Yanda ake subscribe din channel a YouTube

Subscribe abu ne da za ka yi, da zai ba ka daman samun bayanai akan sabbin labarai ko sabbin abubuwa da zarar an daurasu a wani shafin internet. Shafukan internet dadama suna amfani da hanyar yin subscribe domin sanar da mabiya shafukansu a duk lokacin da sukayi sabon rubutu, ko kuma saka sabon abu. Wanda yayi subscribe zai samu sako nan take da wadancan shafukan sun rubuta wani darasi.

Mun yi bayanin menene subscribe da amfaninsa a baya, idan baka karanta wancan darasin ba, shiga nan sai ka karanta menene shi da kuma amfaninsa sannan kadawo kakoyi yanda akeyinsa. Yin subscribe bai da wahala musamman a YouTube wanda akanshi zamuyi tutorial yanzun nan.

Yanzu dai sai kawai ka tanadi kayan aiki wadandan bawasu boyaiyu bane, ga sunan nan a kasa sai ka saukar dasu. Idan kuma kana dasu shikenan sai kaje kayi subscribe.

Kayan aikin su ne:
1. Google mail
2. FireFox
3. Chrome
4. YouTube

Wadannan application guda ukun gaba dayansu amfaninsu dayane. Idan kana da daya shikenan sai kayi amfani dashi. Gmail kuma email ne wanda sai dashi zaka samu daman yin login cikin YouTube, sannan kayi subscribe dashi.

Ga yanda ake yi
1. Da farko, ka je ka shiga shafin YouTube, ko kuma ka shiga application na YouTube, wanda zai kaika shafin YouTube. Ka na shiga sai ka yi login da account naka na gmail. Ka na yin login sai kaje ka shiga channel din da kakeso kayi subscribe. Bari muyi misali da channel mai suna Arewa Teach, wanda ake koyar da yanda ake hada logo, da banner da sauran tutorial akan wayoyi. Kana shiga channel din wajen kasa da sunan channel din zakaga inda aka rubuta SUBSCRIBE, sai ka taba kan rubutun.



Ka na taba kan SUBSCRIBE, din ka duba daga bangaren dama agaba da inda aka rubuta Subscribers, za ka ga wata kararrawa (bell) ta futo. Sai ka taba kan wannan kararrawar. Ko dayake su da kansu zasu rubuta maka Tap the bell to get notified new videos. Bayan kataba kararrawan nan daga kasa kadan zakaga anrubuta maka Subscription added.


Shikenan idan ka yi haka ka gama subscribe na channel a YouTube. Nan gaba su na daura wani sabon bidiyo a channel din zakaga sakon cewa channel mai suna kaza kaza sun daura bidiyo mai suna kaza.


Wannan matakin mai saukin shi ake bi idan za a yi subscribe na channel a YouTube. Subscribe na channel a YouTube daman mun riga da munyi bayanin yanda akeyinsa. Idan bakasan menene subscribe da amfaninsa shiga nan.

Yin subscribe ya na da amfani kuma yana da saukin yi, babu wahala, kuma kyauta akeyinsa. Kawai kaide ka kasance kana da adreshin email na kamfanin Google wato Google mail. Idan kuma baka dashi shiga nan sai ka koyi yanda ake bude shi.

Nan shine karshen wannan tutorial din, kuma anan zamu tsaya sai kuma wani lokacin. Fatan anfanuwa da shafin nan, muna godiya da kawo mana ziyara da kukeyi a ko da yaushe a huta lafiya.

No comments

Powered by Blogger.