Yanda Drone ya ke aiki
Kaman yanda kowa ya sani drone jirgine mara matuki wanda ake amfani da shi a bangaren tsaro kaman leken asiri, ko tattara bayanan sirri, ko kuma kai hare hare a maboyar 'yan ta'adda da sauran masu tada kayar baya. Drone kala biyune akwai babba wanda sojoji suke amfani da shi, kuma akwai karami wanda ake amfani da shi wajen daukar hoto da bidiyo musamman masu shirya finafinai. A darasin nan za mu yi bayanine akan dan karamin drone wanda ake kira quadcopter.
Quadcopter ko kuma a ce drone duk abu dayane, kuma wani dan karamin jirgine wanda ake amfani da shi wajen daukan hotuna da bidiyo musamman ta sama. Drone ana sarrafashi ko tukashi da remote na hannu, ta yanda idan ka na tukashi za ka ga kaman ka na yin game.
Ko ka san menene battery, da kuma amfaninsa?
Drone ya na samun isashshiyar wutar lantarki daga batirin (battery) jikinsa - wanda ake yi masa caji. Sannan kuma batirinsa kaman batir din waya ya ke, sai dai ya fi batirin waya girma. Amma dai duk fasahar batirin iri daya ce - wato shima batirinsa Lithium ion battery ne, ba Lead acid battery ba. Lead acid battery shine batirin da aka hadashi da sinadarin Lead, wannan batirin shine batir din mota da mashin.
Jikin quadcopter akwai kafafuwa guda hudu, kuma kowace kafa jikinta akwai moto. Sannan kuma jikin moto din akwa farfela (rudder). Wadannan moto guda hudu su suke juya farfelolin jikinsu da matukar sauri - juyawan da wadannan farfelolin su ke yi da sauri shine ya ke kawo quadcopter din ya tashi sama, kuma ya yi tafiya a cikin iska. Misali, kowace farfela a minti daya tana juyawa (revolution) akalla sau dubu ashirin da takwas (28000RPM) - saboda quadcoptern ya samu isashshen karfin da zai tashi sama.
Moto guda hudu da su ke jikin kafafuwansa biyu su na juyawa daga hagu zuwa dama (clockwise), wato daya daga sama a bangaren hagu, dayan kuma daga kasa a bangaren dama. Sannan biyu 'yan uwansu su kuma su na juyawa daga dama zuwa hagu (anticlockwise), su ma daya daga sama a bangaren dama, daya daga kasa a bangaren hagu. Kaman yanda ake gani a hoton dake kasa 1 da 4 su na juyawa bangare daya, 2 da 3 ma haka. Wannan juyawar da su ke yi clockwise da anticlockwise ita ta ke sa quadcopter idan ya tashi sama zai iya tafiya ta kowane bangare. Haka kuma zai iya juyawa ya yi kwana a duk lokacin da aka ba shi umarni ta hanyar remote din da ake sarrafa shi.
Quadcopter ya na amfani da radio frequency domin sadarwa tsakaninsa da GPS satellite wadanda su ke can cikin sararin samaniya su na aiki ta yanda za a iya ganosa ko da ya bace indai ya na aiki (amma wannan tsarin a manyan drone ya ke). Amma idan batirinsa ya yi sanyi ko kuma cajinsa ya kare ganosa zai yi wahala, sai dai a gano inda ya ke daga karshe kafin batirinsa ya mutu.
Shin ko ka san menene pixel, da kuma amfaninsa?
Idan moto din jikinsa su na juyawa da sauri za ka ga ya yi can sama, wato idan yanada caji ya na tashi sama sosai, akasin haka kuma idan batirinsa ya fara sanyi zai yi kasa kasa. Idan quadcopter ya na tafiya ta gabar kai kuma ka na so ya yi kwana ya dawo ta yamma ko kudu ko arewa kawai a remove za ka juya wadannan scroller ko analogue kaman hannun game din Play Station (PS). Ka na juya wadannan scrollern za ka ga jirgin ya juya ya na tafiya a hanyar da ka ke so ya bi.
Yanda fasaharsa ta ke aiki shine moto din da su ke bangaren da ka ke so quadcoptern ya juyo su za a karawa gudu (ta hanyar kara musu karfin wuta). Misali, idan a lokacin da quadcoptern ya ke tafiya ta arewa kowace moto ta na samun wuta mai karfin voltage uku (3volts), sannan kowace ta na juyawa sau dubu sha biyar duk minti daya (15, 000RPM). Idan aka karawa biyu karfin wutar daga volt uku zuwa volt biyar (5volts) gudun juyawarsu zai canza, kuma ya karu daga dubu sha biyar duk minti daya zuwa dubu ashirin da biyar duk minti daya (25, 000RPM).
Quadcopter ya na aiki a matsayin mai karban sako (receiver), yayin da remote dinsa ya ke aiki a matsayin mai turo masa sako (transmitter). Akwai wata na'ura a jikinsa wanda ake kira frequency to voltage converter. Amfaninta shine canza frequency zuwa voltage. Remote ya kan tura sakon umarni ta hanyar radio frequency sai wannan na'urar ta canzashi zuwa voltage.
Shin ka na bukatar karin haske gameda Lithium ion battery, tare da amfaninsa?
Farfelolin quadcopter su na juyawa ta yanda su ke danne iska ta yi kasa, yayin da ita kuma iskar ta ke tura jirgin sama. Rudder ko farfela an yi su ne a lankwashe ta yanda za a samu wani angle wanda ake kira angle of attack. To idan farfela tana lankwashe ta yanda za ta bada angle of attack, idan ta na juyawa sama ta ke yi iskar kuma ta yi kasa. Shiyasa, jirage su ke tashi sama. Quadcopter jirgine dan karami wanda ake amfani da shi domin daukan hotunan gurare kaman gona, da jeji, da gidaje, da sauransu, amma ta sama. Kuma ya na samun wutar lantarki daga lithium ion batteryn da ya ke jikinsa. Sannan ana tafiyar da shi ta hanyar remote dinsa wanda yake kamada hannun game din play station.
Domin ci gaba da samun cikakkun bayanai, ko karin haske akan fasahar zamani a ci gaba da kasance da shafin nan. Za mu dakata anan da fatan ana amfanuwa da darusan kimiyya da fasaha wadanda mu ke rubutawa a shafin nan - mun gode.
Sannan duk mai tambaya, sai ya yi kasa wajen comment ya rubuta ta. Mu kuma za mu amsa masa idan Allah ya sa mun sani. Daga karshe kuma mu na fatar sake ganinku tare da abokanku a shafin nan. Mun gode, a huta lafiya😀

Leave a Comment