Menene E-mail?
Wannan tambaya na jima ina jinta a wajen mutane dadama musamman a dandalin sada zumunta na internet. Mafi yawa su kan yi tambaya akan menene e-mail, da kuma amfanin sa. Saboda su kan ga a mafi yawan kafofin sada zumunta akan bukacesa kafin a bude account da su.
Shin ka karanta bayanin yanda ake bude e-mail na kamfanin Google kuwa?
A takaice e-mail dai wata hanya ce da ake amfani da ita wajen tura sakonni, da kuma karbansu ta internet - kaman yanda ake tura sakonnin kar-ta-kwana wato SMS a wayoyin da ba sa iya shiga internet. Sai dai shi e-mail ya fi SMS daukan bayanai mai yawa. Mu na iya cewa kusan duk amfanin da layin waya wato SIM CARD ya ke yi a waya haka shima e-mail ya ke yi a shafukan yanar-gizo. Sannan kuma shi e-mail din kansa sai da lambar waya ake iya bude account din sa.
Shin ko ka san yanda ake tura sakon e-mail?
Ta hanyar e-mail a na iya aika sakonni masu yawa na rubuce-rubuce, ko hotuna, ko bidiyoyi, ko kuma kade-kade da wakoki a cikin lokaci kadan. Da e-mail a na samun daman bude asusun ajiya na banki, da kuma yin rajista a manyan makarantu, da kamfanoni, da sauran ma'aikatu. Hatta account din Facebook da Twitter idan za ka bude a da can farko da e-mail kadai ake iya budesu. Amma kasancewa an samu cigaban fasaha yanzu da lambar waya ma a na bude account din su.
Haka za ka ga mafi yawa sunan kamfanin e-mail din ake sawa a wajen da mu ka rubuta email.com a misalin da mu ka yi a sama. Adreshin e-mail mafi shahara a duniya su ne Google mail, da Yahoo mail, kuma ga yanda adreshin e-mail din su ya ke myemail@gmail.com da myemail@yahoo.com. Idan an lura za a ga gmail.com da yahoo.com a bayan @ to a wajen sunan kamfanin e-mail din ya ke.
Shin ko ka karanta bayanin yanda ake bude e-mail na kamfanin Yahoo kuwa?
Akwai kamfanoni masu yawa da su ke samar da adreshin email - kuma kusan gaba dayansu a kyauta, wato ba sai ka biyasu ko sisi ba. Bayan kamfanonin e-mail mafi shahara wato Google mail, da Yahoo mail akwai wasu na daban kaman @rocketmail da @hotmail da sauransu kuma su din ma kyauta su ke samar da e-mail.
Bawai lambobin waya kadai ba, sakonnin WhatsApp na ka za ka iya daurasu a kan e-mail din ka kafin WhatsApp din ya yi expire. Bayan ka yi updating din sa sai ka yi backup din su - daga nan WhatsApp din zai ci gaba daga inda ya tsaya.
Bayan Google akwai wasu shafukan yanar-gizon da za ka yi rajista da su, sai ka daura abubuwanka ka ajiyesu a can. Sannan kuma duk lokacin da ka ke da bukatarsu za ka iya dawo da su ka yi amfaninka da su.
Wannan abune mai sauki muddin ka na da e-mail musamman na Google - sai ka bude Google drive, ka yi scanning din documents, sannan ka turamasa. Bayan sakon documents din ya je wajen sa, zai budesu ya gani, sannan sai ya yi printing din su, ya cirosu.
Misali, idan ka yi subscribe din wata channel a YouTube - su channel din duk lokacin da su ka daura sabon bidiyo za su turoma sakon cewa sun daura bidiyo mai suna kaza-kaza a taskarsu, kuma za ka ga wajen da za ka shiga ya kaika kan wannan sabon bidiyon, domin ka bude shi ka gani.
Miliyoyin mutane na amfani da adreshin e-mail a yau domin tafiyar da harkokinsu da ma'amalolinsu a internet. Ta hanyar sakonnin e-mail ofisoshi da ma'aikatun su ke aikewa ko karban bayanai a tsakaninsu, musamman bayanan sirri da ba a so wasu su sani. E-mail hanyar karban sakonni ce dake da dadin mu'amala - sai dai tafi dadin aiki ga masu amfani da computer ko manyan wayoyi na zamani.
Mallakar adreshin e-mail zai ba ka daman shiga duk inda ake rajista da shi kaima ka yi taka rajistar a kyauta. Ya na da kyau ya zamanto email din ka ya na da isasshen tsaro. Saboda rashin email din ka zai jawo ma asara inde ka na amfani da shi a gurare masu mahimmanci kaman mu'amalar kudi ta banki.
