Yanda ake kirkiro WordPress
WordPress dayane daga software da ake amfani da su a internet domin bude blog. Kuma shine blog da aka fi amfani da shi wajen gina blog a yau. WordPress shine blog na daya daga cikin blog din da aka raja'a a kansu.
Shin ko ka san menene blog da kuma amfaninsa?
Shi WordPress akan samu damar budeshi, ko mallakarsa ta hanyar mallakar hosting. Hosting din da aka mallaka ta hanyar siya ko na kyauta za a samu daman install din WordPress a kansa. Sannan mafi yawa a yanzu kamfanonin da su ke samar da hosting, su na bayar da domain a kyauta. Amma sai ka siya hosting sannan za su ba ka domain a kyauta. Idan ba ka siya hosting ba, ba za su ba ka domain ba.
Shin ko ka san menene WordPress da kuma amfaninsa wajen gina blog a internet?
Idan ka na son mallakar WordPress, to sai ka fara da mallakar hosting wanda akansa ne duk abubuwan WordPress da shi kansa su ke zama. Domain kuma shine sunan WordPress din naka. Idan ka na bukatar mallakar hosting na kyauta, sai ka je byethost.com, ka yi rajista da adreshin e-mail naka. Idan kuma na kudi za ka bude sai ka je godaddy.com ko bluehost.com ko hostinger.com ko kanoweb.net ka yi rajista da adreshin e-mail din ka, sai ka tura mu su kudin da za ka siya hosting bayan ka gama rajista da su.
Shin ko ka san menene hosting da kuma amfaninsa wajen gina WordPress?
Bayan ka yi rajista, ka biyasu kudin hosting din za su ba ka control panel, wanda a cikinsa za ka yi install din WordPress, da sauran aikace-aikacenka.
Shin ko ka san menene domain da kuma amfaninsa wajen gina WordPress?
2. Bayan ka gama siyan hosting a daya daga cikin shafukan da muka rubuta sunansu a sama, sai ka shiga Control panel. Ka na shiga za ka ga inda aka rubuta + Add site, sai ka shiga wajen.
3. Ka na shiga sai ka duba, za ka ga Create a WordPress login daga can kasa. Daga nan sai ka shiga wajen WordPress username, ka rubuta username din da ka ke so ka yi amfani da shi idan za ka yi Log in cikin dashboard din WordPress din ka. Bayan ka gama da username, sai ka shiga WordPress password, ka rubuta password din da ka ke so. Bayan ka gama rubuta username da password din sai ka shiga inda aka rubuta Add wanda za ka ganshi daga can bangaren dama.
4. Ka na shiga wajen za ka ga Installing WordPress... this process can take few minutes, sai ka jira hosting din su gama yima installing din WordPress din.
5. Lokacin da kake cikin jira su na gama install na WordPress din za ka ga sun rubuta ma WordPress successfully installed! Daga nan sai ka shiga WP Admin, domin ganin dashboard.
6. Ka na shiga WP Admin din za ka ga sun kawoka dashboard na WordPress din.
7. Daga nan sai ka shiga alamar hoton gida wanda ya ke can sama za ka ga an dawo da kai asalin cikin WordPress din naka.
Ko ka karanta bayanin menene website?
8. Duk kuma lokacin da kake so ka shiga dashboard na WordPress din naka sai ka rubuta adreshin WordPress din sannan ka kara /wp-admin a karshen adreshin sai ka yi Ok, za ka ga an kawoka wajen da za ka yi log in cikin dashboard na WordPress din naka.
9. Su na kawoka wajen sai ka rubuta username da password din da ka yi rajistar shafin da su, sannan ka shiga Log in.
10. Ka na yin haka za ka ga an kawoka cikin dashboard din WordPress din naka, daga nan sai ka cigaba da aiyukanka. Domin koyan yanda ake kirkiran sabon page, ko kuma koyan yanda ake seta theme, ko kuma koyan yanda ake install din plugin a WordPress sai a duba darusan da suka wuce a baya wadanda suke karkashin Blogging.
Ina ga zamu tsaya a nan da fatan ana amfanuwa da darusan da mu rubutawa a shafin nan. Sannan kuma kofa a bude take ga mai tambaya. Idan akwai abun da ba a gane ba, sai a yi kasa wajen comment a rubuta.
Mu na godiya a bisa ziyarartar shafin nan da kukeyi. Sai mun sake ganinku, a huta lafiya, mun gode.

Ga yanda ake yi
1. Da farko, ka je Godaddy.com, ko Kanoweb.net, ko Bluehost.com, ko Hostinger.com ka siya hosting za su ba ka domain a kyauta.Shin ko ka san menene domain da kuma amfaninsa wajen gina WordPress?

Leave a Comment