Yanda ake hada jersey a wayar Android
Jersey shine kayan da 'yan wasa kaman kwallon kafa su ke sakawa a lokacin da za su yi wasa da wata kungiya. Wannan kayan shi ya ke bambanta tsakanin kungiyoyin - saboda ko da 'yan wasan da kansu sun fi bambance cewa wannan dan kungiyarsune, wannan ba dan kungiyarsu bane. Mai kallo ma ya kan bambance dan wasan wannan kungiyar da dan wasan wancan kungiyar.
Akwai jerseyn da ake hadawa a cikin wayoyi wadanda ake daurasu a shafukan sada zumunta domin burgewa.
Ga yanda ake hadawa
1. Ka saukar da Make My Football Jersey a wayarka. Bayan ka gama saukar da shi sai ka yi install dinsa, sannan ka budeshi. Ka na budeshi za ka ga jerseyn Brazil. Sai ka duba daga can sama za ka ga wajen rubuta suna da lamba.

2. Wajen rubuta sunan za ka ga an rubuta NAME, wajen rubuta lamba kuma an rubuta NO. Sai ka shiga wajen rubuta suna ka rubuta sunanka, misali, NURA. Sannan ka shiga wajen rubuta lamba ka rubuta lambar da ka ke bukata, misali, 10.

3. Bayan ka gama rubuta suna da lamba, sai ka wajen da aka rubuta ✔DONE.

4. Ka na taba wajen za ka ga sunan da ka rubuta da lambar a jikin jerseyn. Ka duba kasa da jerseyn za ka ga inda aka rubuta Save - sai ka taba wajen.

Ka na taba Save din za ka ga application din ya rubuta maka Image saved a karkashin jerseyn.

Idan kuma ka na bukatar zaban jerseyn wata kasa sai ka duba daga can sama a bangaren hagu za ka ga wasu layi guda uku daya akan daya, sai ka tabasu. Ka na tabasu za ka ga tutotin kasashe dadama sun baiyana.

Sai ka yi kasa za ka ga sauran tutotin, sai ka zabi tutar kasar da ka ke bukatar hada tutarta.

5. Zan yi misali ta hanyar hada jerseyn kasata wato Nigeria. Na zabi tutarta.

Ka na taba tutar kasar za ka ga jerseynta ya baiyana. Sai ka rubuta sunanka, da lambarka, sannan ka taba ✔DONE, kaman yanda ka yi a farko. Za ka ga suna da lambar sun hau jerseyn. Daga karshe, kuma sai ka taba inda aka rubuta Save.

Ka na taba wajen a take za ka ga application din ya rubuta Image saved - kaman dai yanda ka yi a farko.

Wannan application din iya kasashen da su ka je gasar cin kofin duniya na dubu biyu da sha hudu ne wanda aka yi a kasar Brazil. Kuma akwai website din da ake hada jersey a cikinsa ta online. Amma a wannan application din offline ake hadawa.
Kaman dai yanda aka gani wannan matakan ba su da wahala ko kadan. Saboda haka mu na iya cewa kowa zai iya.
Ina ga za mu dakata anan da fatan ana amfanuwa da rubuce rubucen da ake karantawa a shafin nan. Duk wanda ya ke da tambaya sai ya yi kasa wajen comment ya rubuta mana ita. Mu kuma za mu bashi amsa idan Allah ya sa mun sani.
Ku na iya gaiyato abokanku zuwa shafin nan domin su ma su amfana da rubuce rubucen da mu ke wallafawa a shafin nan. Mun gode, sai mun sake ganinku, a huta lafiya✋

Leave a Comment