Yanda ake aiki da ka'idar BODMAS a wajen lissafi 01

Kaman yanda bayanai su ka gabata a darusan koyan lissafi - mun nuna ka'idojin da ake bi wajen warware matsalolin lissafi wanda ya kunshi hadawa da cirewa. Yanzu kuma za mu ci gaba da bayani akan wata ka'ida ta lissafi da ake kira BODMAS. Wannan ka'ida sha-kundum ce domin kusan kowane bangare na lissafi ana aiki da ita.

Menene BODMAS?

BODMAS ya kalmar BODMAS ta kunshi takaitattun harufa guda shida, wadannan harufan kowane daga cikinsu ya na da tasa ma'anar kuma su ake lissafi ma gaba daya. Harafin ‘B’ ya na nufin bracket, sai kuma harafin ‘O’ kuma ya na nufin of, sai ‘D’ kuma ya na nufin division, sai ‘M’ kuma multiplication, sannan sai ‘A’ wato addition daga karshe sai ’S’ wato subtraction.

Brackets ( )

Harafin B din farko ya na nufin bracket, shi kuma bracket a cikin lissafi ya na nufin multiplicati wato ribanyawa. Idan ka ga bracket a cikin lissafi ya na nufin wajen ribanyawa. Amma akwai in da ake amfani da shi domin raba tsakanin alamomin lissafi, misali, a ka'idar lissafi ba a rubuta 3 + -2 = 1, saboda alamonin + da - sun hadu a wajen daya domin haka sai dai a rubuta 3 + (-2)=1. Ina ga mun yi bayanin haka a baya. Abun lura a nan shine bracket din ya nuna cewa wannan negative sign a jikin 2 din ya ke.

Amma idan ka ga wata lamba a cikin bracket da kuma wata a waje to wannan bracket din zai zama multiplication ne. Misali, idan ka ga an rubuta 2(6) hakan ya na daidai da 2 × 6. Kenan shida sau biyu shine sha-biyu wato 2 (6) =12. A ka'idar lissafi idan za ka fara warware shi ka'idar BODMAS za ka dauka, sai ka fara lissafin daga inda ka ga bracket ko da kuwa bracket din shine a karshe ko a tsakiya.

Sai of wato su 2² ko 2³ ko 2⁴ ko X^n

Daga harafin B, sai O wato of shi ma dai duk kusan daya ya ke da bracket, amma wani lokacin ba ribanyawa ake yi ba. Idan idan za ka fara lissafi bayan ka gama da bracket sai ka zo ka duba cikin tambayar idan akwai square (X²), ko wata power (X^n), ko square root (√) da sauransu. Square shine lamba daya a ribanyawa ta da lamba kamanta. Misali, daidai yake da 3 × 3. Idan ka lissafa a na'urar lissafi (calculator) za ta ba ka 9, haka idan ka lissafa uku sau uku za ka samu tara kaman haka 3 × 3 = 9.

Shima power kaman square yake, sai dai shi square lambobi guda biyu iri daya ake ribanyawa kawai. Shi kuma power duk wata lamba da ta dauki wata lamba wannan da aka dauka ita ake kira power. Kuma ana ribanyawa lambar da ta dagata power sau adadin power. Misali, 10⁴, a nan goma sau goma sau goma sau goma ake ribanyawa, 10 × 10 × 10 × 10. Haka ya na nufin dubu goma wato 10 × 10 × 10 × 10 = 10,000. Watakila wani zai yi tunanin cewa 10⁴ arba'in (40) ne. Amma ba arba'in bane dubu goma ne, saboda a sama mun ce goma sau goma har sau hudu.

Bari mu ga yanda lissafin yake, idan mu kace goma sau goma ya zama dari (10 × 10 = 100) kenan, sai mu ce dari sau goma ya zama dubu (100 × 10 = 1000) kenan, hakama idan mu kace dubu sau goma ya zama dubu goma (1000 × 10 = 10,000) kenan. X^n ya na nufin X ta daga n ne, kuma alamar ^ ta na nufin raised power wato daga lamba zuwa sama, misali goma ta daga hudu (10⁴), a nan X din ita ce goman n kuma shine power wato 4.

Rabawa ÷ ko /

Idan aka ba ka lissafi ka warware sai ka duba akwai bracket a cikinsa, idan akwai sai ka warwareshi ta hanyar lissafi. Sannan ka duba akwai square ko power ko square root sai ka warwaresu. Idan kuma babu su sai ka duba akwai division wato rabawa. Ana amfani da alamomin ÷ da / a matsayin rabawa a cikin lissafi. Idan ka ga kaga 10/2 ya na nufin goma a rabata gida biyu, wato haka ya na daidai da 10 ÷ 2 amsarsu dayace 10 / 2 = 5 ko 10 ÷ 2 = 5.

Ribanyawa × Bayan harufan ‘B’ da ‘O’ da ‘D’ a jikin harufan BODMAS sai harafin ‘M’ wato multiplication ma'ana ribanyawa. Wasu bayanan ribanyawa mun yi bayaninsu a sama, saboda haka za mu yi bayanin alamar ribanyawa wato ×. Idan ka ga alamar ribanyawa a tsakanin lambobi biyu hakan ya na nufin wadannan lambobin ribanyasu ake yi. Misali, 2 × 3= 6 wato biyu sau uku ya kama shida, hakama 7 × 3 = 21 bakwai sau uku ya zama ashirin da daya.

Dole idan za ka yi lissafi ka tabbata ka bi wadannan ka'idojin daki-daki, idan kuma ka tsallake ka'ida daya a cikin aikinka to daga karshe lissafin ba za ka samu amsa daidai ba.

Hadawa +

Bayan matakin ribanyawa sai mataki na biyun karshe wato wanda daga shi sai na karshe - su kuma wadannan matakan mun yi bayaninsu a darusa biyu da su ka wuce a baya. Amma gaba bayanin a takaice a na amfani da alamar + matsayin hadawa. Domin haka idan ka samu alamar hadawa a tsakanin lambobi biyu ko uku to hadasu ake. Misali, 2 + 6 = 6 wato biyu a hada da shida ya zama takwas, ko 6 + 4 + 10 = 20, wato shida a hada hudu a hada da goma ya zama ashirin.

Cirewa -

Sai a BODMAS idan cirewa da hadawa su ka hadu to cirewan ake farawa, sannan a zo a hadasu. Domin a nuna cirewa a na amfani da alamar -. Sannan kuma idan ka ga lambobi biyu kuma tsakaninsu akwai alamar cirewa, to lambar bangaren hagu ake cirewa daga ta bangaren dama. Misali, 6 - 2 = 4 wato shida a cire biyu kenan hudu zai rage, ko 20 - 6 = 14 , ashirin a cire shida goma sha hudu zai rage.

Za mu dakata a nan da fatan a na fahimtar darusan lissafi da mu ke rubutawa a shafin nan. Darasi na biyu zai zo da sauran misalai. Mu na godiya a huta lafiya.

3 comments:

  1. Gsky naji dadin wannan darasin Allah YA saka mk Da alhairi

    ReplyDelete
  2. Abokina Allah Yabarni da Xahrata.
    Kaikuma yasaka Maka da alkhairi aiki yayi kyau

    ReplyDelete

Powered by Blogger.