Mu koyi lissafi 01 (mathematics)

Ba wai dalibai kadai ba, za ka samu wasu mutanen ko dubu nawa ka ba su su na iya lissafa ma daidai babu kuskure ko kadan. Amma idan kuma aka zo lissafi a rubuce za ka ga sun kasa tabuka komai, ko kuma za samu kurakurai masu a cikin rubutun lissafin. Kuma bawai dan ba su iya lissafi bane, matsalarsu ita ce ba su san ka'idojin lissafinba.

Lissafi (mathematics) abu ne mai sauki ga wanda Allah ya albarkace shi baiwa a fannin. Ilimin kimiyya da fasaha ya na tafiyane tare da lissafi ko kuma ace shine ma jigonsu. Akwai ka'idoji da akan bi kafin a lissafa kowane irin lissafi, wanda a nan hatta dalibai ma su kan wahala kafin su samu nasara, yayin da wasun su sukan fadi ko da a lokacin jarrabawane.

Ka'idojin hadawa (+) da cirewa (-)

Kaman yanda bayani ya gabata a sama akwai ka'idoji da ake bi da wasu hanyoyi kafin ayi wani lissafi. Ka'idar farko da za mu fara bayani da misali akanta ita ce alamomi (signs). Wani lokaci za ka samu a cikin lissafi akwai lambobi da za ka gani an baka akwai lamba mai alamar cirewa wato negative sign (-), da kuma mai alamar kari wato positive sign(+), sannan ace ka yi lissafi da su ka gano amsar wannan tambayar.

Ga yanda ake yi:

1. Alamar cirewa wato negative sign (-) ana rubuta ta daga bangaren hannun hagu, wato sai an rubuta ta sannan ake rubuta lamba, wato za a fara rubuta 'minus' sannan a rubuta lamba a gabansa. Misali, -2, ko -7, ko -3, ko -9, ko -4 da sauransu.

2. Haka ita alamar kari wato positive sign (+) ana rubuta ta daga bangaren hannun hagu, wato sai an saka ta sannan ake rubuta lamba, ma'ana za a fara rubuta 'plus' sannan a rubuta lamba a gabansa. Misali, +9, ko +5, ko +2, ko +1, ko +7 da sauransu. Wadannan alamomin guda biyu su na da alaka sosai a lissafi, domin daya ya na iya zama dayan - hakama dayan ya kan iya zama dayan, wato negative zai zama positive, shima positive zai koma negative, idan su ka tsallake equal sign.

Misali, idan aka ce ka rubuta lamba shida negative, sai ka rubuta -6, ko kuma lamba shida positive, sai ka rubuta +6 ka na rubuta haka ka gama. Sauran misalan su ne ga negative na lamba bakwai -7, ko negative na lamba goma sha biyu -12, ko positive na lamba daya +1 da kuma positive na lamba takwas +8.

Kowace lamba ka na dakkota kawai alamar positive ko negative za ka rubuta a bangaren hagu. Sanin wannan ka'idar zai taimakama wajen warware matsalolin lissafi, ya na da kyau a sani kowace lamba ana samata alamar positive ko negative, misali +350 ko -350, da +5000 ko -5000, da +6100 ko -6100, da +7760 ko -7760 da sauransu.

Wai shin alamar negative ko positive me su ke idan aka rubutasu a jikin lamba?

A ka'idar lissafi duk inda ka ga an rubuta lamba kuma jikinta akwai negative sign to ana nufin kaman ana bin bashin adadin wannan lambar. Misali, idan ka ga an rubuta -8, to ana nufin cewa ana bin bashin takwas. Kenan sai an samo wata takwas din ko lambar da tafi takwas din sannan a biya wannan bashin.

Amma a nan takwas din da za a nemo mai positive ce wato +8. Ya na da kyau a sani cewa indai lamba positive ce ta zo a farko ita ba a rubuta wannan sign na positive din, wato ba sai an rubuta '+' sannan ake rubuta 8 ba, kawai 8 din shi kadai ake rubutawa.

Misali:

1. Bari mu lissafa -4+7=?, Watakila mutane da yawa za su rikice wasu su ce 11 ne amsa, wasu kuma su ce -11 ne amsa. Amma kuma ba 11 ko - 11 bane amsa, dalili shine bayani ya gabata a sama cewa duk lambar da aka samata negative to ana bin bashin daidai adadin wannan lambar. To a misalin nan na sama kaine ake binka bashin Naira hudu, sai ka yi aiki ka samo Naira bakwai. Shin idan ka biya bashin Naira hudu, nawane zai rage a cikin Naira bakwai? To wannan daidai ya ke da -4+7=3.

2. Ka'ida ta biyu kuma idan dukka lambobin negative ne kaman haka: -5+-9=?, ga yanda ake lissafasu. Kafin mu yi nisa ya na da kyau a sani cewa a lissafi ba a jera operation guda biyu a waje daya, ma'ana ba a jera + da - ko × da ÷ sai dai lamba ta biyun a rubuta ta a cikin bracket tare da sign dinta. Idan an fahimci wannan dokar, to lissafin zai tashi daga -5+-9=?, zai koma -5+(-9)=?.

Idan anfahimci bayanin da ya gabata a sama, wannan amsar za ta zama -14. Domin kaine ake binka bashin Naira biyar, kuma ba ka biya ba, sai ka sake ciyo bashin Naira tara, ka hadasu ka ga idan aka tarasu zai zama ana binka bashin Naira goma sha hudu. Wannan lissafinma haka ya ke -5+(-9)=-14.

Bari mu gani idan ana ganewa, a rubuta amsoshin wadannan lissafin a wajen comment da ya ke kasa. Ya na da kyau mutum ya amsa wanda ya ga zai iya amsawa daga cikin tambayoyi biyar dinnan masu zuwa a kasa.

(1) 20+(-12)=?
(2) -2+(-8)=?
(3) -4+54=?
(4) 70-7=?
(5) 90+35=?
(6) -5+(-85)=?
(7) 16+14=?
.

Alhamdulillah, cikin ikon Allah darasin farko ya kammala akan yanda ake koyan lissafi (maths). A cikin wannan darasin mun dan yi wasu bayanai tare da misalai game hadawa (addition) da cirewa (subtraction).

To jama'a sai a yi hakuri bisa kuskuren da za a iya samu a cikin darasin nan da sauran darusan, domin ni dan Adam ne mai kuskure, kuma dalibi, dolene wani lokaci za a samu kuskure a cikin aiyukana. Daga karshe kuma idan an ga wani kuskure, ya na da kyau a yi kokarin gyara mana ta hanyar rubutashi a wajen comment da ke kasa. Mun gode, sai mun sake ganinku.

2 comments:

  1. Mungane sosai ALLAH sakama da alkairi

    ReplyDelete
  2. (1). 20+(-18)=12
    (2). -2+(-8)=10
    (3). -4+54=50
    (4). 70-7=63
    (5). 90+35=125
    (6). -5+(85)=90
    (7). 16+14=30

    ReplyDelete

Powered by Blogger.