A na so e-mail din ka ya kasance ya na da tsaro. Saboda haka bawai ko ina za ka shiga ka yi rajista da shi ba. Idan ka san za ka shiga ko ina ka yi rajista to ya na da kyau ka nemi wani e-mail din na daban.
Duba da cewa yanzu mugunta da cuta sun yi yawa - dole ne sai mutum ya yi taka tsantsan da bayanan shi na sirri. Adreshin email naka ya na da amfani a wajenka, domin kai kadai ka san iya amfanin da ka ke yi da shi.
Idan Allah ya so za mu zo da bayanan yanda ake bude e-mail da kuma yanda ake aiki da shi a wayar hannu. Ina ga za mu tsaya haka - mu na fatan wannan bayanin zai amfane mu gaba daya.
Ku ci gaba da kawo ziyara shafin nan tare da gaiyato 'yan uwa da abokan arziki domin su zo su amfana da abubuwan da mu ke rubutawa a shafin nan. Mu na fatan za a huta lafiya, mun gode, sai mun sake ganinku.
Shin ka karanta bayanin yanda ake bude e-mail na kamfanin Google kuwa?
Menene e-mail?
E-mail ya na nufin 'Electronic Mail' wato wata kafa ko wata hanyar tura sakonni ta fasahar electronics a internet. Wannan fasaha akan yi amfani da waya ko na'ura mai kwakwalwa domin karba da tura sakonni da ita a yanar-gizo kuma a kyauta.A takaice e-mail dai wata hanya ce da ake amfani da ita wajen tura sakonni, da kuma karbansu ta internet - kaman yanda ake tura sakonnin kar-ta-kwana wato SMS a wayoyin da ba sa iya shiga internet. Sai dai shi e-mail ya fi SMS daukan bayanai mai yawa. Mu na iya cewa kusan duk amfanin da layin waya wato SIM CARD ya ke yi a waya haka shima e-mail ya ke yi a shafukan yanar-gizo. Sannan kuma shi e-mail din kansa sai da lambar waya ake iya bude account din sa.
Shin ko ka san yanda ake tura sakon e-mail?
Ta hanyar e-mail a na iya aika sakonni masu yawa na rubuce-rubuce, ko hotuna, ko bidiyoyi, ko kuma kade-kade da wakoki a cikin lokaci kadan. Da e-mail a na samun daman bude asusun ajiya na banki, da kuma yin rajista a manyan makarantu, da kamfanoni, da sauran ma'aikatu. Hatta account din Facebook da Twitter idan za ka bude a da can farko da e-mail kadai ake iya budesu. Amma kasancewa an samu cigaban fasaha yanzu da lambar waya ma a na bude account din su.
Ya ya adreshin e-mail ya ke?
Shi e-mail adreshine wanda kowane daban ya ke - kaman yanda kowace lambar waya ta bambamta da wata. Yanda adreshin e-mail ya ke shine za ka ga ya na dauke da alamar @ a cikin sa, da kuma sunan kamfanin da su ka samar da wannan email din a bayan alamar @ din. Misali, idan ka ga e-mail kaman haka myemail@email.com a nan misalin da mu ka yi bayan alamar @ din mun rubuta email.com.Haka za ka ga mafi yawa sunan kamfanin e-mail din ake sawa a wajen da mu ka rubuta email.com a misalin da mu ka yi a sama. Adreshin e-mail mafi shahara a duniya su ne Google mail, da Yahoo mail, kuma ga yanda adreshin e-mail din su ya ke myemail@gmail.com da myemail@yahoo.com. Idan an lura za a ga gmail.com da yahoo.com a bayan @ to a wajen sunan kamfanin e-mail din ya ke.
Shin ko ka karanta bayanin yanda ake bude e-mail na kamfanin Yahoo kuwa?
Akwai kamfanoni masu yawa da su ke samar da adreshin email - kuma kusan gaba dayansu a kyauta, wato ba sai ka biyasu ko sisi ba. Bayan kamfanonin e-mail mafi shahara wato Google mail, da Yahoo mail akwai wasu na daban kaman @rocketmail da @hotmail da sauransu kuma su din ma kyauta su ke samar da e-mail.
Amfanonin e-mail
E-mail ya na da amfani mai dimbin yawa ga wanda ya mallake shi, kuma ya san yanda ake aiki da shi. Saboda haka ga wasu kadan daga cikin amfanonin e-mail.1. Import da backup
Idan ka seta e-mail din ka a wayarka za ka iya daura lambobin wayarka gaba daya a kan e-mail din ka - ta yanda duk lokacin da ka bukacesu za ka iya backup din su, su dawo ko da layinka ya bata kuma a kyauta.Bawai lambobin waya kadai ba, sakonnin WhatsApp na ka za ka iya daurasu a kan e-mail din ka kafin WhatsApp din ya yi expire. Bayan ka yi updating din sa sai ka yi backup din su - daga nan WhatsApp din zai ci gaba daga inda ya tsaya.
