Menene GPS Satellite?
Bari mu fara da fassara ma'anar kalmar GPS din da farko, a turance GPS ya na nufin Global Positioning System. GPS wata fasahace wanda ake amfani da ita wajen gano inda wani mutum, ko wani abu ya ke a doron kasa. GPS ya na da amfani ga matafiya musamman a zamanin nan. Saboda zai nuna maka sunan kasa ko garin da ka ke a lokacin da ka ke tafiya da kafa, ko da abun hawa.
Kananun na'urorin GPS ana sakasu a motoci da jiragen sama da na ruwa domin ganin hanyar da ake tafiya a cikinta. Haka kuma ana amfani da ita wajen leken asirin wata kasa. Na'urar GPS ta na da bangarori guda uku, kuma ga bayanin bangarorin kaman haka:
Bangare na farko shine satellite, wato tauraron dan Adam wanda ya ke can cikin sararin samaniya ya na aiki, ba dare ba rana.
Bangare na biyu kuma shine ground satellite, wato satellite wanda ya ke doron kasa ya ke musayar sako da tauraron dan Adam.
Sai kuma GPS receiver wato karamar na'urar GPS da mutane su ke rikewa a hannu ko sakawa a abun hawansu kaman mota ko babur domin gano hanya.
GPS satellite na farko an harba shi cikin sarari a shekarar 1978. Saboda ya taimakawa sojoji samun bayanan sirri akan wadanda su ke nema, da kuma inda za su kai hari. Kuma kowanne daga satellite din da aka harba cikin sarari ana tsammanin zai yi aiki na tsawon shekaru goma ko makamancin haka. A takaice GPS satellite ya na da nauyin kilogram dari tara da bakwai (907kg), kuma ya na da solar panel masu tsayin mita biyar (5metres) ko sama da haka. Wadannan solar panel din su su ke samarwa GPS satellite wutar lantarki ta hanyar hasken rana. Bayan nan kuma cikin GPS satellite akwai batura (batteries) na musamman.
Akwai satellite guda ashirin da hudu na GPS, wadanda aikin su shine gano inda wani mutum ko wani abu ya ke a doron kasa. GPS satellite su na sama a nisan kilomita dubu ashirin (20,000km) tsakanin su da doron kasa. Wato daga radius na duniya zuwa abun da ya yi sama har inda su ke kilomita dubu ashirin ne. Sannan su na zagaye duniya a cikin sa'o'i sha biyu (12hrs). Wato a duk rana su na iya zagaye duniya sau biyu kenan.
Bayan kusan shekaru biyu da harba GPS satellite cikin sarari, a shekarar 1980 gwamnati ta bawa mutane farar hula wadanda ba jami'an tsaro ba dama su yi amfani da na'urar GPS ta hannu idan su ka mallaketa - akwai kananun na'urorin GPS na hannu za ka gan su kaman wayar salula. GPS ya na lissafa lokaci da kwanan wata da nisan abun da su ka hango a doron kasa. Sannan GPS ya na iya sanar da kai cewa lokaci kaza ka yi tafiya, sai ka tsaya a lokaci kaza. A wannan tafiyar da ka yi, kayi tafiyar nisan kilomita kaza, kuma ka yi minti kaza da second kaza kafin ka je inda za ka je, amma fa idan ka na tare da GPS receiver a wajenka.
GPS satellite su na amfani da network domin musayar bayanai tsakanin su da kananun na'urorin GPS da su ke hannun mutane. Domin nunawa mutum inda ya ke da kuma sanar da shi nisan tafiyar da ya yi da kuma lokaci da sauran bayanai.
Akwai kananun na'urorin GPS na hannu, wadanda mutane su ke siya su yi amfani da su a ababen hawansu saboda su gano hanya. Wadannan kananun GPS din ana kiran su GPS receiver. Wayoyin hannu na zamani kaman su iPhone, da Android, da makamantan su su na zuwa da irin wannan fasaha da ke taimakawa a gano hanya. Amma a waya anfi saninsu da Maps, ko Google maps. Wadanda su ke nunawa mutum hanya a cikin wayarsa.
