Mece ce Manhajar Android (OS)?

Assalamu alaikum, masu bibiyar wannan shafin. Ina muku barkanmu da wannan lokaci da kuma farin cikin kasancewa daku a wannan lokaci da zan gabatar da bayanin mece ce manhajar Android OS. Kafin muyi nisa a cikin bayanin yana dakyau ku karanta bayani game da sabuwar Android 12, wacce ita ce babbar manhajace ta Android mafi kyau da tsari a yau.


A yau mutane sun kasance suna amfani da kayan fasaha na lantarki a harkokinsu na yau da kullum. A cikin waÉ—annan kayan lantarkin akwai wayoyin hannu da sauran na'urorin tafi-da-gidanka. Haka zalika wadannan na'urorin sun zama abokan huldar mutane a aikace-aikacensu. Manhajar Android dayace daga cikin manhajojin na'urorin tafi-da-gidanka wacce take da matukar kokari. Wannan manhaja tana daya daga cikin manhajojin da akafi aiki da su a fannonin fasaha mabambanta.


Shin ko kun karanta bayanin yanda fasahar optical fingerprint scanner take aiki?


Manhajar Android, babbar manhaja ce mai matu?ar amfani wacce ake amfani da fasaharta a wayoyin hannu da talabijin da sakago da gilashin ido da agogon hannu mai na'ura a jikinsa da mota mai sarrafa kanta (mota mara matuki) da kuma na'urar daukan hoto da sauran na'urorin zamani masu sarrafa kansu. Wannan manhajar yawaitar wayoyi masu dauke da ita yasa wayoyin Java da Symbian sun bace, sun yi wahalar gani. Haka kuma a yau kana iya cewa manhajar Android tana kalubalantar manyan manhajoji kaman Windows da manhajojin iOS na kamfanin Apple. Kafin wayoyin Android, a shekarun baya mutane sun kasance suna amfani da wayoyi masu aiki da manhajar Java da kuma Symbian (wanda ita ma tana aikine bisa tsarin fasahar OS).


Mece ce fasahar OS?

Kalmar OS a takaice tana nufin operating system. Operating system yana nufin fasahar dake baka daman sarrafa wayarka bisa tsari ko zubin da aka ginata akai. Fasahar OS ita ce take shiga tsakaninka da wayarka, wato ita ce take gano inda ka taba, ko inda ka shiga, ko yin aikin da ka umarci wayarka tayi, sannan ta umarci application din da yake wannan aikin, ko application din da ka umarta yayi aiki. A yau fasahar OS ta cika wayoyin dake hannun jama'a ta ko ina.


Tarihin Manhajar Android

Manhajar Android ta samo asali ne a watan Oktoba na shekarar dubu biyu da uku a Palo Alto dake jahar California a kasar America. Wasu kwararrune a fannin na'ura mai kwakwalwa suka samar da ita. Mutanen sune Andy Rubin da Rich Miner da Nick Sear da kuma Chris White. Shekaru biyu bayan kammala tsari da zubin manhajar Android, a ranar shabakwai ga watan Agusta na shekarar dubu biyu da biyar kamfanin Google ya samu kulla alaka da wadanda su ka kirkiri manhajar Android. Amma ba a kaddamar da ita a cikin wayoyi ba har sai a shekarar dubu biyu da bakwai (2007).


Shin ko ka san yanda zaka kula da batirin wayarka?


An kaddamar da manhajar a tsarin wayar Android wanda ta kunshi bangarorin computer guda biyu, wato software da hardware. Bangaren software shine ya kan bayar da daman sarrafa application. Sannan kuma sai bangaren hardware wanda ya kunshi abubuwan da ake iya gani kuma ake tabawa, kamansu lasifika (speaker), da abun magana (microphone), taba screen (touchscreen), da na'urar daukan hoto (camera), da tocila (torch light). Wadannan bangarorin guda biyu an shiryasu ta yanda za su yi aiki tare da - wato da software za a sarrafa hardware.


Android ta na da nata injin wanda aka shiryata karkashin gudanarwarsa wato Kali Linux. Manhajojin Android ana saka musu sunan kayan zaki da makulashe kaman alawa da cakuleti. Wayoyin da su ka fara futowa da tsarin manhajar Android, su ne HTC, da Motorola, da kuma Samsung. Amma a wancan lokacin da madannai (keypad) su ka futo. Sai dai kamfanonin Google sun janye Android masu madannai duba futowar wayar kamfanin Apple wato iPhone wacce ta zo babu madanni sai dai a taba glashin waya wato touchscreen. Daga nan kamfanonin Google su ka kero wayoyin Android masu amfani da glashi a maimakon madannai.


Shin kana son koyan yanda za ka buÉ—e shafi kaman wannan da kanka?


Wayoyin Android da su ka fara futowa a wancan lokacin sun futo da manhajar Android mai version daga 1.0 zuwa 2.2 (cupcake, da donut, da eclair, da kuma froyo). Daga baya kamfanin Google ya sanar da cewa za a na sakawa manhajojin Android suna kaman sunan kayan kwalam da tande-tande (desserts). Ga version din manhajojin wayar Android tare da sunayensu, kaman haka:


Jerin version din Android

  • 1.5 Cupcake
  • 1.6 Donut
  • 2.1 Eclair
  • 2.2 Froyo
  • 2.3 Gingerbread
  • 3.2 Honeycomb
  • 4.0 Ice cream sandwich
  • 4.1 Jellybean
  • 4.2 Jellybean
  • 4.4 KitKat
  • 5.0 Lollipop
  • 6.0 Marshmallow
  • 7.0 Nougat
  • 8.0 Oreo
  • 9.0 Android Pie (Android Q)
  • 10 Android 10
  • 10 Android 12


Shin ko ka san mene ne bambancin Android OS da iPhone iOS?


Wayoyin Android idan aka kwatantasu da sauran kishiyoyinsu kaman iPhone da iPad, ana iya cewa sun fi saukin kudi. Hakama game da application na su ya fi na sauran wayoyin saurin samuwa. Har-ila-yau, akwai shafuka a internet wadanda za ka saukar da application ko game na Android cikinsu kuma a kyauta. Sannan kuma ka na iya saukar da application daga rumbun wasa na Google wato Google play store - wanda yake zuwa akan kowace wayar Android.


Ana iya cewa wayoyin kamfanin Apple su na da tsada fiye da wayoyin Android na kamfanin Google. Wannan ya sa ake cewa wayoyin iPhone da iPad sai 'yan boko, da samari, da 'yan mata. Ko da yake kowa ma zai iya amfani da wayoyin idan ya samu halin mallakarsu. Ina ga ya kamata mu dakata a nan.


Da fatan ana amfanuwa da darusan fasaha wadanda ake karantawa a shafin nan. Sannan kuma kuna iya rarraba wannan bayanai ga abokanku a shafukan sada zumunta da muhawara na intanet. Haka kuma duk wanda yake da tambaya, sai ya je can kasa wajen comment, ya rubutata, zai samu amsa insha Allahu. Mu na godiya, da fatan za mu sake ganinku, a huta lafiya ✋.

No comments

Powered by Blogger.