Yanda ake seta keyboard a wayar Android
Wayar Android an yi ma ta wani tsari kaman tsarin na'urar girke wanda aka fi sani da desktop. Wannan na'ura idan ka lura za ka ga cewa allon madanninta (keyboard) daban yake, hakama allon manuninta (monitor) shima daban yake, speakerta ma daban take, sannan uwa-uba kwakwalwar na'urar wanda ake kira da central processing unit wato CPU a takaice, itama daban take. Sannan sai a hada su gaba daya su yi aiki a tare. Wato a jona keyboard, da speaker, da monitor, da sauran hardware na computer a jikin CPU din.
Sai dai wasu masu amfani da waya su kan yi korafin cewa keyboard na zuwan wayar ba ya gamsar dasu. Wannan kuwa ya na faruwane saboda rashin wasu abubuwa da ake bukata domin a tsara rubutu dasu a keyboard din.
Ka karanta bayanin yanda ake seta custom theme a keyboard din Android?
Tsara rubutu da emoticon ko emoji ya kan sa wannan rubutun ya kayatar da mai karatu. Idan ka na karanta rubuce-rubuce a shafukan sadarwa na internet za ka ga mutane su na amfani da keyboard iri daban-daban domin tsara rubutunsu da kayan kwalliyar dake kunshi a cikin wannan keyboard din.
Bayan wadannan alamun akwai kuma wasu tsare-tsare da ake yi wa keyboard kaman canza masa theme, da style na rubutu, da sautin da za ka ji duk lokacin da ka taba keyboard din a lokacin da ka ke rubutu, sai kuma kalmomin dictionary wadanda suke baiyana a saman keyboard yayin da ka ke rubutu. Amma bayanan wadannan za su zo a tutorial na gaba - wanda shine cigaban wannan rubutun.
Shin ka na bukatar koyan hada jersey a wayar Android?
Keyboard na zuwan waya ba kowane yare bane za ka samu a cikinsa. Mafi yawa keyboard ya kan zo da yaren kasashen turai kaman English, da French, da Dutch, da Spanish, da Turkish yake zuwa.
Misali, idan ka na bukatar yin rubutu da larabci, ko indiyance, ko sinanci ba za ka iya yin rubutu da wadannan yarukan ba, saboda a cikin wannan keyboard din babusu. Amma idan ka yi amfani da wani keyboard din za ka iya samun yare mai yawa, sannan za ka iya dakko yaren da kaga babu shi a cikin keyboard din. Ga wasu keyboard kadan wadanda za ku dauki daya ku yi aiki da shi a wayoyinku na Android a kyauta.
Shin ka na bukatar cigaban darasin nan wato yanda ake seta theme da font da sound a keyboard din Android?
2. GO keyboard
3. Emoji keyboard cute
4. TouchPal keyboard for Android Go
Bawai gaba daya keyboard din za ka yi aiki da su ba. Za ka dauki guda dayane a cikinsu wanda yake burgeka, sai ka setashi a wayarka - kaman yanda za mu ka yi bayani a kasa.
Ko ka san yanda ake boye bidiyo ko hoto a gallery a wayar Android?

2. Da farko, ka saukar da keyboard din da ka ke bukatar aiki da shi a wayarka a Play store. Sannan kuma ka na iya amfani da keyboard din da mu ka bayar da link din su a sama.
ka yi install din sa. Ka na gama install din sa sai ka bude shi. Ka na budeshi daga tsakiyan screen din wayarka, za ka ga an rubuta One. Sannan kasa da shi kuma za ka ga Enable Emoji Keyboard.
3. Abun da za ka fara yi shine sai ka shiga inda aka rubuta One din.

4. Ka na shiga wajen za ka ga ya kawoka wajen Language & input - kuma za ka ga zabi guda biyu a wajen wato Emoji keyboard da Google keyboard - sannan za ka samu an yi tick akan Google keyboard. Sai ka canza wannan tick din zuwa kan Emoji keyboard, ta hanyar taba kan Emoji keyboard din.

