Mece ce Manhajar iOS?
Kamfanin fasaha na Apple, babban kamfanin fasaha ne a duniya, shine kamfanin da yake kera na'ura mai kwakwalwa wanda ake kira Mac da wayoyi samfurin iPad da iPhone. A zamanin yau wayoyin kamfanin Apple sune wayoyin manyan mutane da 'yan boko da samari tare da 'yan mata adon gari . Domin wayoyin kamfanin Apple sun bambanta da wayoyin Android na hadin gwuiwar wasu kamfanonin fasaha tare da Google - wadanda suma suna daga cikin wayoyin da aka fi amfani da su a duniya.
Menene OS?
OS ya na nufin Operating System. A takaice ya na nufin abun da ya ke baka daman tafiyar da wayarka. OS shi ne ya ke tsakaninka da wayarka, wato shi ne ya ke gano inda ka taba, ko ka shiga, ko ka bayar da umarni wayarka ta yi, sannan ya umarci application din da ya ke wannan aikin, ko kuma application din da ka umarta ya yi aiki. A yau fasahar OS ta cika wayoyin da suke hannun jama'a ta ko ina.Shin ko ka san yanda ake hada intro a wayar Android?
Manyan wayoyin tafi-da-gidanka na OS da iOS kusan aikinsu daya, amma sun banbanta. Wayoyin OS sune Android, iOS kuma sune iPad da iPhone. OS da iOS duk su na aikine akan OS wato operating system. Kaman OS din Android, Operating system din Apple wato iOS ya fi shekaru goma da shigowa hannun jama'a bayan yawaitar wayoyinsu a duniya.
Me iOS yake nufi?
Ba sai mun yi wani dogon bayani game da wadannan takaitattun kalmomin ba. A takaice iOS yana nufin iPhone Operating System ko kuma iPad Operating System, wato dai a takaice ana nufin OS na wayoyin kamfani Apple.Tambari ko rubutun iOS shine abu na farko da zaka fara gani idan ka kunna tablet ko wayarka ta iPhone. Bayan ka kunna wayarka duk inda ka shiga, ko za ka shiga ya na karkashin tafiyarwar operating system ne. Operating system hadakar aikine tsakanin hardware da software. Wadanda za su baka daman karawa ko rage hasken waya, ko bude Bluetooth da rufeshi, ko bude Wi-Fi da rufeshi, ko daukar hoto da sauransu.
Haka kuma iOS ta kan ba ka dama ka tafiyar da application din da ka dakko a App Store - wato a rumbun manhaja na kamfanin Apple.<
Shin ko ka karanta bayanin menene battery?, da kuma asalinsa.
Wane version din iOS ne a wayata?
Kaman kamfanin Google, Apple su ma su kan sabunta manhajarsu lokaci bayan lokaci. Duk lokacin da su ka sabunta manhajarsu to wasu sabbin abubuwa za ka gani a wayar wadanda babu su a cikin tsofin version. Har-wa-yau su ma duk lokacin da su ka sabunta manhajarsu, su kan bata lamba a maimakon suna da Google suke sakawa sabbin manhajojin Android.Menene iOS 10
Sabon version na iOS wanda ya zamo iOS 10, sabbin wayoyin iPad ko iPhone sun futo da shi a watan Satumba na shekarar dubu biyu da sha shida (September, 2016). Kuma version din ya zo a kan iPhone 7 da iPhone 7 plus, wanda Apple su ka kaddamar sati biyu bayan sun baiyana iOS 10.iOS 10 ya zo da karin wasu abubuwa da bangarori wanda ya hada da sabunta Maps, da Messages, da sauran abubuwa mallakin kamfanin Apple.
Menene iOS 11?
Kamfanin Apple ya yi amfani da taron WWDC na shekarar dubu biyu da sha bakwai (2017) ya baiyana sabuwar manhajarsa da za ta futo a shekarar - wanda ya sabunta ta, kuma wanda za ta maye gurbin iOS 10 da ake amfani da ita iPhone da iPad.Futowar iOS 11 ya zamo babban canji ga iPad da iPhone, da kuma masu amfani da su. Saboda tsofin application duk an maye gurbinsu da sabbi ga kuma wasu abubuwa da aka kara tsarasu.
Yaushe iOS 11 zata futo?
Manhajar iOS 11 ta Apple ta futo tun a watan September na 2017, sannan kowa zai iya sabunta tsohuwar manhajarsa ta iOS 10 zuwa iOS 11. A duk lokacin da wata sabuwar manhajar iOS ta futo, ko kuma Apple su ka sabunta ta - za ka ga ana sanar da kai, idan ka shiga sanarwar za a nuna maka inda za ka shiga, ka sabunta ta zuwa sabuwa.Shin ka na so ka san bambancin wayar iOS da Android?
Leave a Comment