Yanda ake seta yaren larabci a keyboard din wayar Android

Shin kana bukatar canza yaren keyboard na wayarka? Ko kuma kana so ka yi amfani da wani yare a keyboard na wayarka? Kana son ka yi rubuta da harufan larabci a wayarka? Kana so ka koyi yanda ake amfani da wani yare a keyboard din wayar android bayan turanci?

Idan kana son ka koyi wadannan abubuwan a wayar Android, kawai ka shirya domin ka zo wajen. Keyboard na waya yakan zo da yaren turanci, kuma akan samu wasu mutane da suke so su yi rubuta da larabci amma abun ya ci tura, saboda ba yaren larabci babu yaren larabci a cikin keyboard din.

Bawai larabci kadai ba akwai wasu yare kaman yaren India, da China, da Russia, da Greece da makamantansu. Wadanda harufan rubutusu sun banbanta da na turancin England ko France. Wasu kanso su yi amfani da wani yare wajen rubutu - amma sun kasa saboda babu yaren, ko kuma su na tunanin cewa turancine kadai ake iya aiki dashi wajen rubutu. Za ka iya amfani da yare daban daban a keyboard na wayarka idan ka bi wadannan matakan masu zuwa a kasa.
Ga Yanda Ake Yi
1. Da farko kafin ka fara seta larabci a keyboard din wayarka, yana da kyau ka duba bayanin da mu ka yi akan yanda ake saka keyboard, da kuma yanda ake seta theme, da font na keyboard din duk dai a wayar Android. Idan kuma ka karanta wancan bayanin, sai ka ci gaba da karantawa. Ka je ka shiga Emoji Keyboard, kana shiga daga can sama a bangaren dama, za ka ga wani dan karamin hoton gear, sai ka tabashi.


2. Kana tabashi zai kawoka cikin Settings na keyboard din, sai ka shiga Language and Dictionary.


3. Kana shiga wajen sai ka shiga Input languages.


4. Kana shiga Input languages - za ka ga wajen seta yaren da ake amfani da shi a keyboard. Idan ka lura za ka ga an yi tick akan Use system language.


5. Sai ka cire tick din da yake kan Use system language, sannan ka yi kasa.


6. Kana yin kasa za ka ga yare kala-kala wadanda suke zuwa a cikin keyboard din. Ka duba a cikin yarukan za ka ga yaren larabci wato Emoji Keyboard Arabic.


7. Daga nan sai ka yi tick akan yaren da kake so ka yi aiki da shi a wayarka. Dama mun ce za mu seta yaren larabci ne - kawai sai ka yi tick akan Emoji Keyboard Arabic.


Kana tick yin akan larabcin sai ka dawo baya, ka futa a cikin keyboard din, ka je wajen rubuta sako za ka ga keyboard naka ya canza, ya koma larabci.

Wadannan matakan ake bi idan za a yi amfani da wani yare a keyboard din wayar Android. Matakan dai ba su da wahala kaman yanda ake iya gani.

Za mu tsaya anan da fatan ana amfanuwa da darusan cikin shafin nan - sannan kuna iya tambaya akan abun da baku ganeba, a wajen comment dake kasa, insha Allahu za ku samu amsa idan Allah ya sa mun sani.

Da fatan za mu sake ganinku, kuna iya gaiyato abokanku su zo shafin nan su amfana, mun gode, sai mun sake ganinku!

No comments

Powered by Blogger.