Yanda Ake Aika Sakon Email

Email hanyace ta tura sakonni a internet. Da email ana iya aika sakon takaddu da sauran document kaman PDF, ko DOCX, da hotuna, da bidiyo, da makamantansu. Sannan wanda aka aika masa wannan sakon zai samesu a nan take, kuma ya yi aiki da su ko karantasu. Sakon email ba kaman sakon sms yake ba, domin shi kana iya rubuta cikakkiyar wasika ka aikata - wanda a sms baka da daman yin haka.

Aika sakonnin email hanyace da za ka yi amfani da ita wajen tura sakonnin cikin sirri. Domin sakonka zai je cikin adreshin email na wanda ka aika masa sakon kai tsaye, shi kuma zai gani, ya karanta, sai yayi maka reply.

A shafin nan mun nuna yanda ake rajistar sabon adreshin email na Yahoo, da na Google cikin sauki, tare da hotunan yanda akeyi. Saboda haka a cikin tutorial din nan kuma za mu nuna yanda ake rubutawa tare da aika sakon email a waya.

Aika sakon email babu wahala, domin kusan duk wanda yake amfani da internet zai iya idan ya nutsu. Nasan masu karanta rubutun nan dadama sun san yanda ake aika sakon email - hakama ba a rasa wadanda suke da muradin koya. Wanda bai san yanda ake aika sakon email ba wannan tutorial din zai amfanesa sosai. Domin zai koyi abun da ya jima yana son koya. Kafin ka aika sakon kana bukatar application guda daya a wayarka, kuma ga application guda uku mun bada link din da zaka iya saukar dasu. Amma guda daya kawai zaka saukar - bawai gaba dayansu ba.

Ganan Kayan Aikin
1. Opera Mini
2. FireFox
3. Chrome


Wadannan browser guda ukun wato Opera Mini, da FireFox, da Chrome amfaninsu daya. Wato da guda daya za ayi aiki a cikinsu - duk wanda kake dashi za ka iya amfani dashi. Idan kuma wayarka babu ko daya, sai ka saukar da wanda kakeso kayi aiki da ita.

Ga Yanda Akeyi
1. Da farko, ka tabbata email bashi da matsala, kuma yana aiki lafiya kalau. Sannan sai ka bude browserka - daya daga cikin wadanda muka bayar da link nasu a sama. Za mu yi misali da Gmail, kana bude browserka sai ka rubuta www.gmail.com sai ka taba Go, ka jira ta kaika cikin shafin Gmail. Kana zuwa cikin shafin Gmail din sai ka shiga Log in ko Sign in. Kana shiga sai ka rubuta adreshin Gmail naka da password, sai ka yi Log in.

2. Kana yin Log in za ka ga an kaika cikin Gmail naka. Kana shigowa cikin Gmail naka, ka duba daga can sama ta bangaren dama sai ka taba hoton abun rubutu.


3. Kana taba wannan hoton abun rubutun za ka ga an kaika wajen da zaka rubuta sakonka ka turashi. Daga sama za ka ga To: kasa dashi kuma Cc/Bcc: shima kasa dashi sai Subject: daga can kasa kuma zakaga wajen rubutu.


4. Kana shigowa wajen da zaka rubuta sako ka aikashi ga yanda za ka yi. Ka fara shiga To: sai ka rubuta adreshin email din wanda zaka aika masa sakon. Sai ka shiga Subject: ka rubutu dalilin yin sakon, sai ka shiga kasa dashi ka rubuta sakonka. Misali, zaka rubuta sakon gaisuwane, ka shiga wajen To: ka rubuta fasaha@yahoo.com sai kayi kasa ka shiga Subject: ka rubuta Gaisuwa sai ka shiga wajen rubutun dake kasa da wajen Subject ka rubuta sakon naka kaman haka Aslm, fatan kana lafiya. Kana gama rubuta sakon sai ka duba daga can sama za ka ga Send yana ta bangaren hannunka na dama, sai ka tabashi.


5. Kana taba Send din nan, za ka ga sakon naka yatafi nan take.


Kana yin haka, nan take wanda ka aika masa sakon zai samu sabon sako a cikin inbox na email nasa. Wannan hanya za kabi idan zaka aika sakon email. Aika sakon email babu wata wahala ko kadan.

Fatan ana amfanuwa da darusan da muke wallafawa a shafin nan. Ko da a Yahoo mail ne idan zaka aika sako wadannan matakan za kabi. Haka kuma kuna da dama kuyi tambaya akan abun da baku gane ba a wajen comment dake kasa.

Da fatan zamu sake ganinku a shafin nan. Sannan kuna iya gaiyato mana abokanku zuwa shafin nan domin suma su zo, su amfana da abubuwan da muke wallafawa a shafin nan. Mun gode, sai mun sake ganinku, a huta lafiya!

No comments

Powered by Blogger.