Yanda za a ci gaba da amfani da WhatsApp bayan ya yi expire
Watakila abokinka ko kai da kanka ka taba fuskantar wannan matsalar. Ka na cikin aiki da WhatsApp a wayarka sai a wayi gari ya nuna ma ka cewa ya yi expire, kuma ya dai na aiki, sannan a lokacin kuma wayarka babu datar da za ka shiga App store ko Play store, ka yi update din WhatsApp na ka. To a cikin tutorial din nan za mu nuna yanda za ka ci gaba da amfani da wannan WhatsApp din da ya nuna ma cewa ya yi expire. Amma kafin mu yi nisa ya na da kyau ka san menene ya ke sa WhatsApp ya ke expire.
A WhatsApp ma haka abun ya ke. Misali, idan kamfanin WhatsApp su ka hada WhatsApp a 01-January-2020, sai su seta wani tsari wanda ya ke aiki da kwanan watan wayar da WhatsApp din ya ke kanta. Wannan tsarin za su seta shi duk lokacin da 03-March-2020 ta yi to WhatsApp din zai tsaya sannan ya nuna ma cewa ya yi expire. To su kuma kamfanin kafin wannan lokacin ya yi za su yi kokari su kawo wasu sababbin canje canje da tsare tsare wanda zai kara burge ma su amfani da WhatsApp.
Bayan wannan su kamfanonin su kan yi amfani da tsarin feedback wanda mai amfani da WhatsApp zai tura mu su ra'ayinsa, da tunanin yanda ya kamata su tsara WhatsApp din domin ya zamo ya na tafiya da zamani.
2. Idan WhatsApp din ka ya yi expire a watan hudu, sai ka canza setin kwanan wata daga watan hudu zuwa watan uku, ko watan biyu. Kaman yanda mu ka yi misali a sama mun ce WhatsApp din ka ya yi expire a 03-March-2020, sai ka dawo da kwanan watan zuwa 03-January-2020, ko 03-February-2020.
3. Ka na yin haka shikenan, sai ka dawo ka bude WhatsApp din na ka. Ka na bude shi za ka ga ya ci gaba da aiki kaman bai yi expire ba.
Amma fa duk lokacin da kwanan watan wayarka ya dawo ya na tafiya daidai to WhatsApp din ba zai yi aiki ba, wato zai nuna cewa ya yi expire. Domin ya wuce lokacin da aka tsara zai dauka ya na aiki.
Ina ga za mu dakata a nan, mu na fatan a na fa'idantuwa da tutorial din da mu ke rubutawa a shafin nan. Kuma mu na fatan za mu sake ganinku a shafin nan kowane lokaci.
Daga karshe kuma duk wanda ya ke da tambaya, sai ya je wajen comment ya rubuta, zai samu amsa idan Allah ya sa mun sani. Mu na godiya tare da fatan za a huta lafiya.
Menene ya ke sa WhatsApp ya yi expire?
Kafin mu shiga tutorial din kai tsaye za mu fara da bayani akan menene ya ke sa WhatsApp ya yi expire. Kamfanonin da su ke kirkiran application su kan sabunta application din su duk bayan wani lokaci, kaman duk bayan watanni uku ko biyar, saboda sun canza wani tsari a cikin application din, ko kuma sun kawo wani tsari wanda da farko babu shi a cikinsa.A WhatsApp ma haka abun ya ke. Misali, idan kamfanin WhatsApp su ka hada WhatsApp a 01-January-2020, sai su seta wani tsari wanda ya ke aiki da kwanan watan wayar da WhatsApp din ya ke kanta. Wannan tsarin za su seta shi duk lokacin da 03-March-2020 ta yi to WhatsApp din zai tsaya sannan ya nuna ma cewa ya yi expire. To su kuma kamfanin kafin wannan lokacin ya yi za su yi kokari su kawo wasu sababbin canje canje da tsare tsare wanda zai kara burge ma su amfani da WhatsApp.
Bayan wannan su kamfanonin su kan yi amfani da tsarin feedback wanda mai amfani da WhatsApp zai tura mu su ra'ayinsa, da tunanin yanda ya kamata su tsara WhatsApp din domin ya zamo ya na tafiya da zamani.
Ga yanda abun ya ke
1. Da farko, ka je settings din wayarka, sai ka canza setin kwanan wata. Misali, idan WhatsApp na ka ya nuna ma cewa ya yi expire a ranar 03-March-2020, sai ka dawo da kwanan watan baya.2. Idan WhatsApp din ka ya yi expire a watan hudu, sai ka canza setin kwanan wata daga watan hudu zuwa watan uku, ko watan biyu. Kaman yanda mu ka yi misali a sama mun ce WhatsApp din ka ya yi expire a 03-March-2020, sai ka dawo da kwanan watan zuwa 03-January-2020, ko 03-February-2020.
3. Ka na yin haka shikenan, sai ka dawo ka bude WhatsApp din na ka. Ka na bude shi za ka ga ya ci gaba da aiki kaman bai yi expire ba.
Amma fa duk lokacin da kwanan watan wayarka ya dawo ya na tafiya daidai to WhatsApp din ba zai yi aiki ba, wato zai nuna cewa ya yi expire. Domin ya wuce lokacin da aka tsara zai dauka ya na aiki.
Ina ga za mu dakata a nan, mu na fatan a na fa'idantuwa da tutorial din da mu ke rubutawa a shafin nan. Kuma mu na fatan za mu sake ganinku a shafin nan kowane lokaci.
Daga karshe kuma duk wanda ya ke da tambaya, sai ya je wajen comment ya rubuta, zai samu amsa idan Allah ya sa mun sani. Mu na godiya tare da fatan za a huta lafiya.
Leave a Comment