuma plural akasin singular ne. Misali, idan mu ka ce 'mutum', kowa ya san cewa mu na nufin mutum guda daya. Amma, kuma idan mu ka ce 'mutane' ba sai mun yi wani dogo bayani ba, domin kowa ya san mu na nufin mutum sama da daya, wato daga mutum biyu zuwa abun da ya yi sama.
Sau da yawa daga cikin dalibai za ka samu, wasu su kan yi kuskure wajen rubuta sunan abu mai yawa da kuma guda daya musamman a turanci. Wannan ya na faruwa ne saboda rashin sanin ka'idar abun tare kuma da mantuwa wasu lokutan.
Ka karanta darasin menene Noun?
Mafi yawa daga cikin kalmomin turanci idan ka na so ka rubuta sunansu na abu mai yawa (plural) za ka ga ana kara 's' ko 'es' ko 'ies' ko 'ves' ko 'a' ko kuma 'i' a karshensu. Wasu kalmomin kuma harufan tsakiyansu ake cirewa a musanyasu da wasu. Misali, akwai inda ake cire 'oo' sai a maye gurbinsu da 'ee' da kuma 'a' a maye gurbinsa da 'e' da dai makamantansu.
Dalibai da dama musamman na secondary su na tunanin cewa kowace kalma 's' ko 'es' ko 'ies' ake kara mata idan ana so a canzata daga sunan kalma daya zuwa masu yawa. Saboda mafi yawa an fi amfani da kalmomin da su ke karewa da 's' ko 'es' ko 'ies' a matakin su, to akwai wasu kalmomin wadanda ba 's' ko 'es' ko 'ies' ake kara musu ba, kuma bayaninsu ya na nan zuwa a kasa.
Shin ka san menene Pronoun?
Idan Allah ya so, za mu yi bayani tare da bayar da misalansu daya bayan daya daidai gwargwadon hali.
1. Akwai wasu kalmomi wadanda 's' ko 'es' ake karawa a karshensu, idan ana so a canza sunansu daga daya zuwa sunan abu mai yawa, kaman a ce tsuntsu (daya), tsuntsaye (masu yawa).
Misalin wadannan shine 'bird' wato tsuntsu, ka na kara 's' a karshen sunan, kalmar za ta dawo 'birds' wato tsuntsaye. Sauran misalan su ne 'cup' idan ka kara 's' sunan zai zama 'cups' wato kofuna kenan, 'cap' wato hula 'caps' kuma huluna, 'ball' kuma kwallo, sunanta zai koma 'balls' wato kwallaye, 'phone' kuma waya 'phones' kuma wayoyi, 'tin' kuma gwangwani, 'tins' kuma gwangwanaye.
Ko ka san yanda ake amfani da IS da ARE?
2. Sai kuma kalmomin da ake kara musu 'es' a karshensu. Idan ka ga kalma ta kare da daya daga cikin wadannan harufan 'e' ko 'ch' ko 'sh' ko 'x' dukkansu 'es' ake kara musu a karshensu.
Misali, kalmar 'bench' idan aka kara 'es' za ta koma 'benches', hakama kalmar 'box' idan aka kara mata 'es' za ta zama 'boxes', ko 'patch' zai koma 'patches' sai 'brush' ya koma 'brushes', sai 'bush' ya koma 'bushes', sannan 'force' ya koma 'forces', da 'ox' ya koma 'oxes' da kuma 'witch' zai koma 'witches' da sauransu.
3. Sai kuma kalmomin da ake kara musu 'ies'. Idan kalma ta kare da harafin 'y' a nan harafin 'y' din ake cirewa, sai a rubuta 'ies'.
Misali , kalmar 'lazy' za ta koma lazies', kalmar 'daddy' za ta koma 'daddies', sai 'berry' ta koma 'berries' sannan 'puppy' ta koma 'puppies' sai 'candy' ta koma 'candies', sai 'fry' ta koma 'fries' da sauransu.
Ga karin bayani game da plural din wasu kalmomin
Wajen da ake amfani da 's' shine ana la'akari da harufa biyu na karshen kalma. Misali, kalmar 'boy' harufa biyu na karshe su ne 'oy' abun duba a nan shine harafin farko wato 'o' wasaline (vowel), sai kuma na karshen wato 'y' bakine (consonant). Idan da za a ce 'y' din ne a farko sannan 'o' din a karshe, to 'es' za a karawa kalmar, wato 'byo' zai zama 'byoes' kenan. Amma wannan kalmar 'byo' din misaline mu ka yi da ita - a gaske ni dai ban san wannan kalmar ba.
