Menene rooting da kuma amfaninsa ga wayar Android?

Na'urorin zamani su na da wasu bangarori wadanda su ke wahalar na'urorin baya wajen tafiyar da su, wasu tsofaffafin na'urorin ma ba sa iya tafiyar da wadannan sabbin bangarorin. Duba da yanayin tsarin da aka yi musu sama da na na'urorin baya.

Mu duba wayar Symbian za ka samu akwai wasu application wadanda ba ta iya budesu har sai an yi hacking din ta. Domin su application din an yi su da sabuwar fasaha ta zamani, ita kuma wayar ta na tafiya akan tsohuwar fasaha. Ka ga kenan dole a samu cikas wajen aiki da irin wadancan application din akan wayar.

Amma idan aka yi mata hacking, hakan zai buda mata kwakwalwa ta zamo ta na iya tafiyar da irin wadancan application din cikin sauki kaman yanda ta ke tafiyar da tsofin application din ta. Ita kanta computer ana mata irin wannan dabara ko buda kwakwalwa, ta koma ta na bude softwaren da ba ta iya budewa a doka.

To rooting shima haka ya ke ga wayar Android. Waya mai version 4 ta koma ta na bude application ko game na waya mai version 5 ko 6. Hatta su ma wayoyi masu manyan version kaman 5 da 6 da 7 ana yi musu rooting. Domin a yi aiki da wasu application akan su.

Menene rooting?
Rooting hanyace da ake amfani da ita ba bisa ka'ida ba wajen budewa da fadada kwakwalwar waya. Kuma ya na da amfani ga wayar sosai hakama ya na da illa tafutar hankali ga waya. Kaman yanda duk abun da ya ke da amfani za ka samu ya na da tasa illar shima rooting haka ya ke.

Amfanonin rooting
1. Rooting zai ba ka dama ka more wasu application din da dole sai da kudi ake yin wasu abubuwa da su, da rooting kyauta za ka moresu.

2. Rooting zai ba ka dama ka canza version na wayarka, daga karamin version zuwa babban version, ko mu ce daga tsohon version zuwa sabon version, ba tare da ka yi amfani da computer ba.

3. Da rooting ana iya hacking din wasu application da game a waya domin samun wani score da coins.

4. Ana iya hacking na lasisin application domin a more wasu game da application a kyauta. Wadanda a baya sai da kudi ake iya yin su, amma sanadin rooting za ka yi su kyauta.

Illolin rooting
1. Rooting ya na da muguwar illa ga waya wanda zai jagoranceka zuwa asarar manhajar wayarka gaba daya.

2. Rooting zai ba ka daman tafiyar da wasu application da su ke da hadari ga waya.

3. Rooting ya na bada dama waya ta yi wasu abubuwan da su ka sabawa tsarin da aka yi ta akai wanda saba musu zai sa ta samu matsala.

4. Akwai wasu illolin da rooting ya ke yi amma ba za ka sani ba har sai ka yiwa wayarka za ka ga haka.

Rooting ya na da amfani idan kasan shi, kuma ka iya tafiyar da waya, sai dai shawarar dazan baka kada ka sake ka yiwa wayar da ka ke aiki da ita. Gwara ka samu wata waya wanda ka ke wasu harkokin da ita kaman wanda ka ke game da ita sai ka yi mata rooting ko da an samu matsala daman ba da ita ka ke kira ba.

Nan shine karshen bayani akan menene rooting da amfaninsa da kuma illolinsa. Fatan ana gane abun da mu ke rubutawa. Ku na iya yin sharhi game da darusan da mu ke rubutawa a wajen comment da ke kasa. Mun gode.

No comments

Powered by Blogger.