Bayanan GPS satellite su na iya ratsawa ta cikin hadiri, ko giza gizai, ko ruwa ko iska, su wuce a lokacin da su ke tafiya. Haka kuma su na iya ratsawa ta cikin glashi ko roba su wuce. Sannan kuma GPS satellite su na da saurin tafiyar kilomita dubu sha daya da dari biyu da sittin da biyar duk sa'a (11265kmph).
GPS satellite guda uku ne su ke iya gano wajen da wani mutum ko wani abu ya ke a doron kasa. Amma kuma sai sun zama su hudu sannan ne su ke iya samar da cikakkun bayanai akan duk abun da su ka hango a doron kasa. Daga baya sai su samar da sauran bayanai kaman gano nisan da abun ya yi, da kuma saurin abun a lokacin da ya ke tafiya, da kuma daidai inda abun ya ke, tare da lokaci da kwanan wata.
Kaman ko wane satellite su ma GPS satellite su na aika bayanai ta hanyar hasken da idon dan Adam baya iya gani, wato Radiowaves. Radiowaves daya ne daga ciki electromagnetic radiation - wadanda suke tafiya a cikin sarari, kuma suna iya ratsa abubuwa masu kauri su wuce. Electromagnetic radiation suna tafiya ne da saurin haske, wato su kan yi tafiya mai nisan mita miliyan dari uku a duk second daya (300, 000, 000m/s). Indai kana da na'urar GPS a hannun ka, wato GPS receiver duk inda ka shiga a doron kasa ana iya gano inda kake da lokacin da kaje wajen da kwanan wata.
Za mu tsaya anan sai kuma idan mun zo da wani bayanin akan wata fasahar kuma. Idan kuna so kusan menene satellite ku shiga nan. Mu na fatan ana anfuwa da bayanan da ake karantawa a shafin nan.
Mun gode da kawo ziyara shafin nan sai mun sake ganinku!
Kananun na'urorin GPS ana sakasu a motoci da jiragen sama da na ruwa domin ganin hanyar da ake tafiya a cikinta. Haka kuma ana amfani da ita wajen leken asirin wata kasa. Na'urar GPS ta na da bangarori guda uku, kuma ga bayanin bangarorin kaman haka:
Bangare na farko shine satellite, wato tauraron dan Adam wanda ya ke can cikin sararin samaniya ya na aiki, ba dare ba rana.
Bangare na biyu kuma shine ground satellite, wato satellite wanda ya ke doron kasa ya ke musayar sako da tauraron dan Adam.
Sai kuma GPS receiver wato karamar na'urar GPS da mutane su ke rikewa a hannu ko sakawa a abun hawansu kaman mota ko babur domin gano hanya.
Tarihin GPS a takaice
Fasahar GPS ta samo asali ne daga wani tsarin tsaro ko yaki da gwamnatin Amurka ta yi, wanda zai taimakawa dakarun sojinta su san inda su ke aiki, da kuma gano maboyar 'yan ta'adda da masu ta da kayar baya, da wasu mahimman abubuwa masu alaka da tsaro, sannan da tattara bayanan sirri akan abokan gaba.GPS satellite na farko an harba shi cikin sarari a shekarar 1978. Saboda ya taimakawa sojoji samun bayanan sirri akan wadanda su ke nema, da kuma inda za su kai hari. Kuma kowanne daga satellite din da aka harba cikin sarari ana tsammanin zai yi aiki na tsawon shekaru goma ko makamancin haka. A takaice GPS satellite ya na da nauyin kilogram dari tara da bakwai (907kg), kuma ya na da solar panel masu tsayin mita biyar (5metres) ko sama da haka. Wadannan solar panel din su su ke samarwa GPS satellite wutar lantarki ta hanyar hasken rana. Bayan nan kuma cikin GPS satellite akwai batura (batteries) na musamman.
