Menene Wi-Fi (wireless)?
Fasahar zamani ta kawo ci gaba, da canje canjen a harkokin yau da kullum. Sannan kuma lokaci bayan lokaci fasaha ta kan kara habaka. Yawaitar na'urorin tafi-da-gidanka a hannun mutane ya kawo sauki ga jama'ar duniya baki daya. A yanzu akwai abubuwan da basa bukatar a jona wayar lantarki a tsakaninsu kafin a sadar da su. Akwai earpiece wanda baya bukatar wayar lantarki domin sauraron wake wake da kade kade a wayar hannu ko computer. Ta hanyar Wi-Fi ana iya shiga internet ko da a cikin waya ko computer babu SIM Card ko Modem.
Menene Wi-Fi?
Wi-Fi sunan fasahar sadarwar zamanice wacce bata bukatar wayar lantarki a tsakanin na'urori (wireless). Wannan fasahar sadarwan wacce bata bukatar wayar lantarki domin sadarwa ta na amfanine da sadarwa Radio waves, wato hasken da ba ma iya ganinsa da idonmu. Sannan kuma sadarwar Wi-Fi tanada matukar sauri domin kawo sadarwar internet da sauran network.
Sannan kuma Wi-Fi ya na nufi wireless Fidelity - a saukake kalmar Wi-Fi ta na nufin tambari ko hatimin kasuwanci na cibiyar injiniyoyin lantarki ne wato Institute of Electrical and Electronic Engineers (IEEE a takaice).
Yaya Wi-Fi Yake Aiki
Kaman dai yanda bayani ya gabata a sama mun ce Wi-Fi hanyar sadarwace wacce ba ta bukatar waya ko igiyar lantarki ta sadarwa. Idan mu ka duba shekarun baya za mu ga cewa jama'a sun yi amfani ta harto ☎ (telephone) domin magana 'yan uwan uwansu na nesa. Tarho ya taka muhimmiyar rawa a bangaren sadarwa - sannan kuma za ka ga jikin tarhon akwai wata waya da aka saka masa wacce ita ce ta ke kawo masa sadarwa tsakaninsa da wanda ya ke magana da su na kusa ko na nesa.
Akwai abunda ake kira antenna. Misalin antenna shine a jikin rediyo (radio) ko talabijin📺 (television) za ka ga wani karfe mai tsayi wanda ake jawoshi ya yi sama idan za a kama tasha a rediyo ko a talabijin. Antenna ta na aiyuka guda biyu - aiki na farko shine aika sakon sadarwa zuwa cikin iska (transmission), aiki na biyu kuma shine karban sakon sadarwa (receiving) daga cikin iska zuwa cikin akwatin rediyo ko talabijin.
To su ma na'urorin da su ke sadarwa a tsakaninsu ta hanyar Wi-Fi su na amfani da antenna domin sadarwa a tsakaninsu. Kasancewa Wi-Fi sadarwace mai gajeren zango, wato iya nisan da ake iya karban sakon a takaice ya ke, shiyasa ake kera na'urorin da antenna mara tsayi. Kuma antennar tana cikin na'urorin yanda ba a iya ganinsu a waje.


Leave a Comment