Mene ne Application?

Na'ura mai kwakwalwa ta zamo babba abokiya huldar mutane a harkokinsu na yau da kullum. Kuma ba komai bane ya sa ta zamo abokiyar huldar mutane face application din dake cikinta.
Domin wadannan application dake cikinta suke taimakamata wajen tafiyar da harkokin al'umma a cikinta. Akwai dimbin application a cikin waya da na'ura mai kwakwalwa wadanda wasunsu akan iya fahimtar aikinsu - wasunsu kuma akasin haka.

Shin ka karanta menene manhajar iOS ta iPhone da iPad?

Muna iya cewa kowane bangaren na computer ko waya akwai application din dake tafiyar da shi. A wayoyin zamani kaman iPhone da Android akwai application din da aikinsu shine yin kira, akwai wadanda aika sakonnine aikinsu, akwai wadanda sarrafa media files ne aikinsu wadannan su ake kira file manager da makamantansu. Amma shin ko ka san hakikanin menene ma'anar application?

Menene application?

Application wata fasaha da aka tsarata domin domin tayi aiki a cikin na'ura mai kwakwalwa. Wannan fasaha bangarece da ake kira computer software, wato ita ba a ganinta - sai dai ayi aiki da ita a cikin waya ko na'ura mai kwakwalwa. A takaice idan babu application ba a iya sarrafa waya ko na'ura mai kwakwalwa, domin suke bada umarni ga asalin fasahar na'ura ko waya wacce ake kira operating system.

Application ta hanyar sune muke sarrafa computer da wayoyinmu. Domin duk aikin da zamu yi da na'urorinmu cikinsu muke shiga su kuma su aiwatar mana da wannan aiki. Misali, idan zaka yi kira da wayarka, application dadamane suke taka muhimmiyar rawa - akwai application din da ta hanyarsa kake shigar da lambobi a waya - kuma akwai application din da shike aijeyama lambobin - sai kuma application din dake aiwatar da kiran da kayi.

Me ka sani game da Android 10, wato sabon version din Android?

Sannan akwai application din dake sanar da kai idan ankiraka - sannan ya baka daman karban wannan kiran. To ka ga kenan idan babu application ba waya. Idan kuma zaka saurari sauti ko kallon bidiyo da ganin hoto - akwai file manager wadanda zasu nemoma wadannan din sannan kuma sai player wadanda ta cikinsu ake gani ko sauraren wadannan media.

Me ka sani game da fasahar Android OS, wato fasahar wayar Android?

Kaman yanda muka sani kowace waya akwai wadannan application din wato Call, da Phone, Messages, da Settings, da Gallery, da Keyboard, da File manager, da Clock, da Calendar, da Multimedia da sauransu. Idan ka samu waya babu wadannan application din to wannan wayar bata amsa sunan waya, sai dai wata na'urar.

Shin ka karanta bayanin mecece fasahar network din 5G?

1. Call:

Bangaren kira akwai application dadama da aka tanada a App store da Play store domin kira da karban kiraye-kiraye. A lokacin da za ka yi kira - application mai suna phone shi zai baka daman shigar da lambobi da kuma ajiyesu a cikin wayarka. Sannan ta hanyarsa zaka gano lambar wayar da za ka kira.

2. Phone:

Phone kuma application ne da ake shigar da lambobin waya da ake kira ta cikinsa. Phone kuma application ne da ya kunshi wajen shigar da lambobin waya da kuma phone book wato rumbun adana lambobin waya.

3. Messages:

Message kuma application ne da ta cikinsa ake rubuta sakonni, kuma a turasu - kuma ta cikinsa ake karbansu. Bayan nan kuma akwai bangaren da zai baka daman turawa da karban sakonin hotuna da murya.

4. Settings:

Settings kuma application ne da ake seta kusan duk wata matsalar da ta shafi wayar. Kowace waya tanada wannan application din kuma aikinsa ya shafi kusan ko ina a wayar.

5. Gallery:

Gallery kuma application ne ake ganin hotuna da bidiyoyi a cikinsa, kuma ya na zuwa a cikin kowace waya - sannan akwai wadanda aka tanada na musamman a App store da Play store.

6. Keyboard:

Keyboard kuma hardware ce da aka tsara a matsayin application, wanda amfaninsa daya da allon madannin computer. Keyboard amfaninsa shine yin rubutu - kaman rubuta sakonnin harufa da lambobi a waya ko a computer.

7. File manager:

File manager shine application din dake baka daman ka sarrafa file din cikin wayarka. File manager shike baka damar canzawa file suna (rename) ko gogewa (delete) da sauran aiyukansa.

8. Clock:

Clock kuma ba sai mun yi bayanin saba. Saboda shine agogo - agogo kuma kowa ya san amfaninsa shine ganin lokaci da kwanan wata. Bayan nan kuma agoguna dadama sukan zo da alarm, wato kararrawar dake tunatar da mutum a lokacin da aka setata.

9. Calendar:

Calendar ma bata bukatar wani dogon jawabi - amfaninta shine ganin kwanan wata da kuma sanin rana da lokaci.

10. Multimedia:

Multimedia kuma application ne da ake bude bidiyoyi da hotuna da kade-kaden cikin waya. Akwai application din media dadama a App store da Play store domin amfanin mai da wayar Android ko iPhone ko kuma na'urar iPad.

Ban da wadannan application din da muka kawo a sama akwai wasu application da ake wasu amfanin dasu. Akwai application kaman Chrome da Opera wadanda ake aiki da su domin shiga internet - akwai Camera wacce ake amfani da wajen daukan hoto da bidiyo - akwai Bluetooth wanda yake bada dama ayi musayar file din cikin waya tsakanin wayoyi biyu, ko kuma sauraron wake-wake da kade-kade da shi.

Ta hanyar application ake sarrafa wayoyi - kuma kowace waya akwaisu sai dai aiyukansu sun bambanta. Zamu dakata da bayanin haka da fatan ana amfanuwa da darusan fasaha da ake karantawa a shafin.

Sannan kuna iya tura wannan darasin a Facebook da Twitter domin abokanku dake can su gani su shigo su karanta. Muna godiya da ziyartar shafin nan da kukeyi mun gode a huta lafiya.

No comments

Powered by Blogger.