Menene Android 10?

Android 10 ita ce sabuwar version din Android ta wannan lokacin wanda ta zo da wasu tsare tsare da bangarori masu mahimmaci fiye da wadanda ake da su a version din Android na baya wadanda ake amfani da su kafin ita. Android 10 kaman yanda Google su ka rubuta ta na dauke da sabbin bangarori wanda aka kirkirosu a baya bayan nan.

Android 10 ita ce babbar manhajar wayoyin Android OS futowa ta goma. Haka kuma ita ce version na goma sha bakwai a cikin jerin version din wayar Android. Wannan version din an futar da shi a ranar uku ga watan Satumba na shekara ta dubu biyu da sha tara (3rd September, 2019) - amma kafin nan Google sun sakawa version din suna "Android Q" daga baya su ka canza masa suna zuwa "Android 10". Sunan Android 10 ya sabawa tsarin sunan version din Android wanda Google su ke sakawa duk wani version a baya. Saboda a baya su na sakawa version din su sunan wani kayan zaki ko makulashe kaman Lollipop (version 5) da Marshmallow (version 6).

Google ya futar da Android 10 beta ta farko da sunan "Android Q" a ranar sha uku ga watan Maris na shekara ta dubu biyu da sha tara (13 March, 2019) - daga cikin jerin wayoyinsa na Pixel kuma a jeri na farko wato wayoyin Pixel da Pixel XL bayan bukatar hakan ta yawaita ga masu amfani da wayoyin Android.

Android 10 a hukumance akwaita kaman yanda Google su ka bayar da sanarwar. Amma fa a halin yanzu wayoyi ba su fara futowa da version din ba. Sai dai ana tsammanin futowar wayoyi masu dauke da version din a cikin shekaran nan ta 2020 ko shekara ta gaba 2021. Sai dai wadannan wayoyin na kamfanin Google wato Pixel 3 da Pixel 3 XL, da Pixel 3a da Pixel 3a XL, da Pixel 2 da Pixel 2 XL, da Pixel da Pixel XL, da kuma OnePlus 7T, da OnePlus 7T Pro su kadai ne za a iya cewa su na dauke da version din "Android 10" ko kuma "Android Q".


Shin wai menene sabo a Android 10?

Sabon version din Android wato Android 10 an kirkirosa bayan da bukatar bunkasar da version din Android na baya wato 'Pie' ta yi yawa. Android 10 ta zo da theme mai duhu (dark theme) wanda zai sa cikin wayar ya yi duhu gaba daya kaman yanda ake yi a wayoyin iPhone da iPad. Tsarin saka duhu a Android 10 kala biyune na farkon kai ne za ka seta theme domin wayar ta yi duhu, na biyu kuma idan wayar cajinta ya yi kasa sai ka seta ta Battery saver mode, sai wayar ta yi duhu.

Sannan version din Android 10 ya zo da tsarin "smart reply for all messaging apps", wato tsarin da ya ke bayar da daman a yi reply din sakonni ga duk wani application din da ake aika sakonni da shi a wayar ta hanyar fahimtar sakon da a ka turoma tare da rubutama martani. Misali, idan aka aikoma sakon Hi, za ka ga wayar ta rubutoma How are you? da Hi, how are you? da kuma What's up? to a cikin wadannan ukun ka na taba daya za ka ga sakon ya tafi, kenan ta yi maka reply akan sakon bayan sakon ya shigo wayarka. Amma fa wannan tsarin ya na aikine da manyan yarukan duniya musamman da turancin burtaniya (UK English) da na amurka (US English) ko faransanci (French).

Bayan wannan kuma idan sakon da aka turoma cikinsa akwai link, wayar za ta nemi ta bude Chrome, domin ganin menene a cikin wannan link din da aka turoma.

Bayan wannan version din Android 10 ya zo da hanyar da za ta ba ka daman amfani da Wi-Fi din wani ta hanyar yin scanning din barcode. Sannan kuma version din Android 10 ya zo da network din 5G wanda shima ake tsammanin zai shigo cikin wayoyi a shekaran nan ko shekara ta gaba wato 2021.

Wannan shi ne bayain Android 10 a takaice, amma za mu dawo mu sabuntashi a duk lokacin da bukatar hakan ta taso. Domin ci gaba da samun bayanai akan fasaha a ci gaba da kasancewa da shafin nan.

Sannan kofa a bude ta ke ga mai tambaya, saboda haka sai a yi kasa wajen comment a rubuta, za a samu amsa idan mun sani.

Mu na fatan sake ganinku, sannan mu na godiya akan ziyartar shafin nan da ku ke yi, ba dare ba rana, mun gode, a huta lafiya.

No comments

Powered by Blogger.