Menene tauraro (star)?
Sararin samaniya ta na dauke da biliyoyi ko triliyoyin taurari sheki, da kyalli wadanda Allah Madaukakine kadai ya san adadinsu. Taurari su ne su ke kyalli, tare da haska cikin sararin samaniya. Sannan taurari ado ne ga sararin samaniya, hakama babbar ni'imace ga rayuwar dan Adam, da shi kansa.
Menene tauraro, da kuma amfaninsa a cikin sarari?
Tauraro shine wani abu mai matukar girma a cikin sarari mai siffar kwallo, wanda ya ke futar da haske tare da zafi daga cikinsa. Zafi ya na samuwa daga cikin tauraro ta nuclear reaction din da ake kira nuclear fusion. Nuclear fusion kuma reaction ne wanda a cikinsa kananun nucleus guda biyu su ke haduwa su samar da nucleus babba guda daya.
Shin ko ka karanta bayanin ya ya saurin duniyar Earth ya ke?
Tauraro shine ya ke rike da planet din da su ke kewaye da shi ta hanyar karfin gravity wanda ido ba ya iya ganinsa. Tsakanin taurari akwai tazara mai nisan gaske, kuma ana auna tazarar nisan da ta ke tsakaninsu da light-year. Light-year shine tsawon nisan tafiyar da haske ya ke yi a cikin shekara daya. Haske ya na yin tafiyar kilomita dubu dari uku a cikin second daya (300, 000kmph). Tsakanin rana da tauraro mafi kusa da ita wato Betelgeuse, akwai nisan light-year dari bakwai (700 light-years).
Shin ko ka karanta bayanin ya ya saurin haske ya ke?
Nuclear reaction din da ya ke faruwa a cikin tauraro ya na faruwa a can tsakiyarsa inda ake kira core. Kuma kananun nucleus din Hydrogen ne guda biyu wato da Hydrogen-2 (²H) da Hydrogen-3 (³H) ne su ke haduwa su samar da nucleus din Helium (⁴He) guda daya.
Shin ko ka karanta bayanin menene exoplanet?
Misalin tauraro wanda kowa ya sani shine rana. Rana ita ce tauraro mafi kusa da mu, sannan kuma ita ta ke dauke da solar system gaba dayansa - domin ita ta ke samar da karfin gravity, da karfin maganadisu (magnet), da kuma zafi da haske ga duniyoyin solar system.
Za mu tsaya a nan da fatan a na amfanuwa da rubuce rubucen da ake karantawa a shafin nan. Duk mai tambaya sai ya yi kasa wajen comment ya rubutu, zai samu amsar tambayarsa idan Allah ya sa mun sani.
Mu na godiya a bisa ziyarar da ku ke kawowa shafin nan, mu na fatan sa ke ganinku tare da abokanku a shafukan sada zumunta na internet, a huta lafiya, sai mun sa ke ganinku.

Leave a Comment