2. Cloud storage
Akwai wasu shafuka ko application wadanda su ke samar da space ko mu ce media storage a online. Wadannan space din a na amfani da su wajen daura media files (kaman hotuna, ko wakoki, ko bidiyo) domin a ajiye su saboda gaba. Musamman Google su na da Google drive bangaren da su ka ware 15GB kyauta ga duk wanda ya mallaki e-mail din su domin ya ajiye abubuwansa a ciki.Bayan Google akwai wasu shafukan yanar-gizon da za ka yi rajista da su, sai ka daura abubuwanka ka ajiyesu a can. Sannan kuma duk lokacin da ka ke da bukatarsu za ka iya dawo da su ka yi amfaninka da su.
3. Scan da transfer
E-mail musamman na kamfanin Google za su ba ka daman ka yi scanning din documents din ka - sannan ka turasu. Misali, idan ka na wani gari ko wata kasa, sai wani ya ce ya na so ka turomasa takaddunka (documents), alhali kai da shi ba a gari daya ku ke rayuwa ba, shin ya za ka yi?Wannan abune mai sauki muddin ka na da e-mail musamman na Google - sai ka bude Google drive, ka yi scanning din documents, sannan ka turamasa. Bayan sakon documents din ya je wajen sa, zai budesu ya gani, sannan sai ya yi printing din su, ya cirosu.
4. Subscription
Da adreshin e-mail ake subscribe a wasu shafuka, kaman channel din YouTube. Subscribe hanyace da wasu shafuka su ke turowa mutum sako kai-a-kai a duk lokacin da su ka rubuta sabon darasi a shafinsu, ko kuma su ka daura wani sabon abu (kaman waka ko bidiyo) a shafinsu. Wannan ya na da amfani wajen samun labarai da sauran bayanai a sauwake.Misali, idan ka yi subscribe din wata channel a YouTube - su channel din duk lokacin da su ka daura sabon bidiyo za su turoma sakon cewa sun daura bidiyo mai suna kaza-kaza a taskarsu, kuma za ka ga wajen da za ka shiga ya kaika kan wannan sabon bidiyon, domin ka bude shi ka gani.
5. Registration
Idan ka na da adreshin e-mail da shi za ka yi rajista a gurare dadama. Misali, idan za ka bude shafi kaman wannan - ko kuma za ka bude account a dandalin sada zumunta kaman Facebook, ko Instagram, ko Twitter da sauransu. A yanzu hatta katin dan kasa da katin zabe a kan bukaci adreshin e-mail saboda mahimmacinsa.Miliyoyin mutane na amfani da adreshin e-mail a yau domin tafiyar da harkokinsu da ma'amalolinsu a internet. Ta hanyar sakonnin e-mail ofisoshi da ma'aikatun su ke aikewa ko karban bayanai a tsakaninsu, musamman bayanan sirri da ba a so wasu su sani. E-mail hanyar karban sakonni ce dake da dadin mu'amala - sai dai tafi dadin aiki ga masu amfani da computer ko manyan wayoyi na zamani.
Mallakar adreshin e-mail zai ba ka daman shiga duk inda ake rajista da shi kaima ka yi taka rajistar a kyauta. Ya na da kyau ya zamanto email din ka ya na da isasshen tsaro. Saboda rashin email din ka zai jawo ma asara inde ka na amfani da shi a gurare masu mahimmanci kaman mu'amalar kudi ta banki.
A na so e-mail din ka ya kasance ya na da tsaro. Saboda haka bawai ko ina za ka shiga ka yi rajista da shi ba. Idan ka san za ka shiga ko ina ka yi rajista to ya na da kyau ka nemi wani e-mail din na daban.
Duba da cewa yanzu mugunta da cuta sun yi yawa - dole ne sai mutum ya yi taka tsantsan da bayanan shi na sirri. Adreshin email naka ya na da amfani a wajenka, domin kai kadai ka san iya amfanin da ka ke yi da shi.
Idan Allah ya so za mu zo da bayanan yanda ake bude e-mail da kuma yanda ake aiki da shi a wayar hannu. Ina ga za mu tsaya haka - mu na fatan wannan bayanin zai amfane mu gaba daya.
Ku ci gaba da kawo ziyara shafin nan tare da gaiyato 'yan uwa da abokan arziki domin su zo su amfana da abubuwan da mu ke rubutawa a shafin nan. Mu na fatan za a huta lafiya, mun gode, sai mun sake ganinku.
Leave a Comment