Yanda scanning din document a wayar Android
Document su ne manyan takaddu masu mahimmaci wadanda ake rubuta bayanai na wasu aiyuka. Haka kuma su ne littattafan karatu kaman a kwalejoji da jami'o'i. Gwamnati ta kan yi amfani da su domin aika sakon wasu bayanai zuwa wasu ma'aikatu.
Scanning din document zai ba ka dama ka yi print na shi a printer. Ta wannan hanyar ake aika manyan takaddu a internet.
Kayan aikin sune
1. Doc scanner
2. Adobe acrobat reader
Ga yanda ake scanning din
1. Da farko, ka je Play store, ka yi install din Doc scanner. Bayan nan kafin mu shiga tutorial din ga rubutun da za mu yi scanning dinsa a jikin wannan takaddar.
2. Bayan ka gama install din application din - sai ka bude shi. Idan ka bude application din za ka ga cikinsa babu komai, sai ka duba daga kasa ta bangaren dama za ka ga hoton camera, sai ka shiga wajen.
3. Ka na shiga wajen camerar wayar za ta bude. Camerar ta na budewa sai ka dauki hoton wannan takaddar. Bayan ka dauki hoton, sai ka shiga OK, wanda ya ke can kasa ta bangaren hagu.
Ka na taba OK, za ka ga application din ya fara Processing Document... Sai ka jira kadan.
4. Ya na gama processing document din zai nuno maka wajen da resize din hoton. Wato wajen da za ka rage ko seta tsayi ko fadin document din. Ka na gama gyara girman document din sai ka taba alamar maki (✔) wanda ya me can sama daga bangaren dama.
Ka na taba wannan maki din za ka ga application din ya sake rubuta maka Processing Document... Anan din ma sai ka sake jiransa ya gama processing din.
5. Application din ya na gama processing din zai kawoka wajen da za ka tsara document din. Idan ka na so ka yi amfani da document din da kalarsa ta asali, sai ka taba Original. Idan kuma ka na so ka canza zuwa baki da fari kadai, sai ka taba B&W. Idan kuma ka na so ka kara hasken document din sai ka taba Lighten. Idan kuma kala za ka canza sai ka taba Color. Idan kuma duhu za ka kara sai ka shiga Dark.
Duk wanda ka shiga a cikinsa B&W, da Lighten, da Color, da kuma Dark za ka ga wani dogon layi a kwance jikinsa za ka ga zuge daga hagu zuwa dama idan za ka kara haske, ko kala. Sannan jikin wannan layin za ka zuge daga dama zuwa hagu idan za ka rage haske. Bayan ka gama seta document din sai ka duba daga can sama a bangaren dama za ka ga alaman maki ✔, sai ka tashi.
Ka na taba wajen za ka ga application din ya fara Processing Document... Sai ka jira ya gama.
6. Application din ya na gama processing din zai nuno maka document din. Idan ka na so ka turashi sai ka taba alama share wanda ya ke can sama a kusa da tambarin PDF.
7. Idan kuma ka na so ka mai document din ya zama PDF sai ka taba tambarin PDF wanda ya ke can sama.
Ka na taba tambarin PDF din za ka ga application din ya yi processing kadan. Ya na gama processing din Adobe acrobat reader zai bude maka PDF din.
8. Sai ka ci gaba da karanta document din bayan ka gama karantawa sai ka dawo baya. Domin ganin sauran bayanai kaman wajen canza suna, ko goge document din sai ka taba wadannan digo guda uku da suke jikin document din.
Ka na taba wajen za ka ga wasu rubutu sun baiyana kaman haka: Save as PDF, da Save to gallery, da Share, da Rename, da kuma Delete a karshe. Idan za ka goge document din sai ka shiga Delete.
9. Ka na shiga Delete - application din zai tambayeka confirmation, sai ka taba Delete.
Ka na taba Delete din za ka ga document din ya goge.
Wadannan matakan ake bi idan za a yi scanning din document a wayar Android cikin sauki. Kuma matakan ba su da wahala kaman yanda mu ka nuna a sama. Da fatan ana amfanuwa da darusan da mu ke rubutawa a shafin nan.
Sannan duk wanda ya ke da tambaya kofa a bude ta ke, sai ya yi kasa wajen comment ya rubuta mana ita. Mu kuma za mu ba shi amsa, idan Allah ya sa mun sani.
Ku na iya tura wannan post din ga dandalin sada zumunta domin abokanku su karanta. Mun gode, sai mun sake ganinku, a huta lafiya.

Leave a Comment