Menene Google AdSense?
Kasancewa yanzu amfani da internet yazama ruwan dare, wato ko ina anayin shi. Hatta kananun wayoyi a yau suma ba'a barsu a baya ba wajen amfani da internet. Ba birni ba kauye ana amfani da internet - kenan yazamo abun da ake amfani dashi a karkara da maraya.
Duba da cewa mutane sun dawo da wasu harkoki masu mahimmaci internet yasa aketa fada tashi domin nemo hanyar samun kudi dashi. Harkoki masu mahimmaci da masu hali sukeyi sun koma internet. Ana neman abubuwa da dama a internet wadanda a shekarun baya abun ba haka yake ba.
Idan muka duba a duniyar yau tanadin tikikin tafiya na jirgin sama, da neman gurbin karatu a jami'o'in kasashen waje musamman kasashen turai da Amurka, hatta neman izinin zama a wata kasa ana iya nema a internet. Kasuwanci da tallace tallace hanyoyine da ake samun kudi a cikin harkokin yau da kullum.
Duniyar yau mutum zai iya karatu yayi nisa har yasamu shedar kammala karatu na jami'a duk a internet, wannan duk yana faruwa ne sanadiyar cigaba da habakar da fasahar internet tayi ne. To a sanadin haka yasa akai ta kokori domin ganin ana samun kudin shiga da internet.
Wannan yasa mutane suke yawan tambaya wai shin tayaya zasu samu kudi ta internet ne? Ko dayake abaya mun danyi wasu darusa da suka gabata akan yadda ake neman kudi a internet - sai dai bayanin bawani mai yawa bane idan kanaso zaka iya shiga nan kaduba su.
Menene AdSense?
AdSense wata hanya ce da ake tallata hajojin wasu kamfanoni da masana'antu da makarantu da ma'aikatu a shafukan internet ga al'umma. Akan tallata hajojin ne ga masu amfani da internet idan suka ga abun da suke so sai su shiga ayi magana da su. Shi kuma wanda ya tallata wannan hajar a shafinsa, wadancan kamfanoni da ma'aikatun da suka bashi zai samu kudi musamman idan wasu suka sayi wani abu ta sanadiyar shafin sa.
A takaice dai AdSense yana nufin wata hanya da ake samun kudi da ita ga masu aiki da internet da mai shafi da su kamfanonin da masu siyan hajar. Abubuwan da ake saidawa a internet suna da sukin farashi, kuma suna da ingancin gaske. Domin kayan wasu kamfanoni ne ake tallatawa jama'an duniya a internet.
AdSense hanyace da blogger wato mutanen da suke rubuce rubuce a shafukan internet suke samun makudan kudi da ita. Kuma mafi yawa an dogara da ita domin neman kudi a internet.
Google AdSense yana nufin AdSense na kamfanin Google, wanda kusan kaso casa'in da biyar na masu amfani da internet musamman bloggers suka dogara akanta wajen neman kudi a internet. Google AdSense ana samun kudi da shi kuma suna biya ne da dalar Amurka. Amma kafin mutum yafara aiki dasu suna da wasu ka'idoji idan mutum ya kiyaye su zai samu amfanuwa. Idan kuma mutum ya karyasu ba zai amfana da su ba.
Kusani dan kun shiga wani shafi kun karanta labarai ko kun saukar da wakoki da bidiyoyi mai wannan shafin bazai samu komai ba. Mai shafi yana samun kudi ne idan mai kai ziyara ya danna kan wannan tallace tallacen da yake gani a shafin. Wannan tallace tallacen da ake gani a shafin shine AdSense, kuma shine hanyar dayake samun kudi.
A takaice wannan shine bayanin menene Adsense da kuma amfaninsa ga bloggers. Fatan anfahinci menene shi da kuma amfanin sa a internet. Mun gode da kawo ziyara wannan shafin!

Leave a Comment