5. Ka na yin tick din Emoji keyboard za ka ga sun nuna ma Attention. Sai ka taba inda aka rubuta Ok wanda yake kasa da Attention din.

6. Ka na gama yin yanda mu ka ce ka yi za ka ga inda aka rubuta One din ya canza, ya koma Two. Idan wajen ya koma Two sai ka duba kasa da shi za ka ga Switch to Emoji keyboard. Daga nan sai ka shiga wajen da aka rubuta Two din.

7. Ka na shiga wajen za ka ga an kawoka wajen Choose input method. Idan ka lura kuma za ka samu an yi tick din English (US). Kai kuma sai ka canzashi, wato ka yi tick din Emoji keyboard English.

8. Ka na yin haka za ka ga wajen da aka rubuta Two din ya canza, ya koma Three. Idan ka duba kasa da shi kuma za ka ga an rubuta Sign in with Google. Idan ka na da adreshin e-mail din Google, wato Gmail sai ka shiga wajen ka yi Sign in da shi.
Idan kuma ba ka da shi kawai ka taba inda aka rubuta Skip ya na can kasa ta bangaren hannunka na dama.

9. Idan ka yi haka, shikenan ka gama seta keyboard a wayarka ta Android. Bayan ka gama komai kaman yanda mu ka nuna za ka ga keyboard din ya nuno ma abubuwa guda uku. Na farko shine Language, na biyu kuma Dictionaries, na karshen shine Finish. Idan application din ya nuna maka wadannan abubuwan sai ka fara shiga Language.

10. Ka na shiga Language za ka ga daga can sama an rubuta Emoji keyboard daga kasa da shi kuma za ka samu an yi tick akan Use system language. Shima daga kasa da shi za ka ga Active input methods kuma an yi tick din Emoji keyboard English(United State).

11. Idan ka yi kasa kuma za ka ga sauran yarukan da suke cikin keyboard din.

12. Wadannan yarukan da ka gani ba ka da daman yin aiki da su har sai ka saukar da su. Idan ka na bukatar saukar da wani yare daga cikinsu domin yin aiki da shi a keyboard din wayarka. Ka dawo baya ka shiga inda aka rubuta Dictionaries.

13. Ka na shiga cikin Dictionaries, za ka samu daga can sama an rubuta Language and Dictionary, daga kasa kuma an rubuta Additional dictionary, za ka ga yare iri daban-daban a wajen kaman yaren kasar Germany, wato Deutsch, da English, da French, da Italiano. Za ka samu cewa an yi tick akan English da France.
14. Duk yaren da kake so ka yi aiki da shi, ka duba kusa da sunansa akwai wani arrow ya na kallon kasa, sai ka taba wannan arrown. Za ka ga ya fara saukar da yaren.

15. Idan kuma ba za ka dakko wani yare ba, ko kuma ba ka da data, sai ka dawo baya ka shiga inda aka rubuta Ok wato Finish.

