Yanda ake aiki da Photomath
Darasin lissafi wato Maths, darasi ne mai wahalar gaske. Lissafi yana da wahala da kuma rikitarwa ga dalibai. Mafi yawan dalibai wannan darasin ya na basu wahala. Saboda rashin fahintar dokoki da ka'idodinsa. Maths darasi ne mai mahimmancin gaske ga dalibin ilimi.
Kasantuwar wayoyi zun zama abokan aiki ga mutane a yau, saboda haka su kan taimakawa mutane wajen saukaka musu wasu aiyukansu na yau da kullum. Hakama wayoyi sun zama abokan karatu ga dalibai domin yin karatu. Littattafai masu yawa yanzu anyi wadanda ake tafiyar da su a cikin wayoyin zamani.
Photomath application ne wanda ake amfani da shi wajen samun amsar tambayoyin lissafi. Bawai maths kadai ba hatta physics da chemistry ana amfani da shi domin samun amsar tambayoyinsu. Photomath ya na bada amsar tambayoyin lissafi dayawa a cikin lokaci kadan, kuma ya na bin ka'idar lissafi wajen bayar da amsar tambaya.
Photomath kyauta ake saukar dashi da kuma tafiyar da shi. Ya na aiki akan wayoyi masu version daga 4 zuwa abun da yayi sama. Photomath ba ya bukatan wani dogo bayani ga dalibi da mai karatu akan yanda ake aiki da shi. Wannan application din ya na taimakawa dalibi wajen amsa tambaya a cikin kankanin lokaci.
Wani abun mamaki ga photomath shine da camera za ka yi aiki ka dauki hoton tambayar lissafi. Shi kuma zai ba ka amsar abun da ka dauka nan take. Yanda akeyi shine za ka rubuta tambayarka a cikin littafi ko bango sai ka shiga application din ka daidai ta cameran wayar a daidai kan wannan tambayar da ka rubuta application din da kansa zai rubuta maka amsa.

Saukar da photomath
1. Photomath ga masu Android.
2. Photomath ga masu iPhone da iPad.
Ya ya ake aiki da Photomath?
Photomath yana da sauki da saurin koya ga wanda bai taba aiki dashi ba. Domin nuna yanda ake aiki da shi, na rubuta wasu lissafi guda biyar a littafina, sannan na dauki hotonsu, na yi amfani da wannan application din na samu amsoshinsu. Tambayoyin sune kaman haka:
1. 2x+7=17
2. sin(20)
3. x=√9
4. 24²+50=
5. 2x+6=10

Wadannan tambayoyin guda biyar za mu yi amfani da photomath mu samo amsoshinsu.
1. Tambaya ta farko x ya na daidai da 5, wato idan muka sa 5 a maimakon x a cikin tambayar zai kama 2(5)+7=17. Wato biyu sau biyar ya kama goma. Sannan goma a tara da bakwai amsar ta zama goma sha bakwai kenan. To x ya na zaman biyar kenan a tambayan nan. Wannan matakin shi ake bi domin gano amsar lissafi ta hanyar ka'idar BODMAS.

2. Amsar tambaya ta biyu kuma ita ce 0.3420 idan ka yi amfani da scientific calculator ko statistical table. Amma 0.912945 kuskurene na application din. Sine na 20 shine 0.3420, anan photomath ya bada amsa ba daidai ba - watakila ko dai rubutun nawane bai futo yanda ya kamataba.

3. Amsar tambaya ta uku ita ce 3. Square root ya na nufin wace lambace idan aka ribanyata da irinta za ta bayar da lambar da aka rubuta a cikinsa, mun yi misali da 9. Shine mu ka ce uku sau uku, amsar mu za ta kama tara ce.

4. Amsar tambaya ta hudu ita ce 626. Saboda 24² ya na nufin ashirin da hudu sau ashirin da hudu - wato ya kama dari biyar da saba'in da shida 576. Idan aka tara hamsin tare da dari biyar da saba'in da shida, amsar za ta kama dari shida da ashirin da shida wato 626.

5. Sai kuma amsar karshe wato inda x yake daidai da 2. Biyu sau biyu ya kama hudu. To hudu a tara da shida amsar za ta kama goma.

Wannan kadan kenan daga cikin aiyukan da wannan application din ya ke yi. Photomath ya na aiki da sauri kuma ya na bayar da amsa daidai. Amma wani lokacin ya kan bayar da amsa ba daidai ba. Wannan ya na faruwa ne wani lokacin saboda rashin gane me aka rubuta.
Idan za ka yi aiki da wannan application din ka tabbata ka rubuta tambayarka yanda kowai zai ganewa ya fahinci tambayar. Saboda rashin yin rubutu mai kyau ya na kawo application din ya kasa fahintar tambayarka - balle ma ya baka amsa.
Bayan haka kuma application din nan akwai calculator a cikinsa wanda zai taimaka wa dalibi a lokacin yin lissafi. Akwai wasu application masu yawa domin dalibai a kowane fanni na ilimi. Za ka samesu mafi yawa kyauta ake saukar da su ayi amfani da su duk a kyauta.
Za mu dakata a nan sai kuma wani darasin. Amma kafin sannan ya kamata a sani Photomath application ne wanda ake amfani da shi ayi lissafi ta hanyar daukan hoton rubutu akan littafi, kuma ya na zuwa da calculator dan yin lissafi da kanka. Mun gode da kawo ziyara wannan shafin a huta lafiya! ;)

Leave a Comment