Saukar da Gboard a wayarka

Bayanai sun gabata a shafin nan akan menene keyboard, da kuma yanda ake seta shi a wayar Android. Kuma a wadancan darusan mun nuna yanda ake seta theme a keyboard din amma a wayar Android. Saboda haka yanzu kuma za mu cigaba da bayani akan daya daga cikin keyboard din da aka fi amfani da su a manyan wayoyin zamani wato Gboard.

Shin ko ka san menene Android 10, wato sabon version din Android?

Menene Gboard?

Gboard ya na nufin Google keyboard a takaice. Gboard application ne na keyboard wanda ake amfani da shi a wayoyin iPhone da Android. Kuma keyboard din ya kunshi kusan kowane shahararren yare na duniya da alamomin rubutunsa (symbols).

Google keyboard ya fara futowa a wayoyin iOS wato iPhone a cikin watan May na shekarar 2016, sannan wayoyin Android su ka fara futowa da shi a karshen shekarar wato a watan December, na 2016. Shigowar Gboard a wayoyin Android ya fara rikitar da masu amfani da ita saboda keyboard din da su ke aiki da shi kafinsa.

Shin ka karanta bayanin menene manhajar Android OS ta wayar Android?

Gboard ya zamo daya daga cikin application din Google da aka fi saukarwa a Play store. A cikin watan August na shekarar 2018 adadin masu saukar da Gboard a wayoyin Android kadai ya kai biliyan daya. Kuma hakan ya sanya shi ya zamo daya daga cikin sanannun kuma mafiya shahara daga cikin application din Android.

Saukar da Gboard

1. Gboard na masu Android
2. Gboard na masu iPhone da iPad

Amma kafin haka a cikin wata March na shekarar 2018 din aka sabunta Gboard ta hanyar kara adadin yarukan dake cikinsa. Yarukan da aka karamar daga yankin turai akwai Croatian, da Czech, da Dutch, da Finnish, da Greek, da Polish, da Romanian, da Baluchi, da Swedish, da Catalan, da Hungarian, da kuma Turkish. Sai Malay na kasar Malaysia daga gabashin duniya, sai Latin American Spanish daga yankin Latin America.

Shin ko ka karanta bayanin da mu kayi akanadadin bytes din da suke cikin memory 1GB?

A yanzu haka akwai yarukan Hausa da Swahili da larabci daga cikin yarukan nahiyar afurka. Saboda haka idan ka na bukatarsa - sai ka shiga Google play store - amma idan ka na aiki da wayar Android. Idan kuma da wayar iPhone ko na'urar iPad kake aiki sai ka shiga App store ka saukar da shi.

Shin ko ka san menene electromagnetic radiation?

Bayan kun saukar da Gboard a wayoyinku na Android ko iPhone ko na'urar iPad, sai kuyi install dinsa, sannan ku setashi, sai ku cigaba da aiki da shi a wayoyinku. Masu amfani da iPhone ko na'urar iPad ga bidiyo a sama na yanda ake seta Gboard - wadanda suke aiki da Android su duba shafin nan mun yi bayanin yanda ake seta keyboard.

Shin ka san menene visible light, da kuma amfanoninsa?

Ina ga zamu dakata a nan da fatan ana amfanuwa da tutorial dinmu.

No comments

Powered by Blogger.