16. Ka na shiga wajen za ka ga keyboard din ya kawoka cikinsa.

Shin ko ka san cewa a na iya scanning din document a wayar Android?
Ya na kawoka cikinsa ka duba daga can sama za ka ga an rubuta Emoji keyboard. Daga kasa da shi kuma ta bangaren hannunka na hagu za ka ga Theme, da Font, da kuma Sound. Za mu tsaya a nan sai a tutorial na gaba, mu ci gaba daga inda muka tsaya.
Ko a iya nan ka tsaya ka gama seta keyboard a cikin wayarka ta Android. Amma za mu ci gaba a darasi na gaba wanda a cikinsa za mu nuna yanda ake seta theme, da font, da kuma sautin keyboard da kuma yanda ake ajiye kalma acikin dictionary na keyboard din.
Da fatan ana amfanuwa da rubuce rubuce da tutorial din da mu ke wallafawa a shafin nan. Idan kuna da tambaya za ku iya rubuta mana ita a wajen comment da ke kasa.
Mu na fatan za ku ci gaba da kasancewa da shafin nan, tare da gaiyato mana sauran 'yan uwa da abokan arziki suma su zo su amfana da rubuce rubucen shafin nan. Mun gode, sai mun sa ke ganin ku, a huta lafiya!
Menene keyboard?
Keyboard application ne da ake yin rubutu da shi a cikin waya. Kaman yanda kowace na'ura take zuwa da keyboard a matsayin hardware, itama wayar Android haka take zuwa da keyboard din ta amma a matsayin software, saboda amfanin mai wayar.Sai dai wasu masu amfani da waya su kan yi korafin cewa keyboard na zuwan wayar ba ya gamsar dasu. Wannan kuwa ya na faruwane saboda rashin wasu abubuwa da ake bukata domin a tsara rubutu dasu a keyboard din.
Ka karanta bayanin yanda ake seta custom theme a keyboard din Android?
Tsara rubutu da emoticon ko emoji ya kan sa wannan rubutun ya kayatar da mai karatu. Idan ka na karanta rubuce-rubuce a shafukan sadarwa na internet za ka ga mutane su na amfani da keyboard iri daban-daban domin tsara rubutunsu da kayan kwalliyar dake kunshi a cikin wannan keyboard din.
Bayan wadannan alamun akwai kuma wasu tsare-tsare da ake yi wa keyboard kaman canza masa theme, da style na rubutu, da sautin da za ka ji duk lokacin da ka taba keyboard din a lokacin da ka ke rubutu, sai kuma kalmomin dictionary wadanda suke baiyana a saman keyboard yayin da ka ke rubutu. Amma bayanan wadannan za su zo a tutorial na gaba - wanda shine cigaban wannan rubutun.
Shin ka na bukatar koyan hada jersey a wayar Android?
Keyboard na zuwan waya ba kowane yare bane za ka samu a cikinsa. Mafi yawa keyboard ya kan zo da yaren kasashen turai kaman English, da French, da Dutch, da Spanish, da Turkish yake zuwa.
Misali, idan ka na bukatar yin rubutu da larabci, ko indiyance, ko sinanci ba za ka iya yin rubutu da wadannan yarukan ba, saboda a cikin wannan keyboard din babusu. Amma idan ka yi amfani da wani keyboard din za ka iya samun yare mai yawa, sannan za ka iya dakko yaren da kaga babu shi a cikin keyboard din. Ga wasu keyboard kadan wadanda za ku dauki daya ku yi aiki da shi a wayoyinku na Android a kyauta.
Shin ka na bukatar cigaban darasin nan wato yanda ake seta theme da font da sound a keyboard din Android?
Ga jerin keyboard din
1. Gboard2. GO keyboard
3. Emoji keyboard cute
4. TouchPal keyboard for Android Go
Bawai gaba daya keyboard din za ka yi aiki da su ba. Za ka dauki guda dayane a cikinsu wanda yake burgeka, sai ka setashi a wayarka - kaman yanda za mu ka yi bayani a kasa.
Ko ka san yanda ake boye bidiyo ko hoto a gallery a wayar Android?
Ga yanda ake seta keyboard
1. Kafin mu yi nisa a cikin bayanin, ga yanda keyboard na zuwan waya ya ke a wayata. Za mu yi misali da Emoji keyboard a cikin tutorial din nan.2. Da farko, ka saukar da keyboard din da ka ke bukatar aiki da shi a wayarka a Play store. Sannan kuma ka na iya amfani da keyboard din da mu ka bayar da link din su a sama.
ka yi install din sa. Ka na gama install din sa sai ka bude shi. Ka na budeshi daga tsakiyan screen din wayarka, za ka ga an rubuta One. Sannan kasa da shi kuma za ka ga Enable Emoji Keyboard.
