Ko Kasan Menene Visible Light?

Visible Light wato farin haske, nau'ine na karfi (energy) wanda yake bamu dama mu kalli ko wane abu da launinsa a idanuwan mu. Farin haske kaman hasken rana yana dauke da haske gaba daya - wato yana kunshe da hasken da muke iya gani da idanunmu, da wadanda bama iya ganinsu.

Farin haske daya ne daga cikin electromagnetic radiation wadanda suke iya tafiya a cikin sarari ba tare da taimakon wani abu ba. Haske shine abun da yafi kowane abu sauri kaman yanda binciken kimiyya ya tabbatar. Saboda haske yana da saurin tafiyar mita miliyan dari uku a duk second daya (300 000 000m/s), wato dai dai da tafiyar kilomita dubu dari uku a duk second daya (300 000km/s).

Akwai nau'ukan haske guda bakwai - amma daga cikinsu guda daya ne kawai muke iya gani da idanunmu kuma shine visible light - wanda muke bayaninsa a yanzu. Sauran guda shidan bama iya ganinsu, amma muna amfani dasu a fannoni dadama na rayuwa. Misali, kaman X-rays ana amfani da su wajen daukan hoton kayan cikin mutum ko dabba. Haka kuma ana amfani da wannan hasken wajen binciken injinan jiragen sama. Tashoshi jiragen sama suna amfani dashi wajen bincika kayan da suke cikin akwatin matafiya.

Wasu hasken ana amfani da su ne a bangaren sadarwa da fasahar daukan hoto. Infrared nau'ine na haske mai dauke da jan launi wanda idonmu baya iya ganinsa. Sai dai muna iya jinsa a jikinmu. Idan ka shiga cikin hasken rana za ka ji zafi. Wannan zafin da kake ji a cikin hasken rana yana futowane ta bangaren infrared.

Akwai su Radiowaves, da Microwaves wadanda ake amfani dasu wajen sadarwar zamani. Ana amfani da Microwaves, da Radiowaves a bangaren sadarwar wayoyi, da na'urori, da talabijin, da kuma rediyo ta hanyar satellite.

Visible light shine hasken dake bamu dama muyi kallo wanda yake zuwa mana daga rana. Haka kuma akwai na'urori da ake amfani da su domin samar da farin haske. Visible light yanda muke ganinsa a idonmu muna ganin farin haskene. Amma ba farin haske bane, idan akayi amfani da wata na'ura mai suna spectroscope za a gane cewa ba farin haske bane. Haduwar haske mai launin shudi, da kore, da ja su suke ba da farin haske.

Ana amfani da farin haske wajen daukan hoto. Haka kuma ana amfani da farin haske wajen sadarwar internet ta cikin optical fibre cable. Bayan wannan kuma a fannin kiwon lafiya ana amfani da visible light a cikin optical fibre cable domin daukan hotunan kayan ciki na mutum.

Kuma ana amfani da visible light a cikin na'urar projector, wanda ake haskata a jikin bango a manyan gidajen kallo na zamani.

Haske yana da amfani sosai a cikin rayuwarmu ta yau da kullum. Muna amfani da kananun na'urorin hannu domin yin aiki a cikin dubu.

Za mu tsaya a nan da fatan ana amfanuwa da rubutucen da mukeyi a shafin nan. Mun gode da kawo ziyara shafin nan na kimiya da fasahar zamani. Mun gode, sai mun sake ganinku.

No comments

Powered by Blogger.