Akwai satellite guda ashirin da hudu na GPS, wadanda aikin su shine gano inda wani mutum ko wani abu ya ke a doron kasa. GPS satellite su na sama a nisan kilomita dubu ashirin (20,000km) tsakanin su da doron kasa. Wato daga radius na duniya zuwa abun da ya yi sama har inda su ke kilomita dubu ashirin ne. Sannan su na zagaye duniya a cikin sa'o'i sha biyu (12hrs). Wato a duk rana su na iya zagaye duniya sau biyu kenan.
Bayan kusan shekaru biyu da harba GPS satellite cikin sarari, a shekarar 1980 gwamnati ta bawa mutane farar hula wadanda ba jami'an tsaro ba dama su yi amfani da na'urar GPS ta hannu idan su ka mallaketa - akwai kananun na'urorin GPS na hannu za ka gan su kaman wayar salula. GPS ya na lissafa lokaci da kwanan wata da nisan abun da su ka hango a doron kasa. Sannan GPS ya na iya sanar da kai cewa lokaci kaza ka yi tafiya, sai ka tsaya a lokaci kaza. A wannan tafiyar da ka yi, kayi tafiyar nisan kilomita kaza, kuma ka yi minti kaza da second kaza kafin ka je inda za ka je, amma fa idan ka na tare da GPS receiver a wajenka.
GPS satellite su na amfani da network domin musayar bayanai tsakanin su da kananun na'urorin GPS da su ke hannun mutane. Domin nunawa mutum inda ya ke da kuma sanar da shi nisan tafiyar da ya yi da kuma lokaci da sauran bayanai.
Akwai kananun na'urorin GPS na hannu, wadanda mutane su ke siya su yi amfani da su a ababen hawansu saboda su gano hanya. Wadannan kananun GPS din ana kiran su GPS receiver. Wayoyin hannu na zamani kaman su iPhone, da Android, da makamantan su su na zuwa da irin wannan fasaha da ke taimakawa a gano hanya. Amma a waya anfi saninsu da Maps, ko Google maps. Wadanda su ke nunawa mutum hanya a cikin wayarsa.
Bayanan GPS satellite su na iya ratsawa ta cikin hadiri, ko giza gizai, ko ruwa ko iska, su wuce a lokacin da su ke tafiya. Haka kuma su na iya ratsawa ta cikin glashi ko roba su wuce. Sannan kuma GPS satellite su na da saurin tafiyar kilomita dubu sha daya da dari biyu da sittin da biyar duk sa'a (11265kmph).
GPS satellite guda uku ne su ke iya gano wajen da wani mutum ko wani abu ya ke a doron kasa. Amma kuma sai sun zama su hudu sannan ne su ke iya samar da cikakkun bayanai akan duk abun da su ka hango a doron kasa. Daga baya sai su samar da sauran bayanai kaman gano nisan da abun ya yi, da kuma saurin abun a lokacin da ya ke tafiya, da kuma daidai inda abun ya ke, tare da lokaci da kwanan wata.
Kaman ko wane satellite su ma GPS satellite su na aika bayanai ta hanyar hasken da idon dan Adam baya iya gani, wato Radiowaves. Radiowaves daya ne daga ciki electromagnetic radiation - wadanda suke tafiya a cikin sarari, kuma suna iya ratsa abubuwa masu kauri su wuce. Electromagnetic radiation suna tafiya ne da saurin haske, wato su kan yi tafiya mai nisan mita miliyan dari uku a duk second daya (300, 000, 000m/s). Indai kana da na'urar GPS a hannun ka, wato GPS receiver duk inda ka shiga a doron kasa ana iya gano inda kake da lokacin da kaje wajen da kwanan wata.
Za mu tsaya anan sai kuma idan mun zo da wani bayanin akan wata fasahar kuma. Idan kuna so kusan menene satellite ku shiga nan. Mu na fatan ana anfuwa da bayanan da ake karantawa a shafin nan.
Mun gode da kawo ziyara shafin nan sai mun sake ganinku!
Leave a Comment