Yanda Ake Bude Google Mail (2020)

Google mail ko kuma Gmail a takaice. Adreshin Email ne wanda kamfanin Google suke samarwa ga masu amfani da internet a kyauta. Mutane dayawa sukanyi tambaya akan cewa wai email daban gmail ma daban? Gmail shine email wanda kamfanin Google suke samardashi, email kuma ya kunshi duk wani kamfanin email kaman Yahoo mail, da Hotmail, da shi Gmail din kanshi.

Gmail email ne wanda ake amfani da shi a bangarori dadama a internet. Wasu bangarorin ba a iya aiki dasu a waya ko a internet har sai anyi amfani da Gmail. Misali, daura bidiyo a YouTube, ko kuma shiga PlayStore duk ba a iya yin su har sai an yi amfani da Gmail.

Ba tare da wani bata lokaci ba, sai kuyi kasa bayanan yanda ake bude Gmail sunanan a rubuce, sannan kuma a tanadi kayan aiki.

Kayan Aikin Sune:
1. Chrome


Ga Yanda Akeyi
1. Da farko, ka tabbata kanada Chrome a wayarka idan kuma bakada ita sai ka saukarda ita ta link din da muka bayar a sama. Bayan ka saukar da ita sai kayi install nata. Kana gama install nata sai ka budeta - ka shiga wajen rubuta url address, ka rubuta www.gmail.com sannan ka taba Ok, ko kuma Go. Kana taba Ok, ko Go din sai ka jira browser ta bude maka shafin Google mail. Idan ta bude maka shafin sai ka shiga inda aka rubuta Sign in wanda yake sama ta bangaren dama.


2. Kana shiga za a kawoka shafin da ake Sign in. Daga kasa zaka samu wajen da aka rubuta Email or phone, kasa dashi kuma akwai Create account. Sai ka taba inda aka rubuta Create account.


3. Kana taba wajen wasu zabuka guda biyu zasu baiyana a wajen. Zabukan sune For myself, da kuma To manage my business, sai ka shiga na farkon wato For myself.


4. Kana zaban For myself za a kawoka shafinda zaka yi rajistar sabon account na Gmail naka. Daga can sama zaka samu an rubuta Create your Google Account daga kasan kuma zaka ga wajen First name, sai wajen Last name, sai kuma Username, zaka ga an rubuta @gmail.com ta bangaren dama, daga nan kuma sai Password, daga karshe kuma sai Confirm. Sai ka cike guraren da bayananka.


5. Za mu yi misali, da yanda na yi lokacin da nake bude Gmail dina. Ka shiga First name ka rubuta sunanka, misali na rubuta sunana Nura. Sai kuma wajen Last name ka rubuta sunan mahaifinka, misali Mahdi. Sai kuma wajen Username ka rubuta sunan da zai kasance shine adreshin email naka, misali Nuramahdi - amma ba sai ka rubuta @gmail.com ba, sunan kawai zaka rubuta. Sai ka shiga wajen Password ka rubuta password naka. Daga nan kuma sai kayi kasa ka shiga Confirm, ka sake rubuta password naka a wajen. Kana gama cike komai sai ka shiga Next.


6. Kana shiga Next zaka ga an kawoka shafin Welcome to Google daga kasa kuma za ka ga tutar kasarka a wajen da zaka rubuta lambar wayarka. Kasa da ita kuma sai wajen recovery email address, sannan wajen zaban kwanan wata da shekarar da aka haifeka wato Day, da Month da kuma Year, kasa dasu kuma sai wajen zaban jinsi. Sai ka cike wajen da bayananka wadanda ake bukata a shafin sannan ka shiga Next.


7. Zan cike shafin da bayanai na, wajen Phone number na rubuta lambar wayata, misali 08012345678. Sai wajen recovery email address na rubuta fasahablog@gmail.com, a wajen Day sai na zabi 03. Wajen Month na zabi watan hudu wato April, sannan na zabi 1990 wajen Year. Wato hakan yana nufin an haifeni ranar 03 ga watan April na shekara ta 1990. Daga karshe kuma sai na zabi Male a wajen Gender, Male shine na miji, Female kuma ta mace. Kana gama cike wajen sai kayi kasa ka shiga Next.


8. Kana shiga Next za a kawoka shafin da aka rubuta Verifying your phone number. Kana shigowa shafin zaka ga tutar kasarka a kusada lambar wayar da ka rubuta a baya. Sai ka shiga Send.


9. Kana shiga Send za ka ga sun tura maka sakon sms dauke da wasu code. Sai ka bude cikin inbox na lambar da ka rubuta a baya, sai ka kwafo wadannan code din, ka dawo ka rubutasu a inda aka rubuta Enter verification code. Idan kuma baka bukatar su turo maka code din ta sms, sai ka duba kusa da Send za ka ga Call instead kana shiga za ka ga Google sun kiraka, idan ka dauka zaka ji suna fada maka code din da zaka sa. Sai kasa code din ka shiga Send.


10. Daga nan zasu kawoka inda aka rubuta Get more from your number. Sai ka shiga Skip, ko kuma ka shiga Yes, I'm in.


11. Kana shiga daya daga cikinsu, zasu kawoka shafin Privacy and policy sai kayi kasa ka karanta bayanan da suka rubuta.


Sai ka sake yin kasa domin shafin akwai bayanai da dokokin da ka'idojin amfani da Gmail a rubuce.


Bayan ka gama karantawa daga can kasa zaka ga I agree, sai ka shiga wajen.


12. Kana shiga I agree za a kawoka shafin Upgrade to the Gmail, sai kayi can kasa ka shiga Use the web version. Idan kuma kanada application na Gmail sai ka shiga OPEN THE GMAIL APP. Idan kuma baka dashi sai ka shiga Use the web version kawai.


13. Kana shiga zasu kawoka cikin inbox na sabon Gmail din da ka gama budewa. Zaka samu cikin inbox din babu sako ko daya.


Recovery email shine email din da zaka rubuta lokacin da kake rajista, ko kuma bayan ka gama rajistar sabon email, wanda zaka yi amfani dashi wajen dawo da email naka koda lambar da ka bude email din da ita bata kusa, ko bata aiki, ko kuma ta bata. Tsarin saka recovery email ada sai ka gama rajistar email zaka sakashi, amma a yanzu lokacin da kake rajista zaka sakashi sai dai optional ne, wato idan kanada email sai ka rubutashi a wajen. Idan kuma bakada wani email wanda zaka yi amfani dashi, shikenan sai ka tsallake wajen ba tareda ka rubuta komai a wajen ba.

Wannan ita ce sabuwar hanyar da ake bude email da ita a wayar Android. Kuma hanyar batada wahala, kaman yanda muka nuna daki daki, daya bayan daya. Bude gmail yana da amfani sosai musamman saboda yanada tsaro fiyeda sauran kamfanonin email.

Da fatan ana amfanuwa da darusan da muke wallafawa a shafin nan. Idan akwai mai tambaya sai ya je wajen comment da yake can kasa ya rubuta tambayarsa a wajen. Mu kuma zamu amsa masa idan Allah yasa mun sani.

No comments

Powered by Blogger.