Yanda Ake Bude Sabon Email Na Yahoo

A baya munyi bayanin yanda ake bude Google mail, da kuma yanda ake verification nashi. Daga karshe har muka gwada tura sako, sai dai wancan darasin na masu aiki da kananan wayoyi da Symbian ne kadai. Masu aiki da Android da sauran manyan wayoyi suma mun yi musu bayanin yanda ake bude Google mail. Wannan yasa muka yanke shawarar nuna muku yanda ake bude Yahoo Mail cikin sauki.

Bude Yahoo Mail babu wata wahala ga masu aiki da Android da sauran manyan wayoyi. Saboda a cikin minti hudu zaka iya gama komai har kayi verification nashi. Sai dai kafin nan kuma yana da kyau kayi amfani da password mai karfi sosai, wato password mai wahalar ganewa. Daga karshe kuma ka saka recovery email da recovery phone number saboda tsaro.

Shima Yahoo Mail yana da nashi amfanin, kaman yanda mu kayi bayanin amfanin Gmail, sai dai shi Yahoo Mail bai kai Google mail tsaro ba. Shima Yahoo mail yana da nashi tsarin tsaron, muna iya cewa daga Google mail sai shi a fagen tsaro a cikin kamfanonin email da muka sani.

Sannan muna iya cewa Yahoo Mail kusan shine email na biyu da mutane su kafi aiki da shi bayan Google mail. Shima ana amfani dashi wajen saka website a Searching engine na Bing, yayin da shi kuma Google mail kawai a Google searching ake aiki dashi.

Application Din Da Ake Bukata
1. FireFox
2. Chrome
3. Yahoo mail

Wadannan application din guda uku bawai gaba daya zamuyi aiki da su ba. Application biyu na farkon wato FireFox da Chrome, ba zamuyi aiki dasu ba, zamuyi aiki da na ukun ne wato Yahoo mail wanda shine yafi sauki wajen bude email.

Ga Yanda Akeyi
1. Da farko, ka saukar da application na ukun daga link din da muka bayar a sama. Bayan ka gama saukar dashi sai kayi install nashi. Kana gama install nashi sai ka bude shi zakaga ya nuno maka YAHOO! MAIL daga tsakiyan allon wayar ka. Kana ganin wannan rubutun sai kayi kasa ka shiga inda aka rubuta Create a Yahoo account.


2. Daga nan zasu kai ka wajen da zakayi Sign up. Wato wajen da zaka bude sabon account naka. Kana shiga wajen sai kasa sunan ka a wajen rubutu na farko, misali Nura. Wajen rubutu na biyu kuma kasa sunan mahaifin ka, ko kuma wani suna daban, misali Mahdi. Sannan kasa sunan da kake so yazama shine adreshin email din naka, misali idan kasa nura.mahdi sunan email din naka zai zama nura.mahdi@yahoo.com - daga nan sai kuma wajen saka password, anan din ma ka rubuta password naka. Amma yana da kyau ka rubuta password mai wahalar ganewa.

3. Kana gamawa da password, sai kasa lambar wayar ka a wajen saka lambar waya, a kusa da ita zakaga Country code. +234 shine Country code na Nigeria - daga nan kuma sai ka zabi watan da aka haifeka, misali watan biyar shine May, gaba da shi kadan kasa nawa ga wata aka haifeka, misali 05, sannan ka zabi a wace shekara aka haifeka, misali 1995. Kana gama cike wannan wajen sai ka zabi jinsin ka wato namiji ko mace. Male shine namiji, Female mace. Kana gama komai sai kayi kasa ka taba Continue.


4. Daga nan zata kai ka wajen da zakayi verifying na account naka. Idan ka lura daga can sama zakaga lambar wayar da kasa, sai ka duba kasa da ita ka taba inda aka rubuta Text me an Account key. Wato kana so su turo maka wasu code domin su tabbatar da cewa kana kusa da layin wayar da kake bude email din dashi.


5. Kana yin haka zasu turo maka sako cikin layin ka. Sai kaje inbox na wayar, ka bude wannan sakon ka kwafo wadannan lambobin da suka turo maka. Sai ka dawo cikin application na Yahoo din kasa kasu, sai ka taba inda aka rubuta Verify.


6. Kana taba Verify nan take zasu nuna maka sakon Congratulation, wato suna tayaka murna da bude sabon account dasu. Daga nan zasu kai ka cikin email naka, aciki ma zakaga wasu sakonni.


Shikenan kagama komai, zakaga wasu sakonnin da suke tayaka murna a cikin inbox naka daga kamfanin Yahoo. Sai ka bude ka karanta su, daga nan sai ka cigaba da sauran harkokin ka na internet da sabon email naka.


Lokacin da ka zabi sunan adreshin email naka, idan su kace maka akwai mai wannan sunan to ka kara wasu lambobi a gaban sunan. Misali, ka zabi nura.mahdi idan akwai mai wannan sunan sai ka kara wasu lambobi kaman haka nura.mahdi223 ko kuma ka kara wani suna a gaban sunan naka.

Wajen lambobin sirrin wato password, yana da kyau kayi amfani alamomin rubutu wato Symbols wadanda ake kiran su Special characters. Saboda yanzu akwai azzaluman mutane da suke mugunta suna kwace wa mutane email nasu. Amma idan kasa lambobin sirri mai wahalar ganewa, to zaka samu tsaro cikin ikon Allah.

Bayan kagama bude sabon adreshin Yahoo mail naka, ka kaje ka sa Recovery email. Recovery email wani email ne da zaka sa ko da wannan email din naka yasamu matsala zaka iya seta komai, ta hanyar amfani da email din da kasa a Recovery email.

Sannan akwai Recovery number, anan ma duk lambar da kasa da ita zakayi amfani wajen dawo da account naka, ko da kamanta password naka.

Za mu tsaya anan sai kuma mun zo da wani sabon tutorial din. Da fatan ana amfanuwa da abubuwan da ake karantawa a shafin nan. Mun gode da kawo mana ziyara, da fatan zamu sake ganin ku!📄📝💬

1 comment:

  1. This is such a great resource that you are providing and you give it away for free. I love seeing blog that understand the value of providing a quality resource for free. intercom alternatives

    ReplyDelete

Powered by Blogger.