Yanda ake boye hoto ko bidiyo a gallery a wayar Android
Akwai wasu hotuna ko bidiyo wadanda watakila za ka so ka boye su saboda ba ka so wani idan ya karbi wayarka ya gansu. Ko kuma idan ka na da wani hoto ko bidiyo wanda ba ka so ka rasa su wannan ma zai sa ka boye wasu file a Gallery na wayarka ta yanda babu wanda zai iya ganinsu.
Ana boye wasu abubuwan ne saboda tsaro, ko sirri, ko kuma dai abun da ba a so wani ko wasu su gani. Bayan haka kuma ana boye wasu abubuwan saboda a ajiye su domin a yi aiki da su a gaba.
Ba kaman yanda ake amfani da Gallery vault ba, idan za a boye abubuwa kaman hoto ko bidiyo a cikin Gallery. Akwai wasu application da dama da ake amfani da su domin a boye abubuwa a cikin waya - amma a wannan tutorial din yanda ake boye abubuwa a Gallery za mu yi.
Kawai abun da za mu ce a nan shine a tanadi kayan aiki. Sai a cigaba da karanta tutorial din har sai an karanta gaba daya. Mun tanadi kayan aiki kaman yanda mu ke tanadar kayan aiki a kowane daga cikin tutorial din mu.
Application din da ake bukata
1. Es File Explore
Bayan ka tanadi kayan aiki wato application din da mu ka bayar da sunansa a sama - sai ka yi kasa ka ci gaba da karatu akan yanda ake yi.
Ga yanda ake boye su:
1. Da farko, ka saukar da application din a Play store ta hanyar link din da mu ka bayar a sama, ko kuma ka shiga nan ka saukar da application din a shafin apkpure.com idan ba ka iya shiga Play store a wayarka. Bayan ka saukar da application din sai ka yi install nashi a wayarka. Kafin mu yi nisa da farko ga yanda Gallery ya ke, kuma za mu boye folda mai suna Camera.
Shin ka san yanda ake dawo da abubuwan da aka goge a wayar Android?
2. Bayan ka gama duk abun da mu ka ce ka yi a sama, sai ka bude application din. Ka na bude shi, ka duba, daga can kasa ta bangaren hannunka na hagu, za ka ga inda aka rubuta New tare da alamar kari wato +, sai ka taba wajen.
3. Ka na taba inda aka rubuta New din za ka ga application din ya nuno maka zabi guda biyu. Wato File, da Folder, sai ka taba na biyun wato Folder.
4. Ka na taba zabi na biyun wato Folder, application din zai nuna maka wajen yin rubutu. Sai ka rubuta .private sannan ka taba Ok. Ka da a manta dole ne sai an rubuta alamar aya wato full stop, ko period kafin a rubuta private din.
5. Ka na yin haka za ka ga wannan foldar da ka gama kirkira ta bace, ba a ganin ta. Daga nan sai ka duba can sama ta bangaren hannunka na hagu, ka taba wajen da ka ga alaman zanen waya da duniya.
6. Ka na taba wajen za ka ga wasu zabuka, guda hudu ko biyar ko kuma sama da haka. Zabukan su ne Favorite, da Local, da Library, da Network, da kuma Tools - sai ka taba na karshen wato Tools.
7. Ka na taba Tools din za ka ga ya nuno maka wasu zabuka. Ya na nuna maka wadannan zabukan sai ka yi kasa ka je daidai inda aka rubuta Show hidden files, kuma za ka same shi a rufe wato a OFF.
8. Abun da za ka yi sai ka bude shi, wato ka canza shi daga OFF zuwa ON. Ka na ganinsa a rufe sai ka taba kan OFF din za ka ga ya bude, wato ya dawo ON.
Ka san yanda ake compress da extract na abubuwan cikin zip file a wayar Android?
9. Ka na budewa, za ka ga wancan foldar wato .private wanda ka kirkira a baya ta baiyana.
10. Ka na gama matakan nan na sama sai ka je ka yi move na file ko foldar da ka ke so ka boyeta zuwa cikin .private - za mu yi misali da folda mai suna Camera wanda ta ke cikin DCIM wato inda hotunan da ake dauka da Camera su ke zama. Saboda haka sai ka je ka bude DCIM.
11. Ka na bude DCIM za ka ga folda mai suna Camera a cikinta, sai ka yi marking din ta, ka duba daga kasa za ka ga alamar almakashi jikinsa an rubuta Cut, sai ka taba wajen.
12. Ka na taba Cut sai ka dawo baya ka shiga cikin folda mai suna .private din.
13. Ka na shiga foldar sai ka yi paste din wancan foldar Cameran a ciki.
14. Ka na gama move na wancan foldar zuwa cikin .private din, sai ka dawo cikin Gallery ka duba ka gani, za ka ga wannan foldar wato Camera ta bace gaba daya ba a ganin ta.
Shin ko kasan menene Google play service, da kuma yanda ake update nashi a wayar Android?
Ga yanda ake dawo da su:
1. Idan kuma ka na so ka dawo da su bayan ka boye su, sai ka koma cikin foldar .private din ka bude ta.
2. Ka na bude foldar za ka samu wancan foldar da ka yi move nata zuwa nan - daga nan sai ka sake marking na wannan foldar, sai ka taba Cut, kaman yanda ka yi a baya. Ka na yin haka sai ka futo a cikin foldar.
3. Ka na futowa sai ka dawo ka ajiye foldar a inda take na asali. A misalin da mu ka yi, mun dakko foldar Camera daga cikin DCIM ne. Yanzu kuma za mu sake dawo da ita inda take na asali wato cikin DCIM.
4. Ka na dawowa cikin DCIM, sai ka yi paste na ta a nan.
5. Ka na dawo da wannan foldar inda take na asali za ka ga foldar ta dawo, ta baiyana a cikin Gallery.
Wannan ita ce hanyar da ake bi mafi sauki da ake boye hoto ko bidiyo a cikin Gallery. Hanyar nan ba ta da wahala, kuma application guda daya ake bukata idan za ayi wannan aikin.
Akwai wata hanya da ake amfani da wani application mai suna Gallery vault wanda sai an seta password, sannan ake iya boye abubuwa a cikin Gallery da shi. Ba kaman wancan hanyar ba, a wannan hanyar da muka nuna ba a amfani da password.
Idan ka bi ta wannan hanya cikin sauki za ka boye abubuwa a cikin Gallery na wayar ka ta Android - kuma ka dawo da su ana ganin su kaman yanda suke da farko.
Za mu tsaya anan sai mun zo da wani tutorial din a gaba. Da fatan ana amfanuwa da abubuwan da ake karantawa a shafin nan. Idan kuma kuna da tambayoyi za ku iya ajiye mana su a wajen comment dake can kasa.
Mun gode, da kawo ziyara shafin nan fatan za mu sake ganin ku, sannan kuma muna bukatar ku gaiyato mana abokan ku suma su zo su amfana da abubuwan mu ke wallafawa a shafin nan. Mun gode, sai mun sake ganin ku, a huta lafiya!

Leave a Comment