Idan kuma daga cikin harufa biyu na karshen kalma, harafin farko ya zamo wasali (a, i, e, o, u) ne sannan harafin 'y' ya zo a gaban sa, misali 'day' to ba a cire 'y' din a ce za a saka 'ies' sai dai a rubuta 's' din kadai a gaban kalmar wato 'days' - ga wasu misalan 'bay' ba a rubuta 'baies' ko kuma 'way' asa 'waies', ko 'hay' asa 'haies' sai dai asa 's' din kadai wato 'bays' da 'ways' da kuma 'hays'.
4. Sai kuma kalmomin da ake kara masu 'ves' a karshensu. Kalmomin da sunan su ya ke karewa da harafin 'f' ko 'fe' ana cire wannan 'f' ko 'fe' din sai a maye gurbinsu da 'ves'.
Misali, kalmar 'self' za ta koma 'selves', hakama kalmar 'shelfe' za ta koma 'shelves', sannan kuma 'sheaf' zai koma 'sheaves' da sauransu.
5. Sai kuma wadanda ake kara masu 'a' yawanci kalmomin da su ka kare da 'um' kawai 's' ake kara musu a karshe, ko kuma a cire 'um' din a saka 'a' a karshen su domin a canzasu zuwa plural.
Misalin wadannan kalmomin su ne spectrum zai koma 'spectra' ko 'spectrums', sai kuma momentum ya koma 'momenta' ko 'momentums, sai kuma crematorium ya koma 'crematoria' ko 'crematoriums' sannan 'quantum' ya koma 'quanta' ko 'quantums' da sauransu.
Sannan ana iya rubuta plural din kalmomin da su ka kare da 'um' ta hanyar rubuta 's' a karshensu ko kuma a goge 'um' din karshensu sai a rubuta 'a' a wajen, kaman yanda mu ka yi misali a sama wato 'quantum', ya koma 'quantums', ko 'quanta'. Duk wanda ka yi amfani da shi babu komai, sai dai gwanayen turanci sun fi amfani da 'a' a maimakon su rubuta 's'.
6. Sai kuma kalmomin da ake saka musu 'i'. Kalmomin da su ke karewa da 'us' wani lokacin 'es' ake kara mu su a karshensu, kaman 'bus' za ta koma 'buses'. Sai dai wasu kalmomin kuma 'us' din ake cirewa sai a saka harafin 'i' maimakon 'us' din.
Misali, kaman kalmar 'fungus' za ta koma 'fungi', sai kalmar 'radius' za ta koma 'radii', sai 'nucleus' za ta koma 'nuclei' da sauransu.
7. Sai kuma wadanda ake canza harufan tsakiyansu. 'Tooth' hakori ake rubutawa, bawai 'toothes' ko 'tooths' ake rubutawa ba. Abun da ake yi a nan shine sai a canza harufan tsakiyan kalman.
Misali, kalmar 'tooth' za ta koma 'teeth' ko kuma 'goose' ta koma 'geese'. Sai kuma 'man'. Idan ka rubuta 'mans' ka yi kuskure, sai dai ka rubuta 'men', hakama kalmar 'woman' za ta koma 'women'. Amma idan ka rubuta 'womans' to ka yi kuskure.
8. Akwai wasu kalmomin kuma su ba a canza ko da harafi daya ne ajikin su, idan za a canzasu daga singular zuwa plural. Saboda su ba sa zuwa guda daya sai dai bibbiyu ko sama da haka. Saboda haka sai dai a yi amfani da wasu kalmomi wadanda su ke nuna cewa wannan abun ba guda daya bane. Kalmomin da ake amfani da su a nan su ne some, da piece, da few, da several, da much, da many da makamantan su.
Kalmomi kaman Scissors, shoes, da trousers, da pliers, da banns, da kuma news misalai ne na kalmomin da ba'a canza komai ajikin harufan su, sai dai ayi amfani da daya daga cikin kalmomin da muka bayar a sama. Idan mutum ya rubuta scissorses ko trousers ko plierses to yayi kuskure - sai dai yayi amfani da kalmomi masu nuna adadin abu. Misali some trousers, ko few scissors ko dayake dayan angane.
Bari mu tsaya anan da fatan ana fahimtar darusan da muke rubutawa a shafin nan. Ga wasu tambayoyi guda biyar da muke bukatan amsoshinsu daga wajenku. Sai ku yi comment da amsarku a wajen comment dake kasa. Idan kuma kuna da tambaya kuna iyayinta, idan mun sani zaku samu amsa insha Allahu.
1. Rug
2. Cub
3. Neutron
4. Millennium
5. Fog
Sannan daga karshe kuma muna fatan zamu sake ganinku a shafin nan. Mun gode, ahuta lafiya! Muna jiran amsa daga gareku.

Leave a Comment