Menene computer storage?

Na'urori ma su kwakwalwa wato computer da wayoyin hannu su na ajiye bayanai ta hanyar file akansu a matsayin binary code. Waka, da bidiyo, da hoto, da game ko application da mu ke ajiyewa akan wayoyi da computer su na zama ne a matsayin binary wato 0 da 1. Wadannan ma'ajiyoyin su ma iri daban dabanne ko kuma ace girma girma, wato wannan ya fi wancan daukan abubuwa.

Akwai ma'ajiyi iri daban daban na computer da waya, wadanda muke amfani dasu a bangarori dadama. Da ikon Allah zanyi bayanin wadannan ma'ajiyan da kuma girman su.

Menene bit?

Bit shine dan karamin ma'ajiyi na na'ura, kuma ya na iya daukan abubuwa guda biyu kadai, a matsayin true da false, ko yes da no, ko kuma on da off, amma dai amfani da 0 da 1. Bit guda takwas su ne su ke zama byte daya. Shi kuma byte daya ya na iya daukan abubuwa guda dari biyu da hamsin da shida (256 values). Ba wai bidiyo ko hoto ko waka dari biyu da hamsin da shida ake nufi ba, wasu kananun abubuwa ne da nauyin su bai kai nauyin harafi daya ba.

Watakila wani zai yi mamakin cewa bit ya kan dauki abubuwa biyu ne kadai, sannan kuma bit takwas su ne byte daya. Amma kuma byte daya ya na daukan abubuwa dari biyu da hamsin da shida. Alhali kuma idan aka ce biyu sau takwas, amsar ita ce sha shida, ba dari biyu da hamsin da shida ba.

To ga yanda abun ya ke za ka lissafa biyu sau biyu abun da ka samu shima za ka ribanya shi sau biyu har sai ka yi haka sau takwas. Ga yanda ake yi biyu sau biyu (2x2) hudu kenan (4). Hudu sau biyu (4x2) takwas (8). Takwas sau biyu (8x2) sha shida (16). Sha shida sau biyu (16x2) talatin da biyu (32). Talatin da biyu sau biyu (32x2) sittin da hudu (64). Sittin da hudu sau biyu (64x2) ya kama dari da ashirin da takwas (128). Dari da ashirin da takwas sau biyu (128x2) ya zama dari biyu da hamsin da shida (256).

Ga sunayen girman storage din computer, kaman haka:
1. Byte
2. Kilobyte
3. Megabyte
4. Gigabyte
5. Terabyte
6. Petabyte
7. Exabyte
8. Zettabyte
9. Yottabyte

1. Bayanin byte

Byte ya na iya daukan lamba, ko harafi, ko launi, ko html da sauransu. Idan aka kara adadin byte zai dauki lambobi, jimlolin rubutu, da sauransu. Byte guda dubu daya da ashirin da hudu shine kilobyte daya.

2. Kilobytes

Matsakaicin hoto mai kyau ya na kai nauyin kilobyte dari (100kB) ko sama da haka. Kilobyte guda dubu daya da ashirin da hudu shine ya ke zama Megabyte daya. Mega ya na nufin miliyon, wato akwai byte miliyon daya da wani abu a cikin Megabyte daya kenan.

3. Megabytes

Sautin murya (audio) mai tsawon minti daya ya na iya kai girman Megabyte daya (1MB). Floppy disk mai tsawon inchi uku da rabi (3.5 inch) ya na kai girman megabyte daya da digo arba'in da hudu (1.44MB).

4. Gigabytes

Faifayin CD na bidiyon CD, ko VCD ya na kai girman Megabyte dari bakwai (700MB), wato kusan Gigabyte daya. Gigabyte daya ya na daukan Megabyte dubu daya da ashirin da hudu (1024MB).

Faifayin bidiyon CD ko na DVD su na daukan Gigabyte guda hudu da digo bakwai (4.7GB). Faifayin DVD na Blue ray disc wanda ake daukar season film da shi ya na daukan Gigabyte ashirin da biyar (25GB). Flash drive ya na daukan Gigabyte talatin da biyu (32GB), kuma akwai manyansa ma su girman Gigabyte sittin da hudu (64GB) da kuma Gigabyte dari da ashirin da takwas (128GB).

5. Terabyte

Terabyte ya na daukan gigabyte dubu daya da ashirin da hudu (1024GB). Sannan hard drive ya na daukan Terabyte daga daya zuwa takwas (1-8TB).

6. Petabyte

Petabyte ya na daukan terabyte dubu daya da ashirin da hudu (1024TB). Kuma kamfanonin da su ke samar da hosting ga mutane a internet kamansu Godaddy da Bluehost, da su YouTube, da Facebook, da Amazon, da Instagram duk suna amfani da ma'ajiyi mai daukan terabyte dubu daya da ashirin da hudu (1024TB).

7. Exabyte

Exabyte ya na daukan petabyte dubu daya da ashirin da hudu (1024PB). Gaba daya hidimomin internet (internet traffic) na duniya a wata daya ana auna girmansa a matsayin Exabyte, ko kuma Petabyte dubu da ashirin da hudu (1024PB).

8. Zettabyte

Sai kuma na biyun karshe wato Zettabyte wanda duk guda dayansa ya na daidai da Exabyte guda dubu daya da ashirin da hudu (1024EB).

9. Yottabyte

Na karshe kuma shine Yottabyte (1024ZB). Wadannan biyun na karshe har zuwa yanzu ban san a ina ake ai da su ba. Daga karshe kuma mu na fatan ana jin dadin kasancewa da shafin nan. Da fatan a na amfanuwa da darusan fasaha wadanda mu ke rubutawa a shafin nan.

Za mu dakata a nan da fatan za mu sake ganinku, duk mai tambaya sai ya yi kasa wajen comment ya rubuta. Mun gode, a huta lafiya.

No comments

Powered by Blogger.