Menene Force?

Shin sau nawa ka ke yin aiki a kullum, kaman dagawa, ko turawa, ko kuma jawowa?

Ba kaman yanda akasarin mutane su ka sani ba, a physics idan aka ce aiki (work done) a na nufin a sa karfi a tura wani abu, ko kuma a sa karfi a jawo wani abu.

Domin a lokacin da ake jawo wannan abun ko turashi za a samu lokaci da nisa da kuma karfin aikin. A kimiyyar physics duk aikin da za a yi ko aka yi dolene a samu cewa wannan aikin sai an dauki lokaci kafin a gama shi (time). Sannan kuma dole abun ya canza daga wajen da ya ke zuwa wani wajen, kenan akwai nisa ko tazara (distance), sai kuma karfin da aka sa lokacin da aka yi aikin (force).

Idan mu ka duba a cikin aiyukan mu na yau da kullum kaman tafiya, ko dauka, ko ajiye abu a kan bukaci sa karfi (wato force ba energy ba). Haka kuma tura abu ko jawoshi shima ana bukatar saka karfi. Wannan karfin da mu ke sawa domin daga abu ko tura abu shi ake kira force.

Menene force?

Force ya na nufin tursasa wani, ko wani abu, ko kuma saka karfi domin tura wani abu, ko kuma jawoshi, hakama daga abu, ko tsayar da abun da ya ke tafiya, ko canza gudun abun da ya ke tafiya, da kuma saka abun dake tsaye ya motsa, ko fara tafiya. To wannan karfin shi ya ke kawo acceleration (canzawar motsin abu).

Wannan nau'in karfin a physics ya dogara ne akan nauyin abu (mass) da kuma canzawar tafiya ko saurin abun (acceleration) da wannan karfin ya sa wannan abun.

Misali, mota ta na tsaye sai a ka ce ku tura ta, to sai ku ka tura motar daga inda ta ke tsaye zuwa nisan mita goma (10m). Ka ga a nan kun yi aiki tunda kun tura motar daga inda take tsaye zuwa wani wajen nisan mita goma. Karfin da ku ka sa shine force, nisan mita goma shine distance. To idan mu ka gano adadin karfin da ku ka sa za mu iya gano adadin aikin da ku ka yi.

Akwai wani wasa mai suna 'tug of war' wanda za ka ga mutane sun rike igiya daya wasu a gabar wasu a yamma, kuma kowanne ya na ja ta bangarensa - wadanda su ka fi karfi su ne za su rinjayi dayan bangaren. To karfin da su ka sa domin jawo wannan igiyar zuwa bangaren su shine force ne.

Kwatankwacin haka ya ke faruwa tsakanin maganadisu (magnet) da karfe. Maganadisu ko kurar karfe (magnet) su ma haka su ke sa karfi su jawo karfe zuwa jikinsu. Wannan karfin da su ke sawa su jawo karfe shi ake kira magnetic force. Kuma maganadisu guda biyu idan ka hadasu za ka ga wani lokacin su na korar junansu (repulsion), idan kuma ka juyasu za ka ga su na kama junansu (attraction).

Maganadisu daga karshensu ta sama ko ta kasa a na kiran wajen pole. To kuma pole kala biyune ajikin maganadisu akwai pole din sama, da pole din kasa, wato north pole da south pole. Idan ka hada south pole da south pole za ka ga maganadisun su na korar junansu. Idan kuma ka hada south pole da north pole za ka ga su na kama junansu.

Ire-iren force

Ire iren force guda biyu ne sune;
1. Contact force
2. Non-contact force

1. Contact force:

Contact force dayane daga cikin ire iren force guda biyu, kuma shi ana ganin mai yin aikin ya na taba jikin abun da yake dagawa ko turawa ko jawowa. Misali, idan za ka tura mota ko mashin ko wheelbarrow dolene sai hannunka ya taba jikin motar ko mashin din kafin ka tura abun kenan hannunka ya na contacting din abun da ka ke aiki akansa.

2. Non-contact force

Non-contact force ko kuma field force shima dayane daga cikin ire-iren force, amma sai dai shi ba a ganin abubuwa biyun su na taba junansu a lokacin da daya ya ke tura ko jawo dayan. Misali, idan ka samo kurar karfe da kusa (nail) idan ka ajiye kusar a kusa da kurar karfen za ka ga wannan kurar karfen ta na jawo kusar zuwa jikinta.

Amma idan mu ka lura ba za muga wani abu kaman hannu ajikin kurar karfen ba a lokacin da ta ke jawo kusar, kawai sai dai mu ga kusar ta zo jikin kurar karfen. Hakama gravity da electric force da nuclear force su ke rike abu ko jawoshi. Ire-iren non-contact force su ne:

Ire-iren field force

1. Magnetic force
2. Electric force
3. Gravitational force
4. Nuclear force

1. Magnetic force

Magnetic force ya na nufin karfin maganadisu ko kurar karfe wanda su ke sawa, su jawo wani karfe zuwa jikinsu, ba tare da an ga wani abu a jikin kurar karfen ya na jawo wancan karfen ba. Misali, idan ka ajiye kusa a wajen kurar karfe za ka ga a take wannan kurar karfen ta jawo wannan kusar zuwa jikinta.

2. Electric force

Electric force kuma karfine da ake samun shi a cikin kayan wutar lantarki a lokacin da su ke aiki.

3. Gravitational force

Gravitational force wani karfine da ido ba ya iya ganinsa, sai dai jiki ya ji shi, wannan karfin shine ya ke jawo abubuwa daga sama zuwa kasa a duniya. Sannan kowace duniya karfin gravity dinta dabanne, misali, duniyar nan da mu ke ciki earth, karfin gravityn ta shine 9.8N/kg.

4. Nuclear force

Nuclear force kuma wani karfine da ke aiki a inda idon mu ba ya iya hangowa. Nuclear force shine ya ke rike da neutron da proton a cikin nucleus din atom.

Za mu dakata a nan da fatan a na amfanuwa da darusan da mu ke rubutawa a shafin nan.

No comments

Powered by Blogger.