3. Abun da za ka fara yi shine sai ka shiga inda aka rubuta One din.
4. Ka na shiga wajen za ka ga ya kawoka wajen Language & input - kuma za ka ga zabi guda biyu a wajen wato Emoji keyboard da Google keyboard - sannan za ka samu an yi tick akan Google keyboard. Sai ka canza wannan tick din zuwa kan Emoji keyboard, ta hanyar taba kan Emoji keyboard din.
5. Ka na yin tick din Emoji keyboard za ka ga sun nuna ma Attention. Sai ka taba inda aka rubuta Ok wanda yake kasa da Attention din.
6. Ka na gama yin yanda mu ka ce ka yi za ka ga inda aka rubuta One din ya canza, ya koma Two. Idan wajen ya koma Two sai ka duba kasa da shi za ka ga Switch to Emoji keyboard. Daga nan sai ka shiga wajen da aka rubuta Two din.
7. Ka na shiga wajen za ka ga an kawoka wajen Choose input method. Idan ka lura kuma za ka samu an yi tick din English (US). Kai kuma sai ka canzashi, wato ka yi tick din Emoji keyboard English.
8. Ka na yin haka za ka ga wajen da aka rubuta Two din ya canza, ya koma Three. Idan ka duba kasa da shi kuma za ka ga an rubuta Sign in with Google. Idan ka na da adreshin e-mail din Google, wato Gmail sai ka shiga wajen ka yi Sign in da shi.
Idan kuma ba ka da shi kawai ka taba inda aka rubuta Skip ya na can kasa ta bangaren hannunka na dama.
9. Idan ka yi haka, shikenan ka gama seta keyboard a wayarka ta Android. Bayan ka gama komai kaman yanda mu ka nuna za ka ga keyboard din ya nuno ma abubuwa guda uku. Na farko shine Language, na biyu kuma Dictionaries, na karshen shine Finish. Idan application din ya nuna maka wadannan abubuwan sai ka fara shiga Language.
10. Ka na shiga Language za ka ga daga can sama an rubuta Emoji keyboard daga kasa da shi kuma za ka samu an yi tick akan Use system language. Shima daga kasa da shi za ka ga Active input methods kuma an yi tick din Emoji keyboard English(United State).
11. Idan ka yi kasa kuma za ka ga sauran yarukan da suke cikin keyboard din.
12. Wadannan yarukan da ka gani ba ka da daman yin aiki da su har sai ka saukar da su. Idan ka na bukatar saukar da wani yare daga cikinsu domin yin aiki da shi a keyboard din wayarka. Ka dawo baya ka shiga inda aka rubuta Dictionaries.
13. Ka na shiga cikin Dictionaries, za ka samu daga can sama an rubuta Language and Dictionary, daga kasa kuma an rubuta Additional dictionary, za ka ga yare iri daban-daban a wajen kaman yaren kasar Germany, wato Deutsch, da English, da French, da Italiano. Za ka samu cewa an yi tick akan English da France.
14. Duk yaren da kake so ka yi aiki da shi, ka duba kusa da sunansa akwai wani arrow ya na kallon kasa, sai ka taba wannan arrown. Za ka ga ya fara saukar da yaren.
15. Idan kuma ba za ka dakko wani yare ba, ko kuma ba ka da data, sai ka dawo baya ka shiga inda aka rubuta Ok wato Finish.
16. Ka na shiga wajen za ka ga keyboard din ya kawoka cikinsa.
Shin ko ka san cewa a na iya scanning din document a wayar Android?
Ya na kawoka cikinsa ka duba daga can sama za ka ga an rubuta Emoji keyboard. Daga kasa da shi kuma ta bangaren hannunka na hagu za ka ga Theme, da Font, da kuma Sound. Za mu tsaya a nan sai a tutorial na gaba, mu ci gaba daga inda muka tsaya.
Ko a iya nan ka tsaya ka gama seta keyboard a cikin wayarka ta Android. Amma za mu ci gaba a darasi na gaba wanda a cikinsa za mu nuna yanda ake seta theme, da font, da kuma sautin keyboard da kuma yanda ake ajiye kalma acikin dictionary na keyboard din.
Da fatan ana amfanuwa da rubuce rubuce da tutorial din da mu ke wallafawa a shafin nan. Idan kuna da tambaya za ku iya rubuta mana ita a wajen comment da ke kasa.
Mu na fatan za ku ci gaba da kasancewa da shafin nan, tare da gaiyato mana sauran 'yan uwa da abokan arziki suma su zo su amfana da rubuce rubucen shafin nan. Mun gode, sai mun sa ke ganin ku, a huta lafiya!
Leave a Comment