Yanda Ake Saka Theme A WordPress
A darusan da suka wuce na baya munyi bayanin yanda zaka bude blog da kanka, sannan muka nuna yanda ake saka domain, da kuma yanda ake bude hosting duk a kyauta. Daman kuma bayanin namu yana tafiyane daya bayan daya kaman yanda muka tsara. Bayan an bude blog, sai kuma a cigaba da tsarashi ta yanda zai dauki hankalin mai kawo ziyara.
A bayanin mu na yanzu zamu nuna yanda ake saka theme ne a blog bayan an riga an bude blog. Sai kuma a gaba mununa yanda akeyin sauran aiyukan. Amma kafin nan zamuyi bayanin menene theme, da kuma amfaninsa a blog.
Menene Theme A WordPress?
Theme wani file ne da ake sawa WordPress wanda yake canzawa blog naka tsari da salo ta yanda zai dauki hankalin duk wanda ya shiga shafinka. Theme file ne daya kunshi abubuwa masu yawa acikinsa, wadannan abubuwan nacikinsa sune suke canza yanda ake ganin blog.
Wasu mutane ko kamfani ne suke tsara theme domin ayi amfani dashi a shafin WordPress. Wadanda suke tsara theme suna badashi kyauta, sai kuma su hada na siyarwa mai kyauta. Ta wannan hanyar suke samun kudi. Haka kuma duk bayan wani lokaci, zakaga ana cewa kayi update na theme naka. Duk lokacin da kaga sanarwar cewa kayi update nashi, kawai kayi update din. Saboda sun sabunta shi.
Kafin ka daura theme kana bukatan kayan aiki wadanda basu wuce biyu ba, kuma ga sunan a kasa mun bada link din da za'a saukar dasu.
Kayan Aikin Sune:
1. WordPress Theme
2. FireFox.
3. Chrome.
Wadannan browser guda biyun wato FireFox ko Chrome amfaninsu daya, dasu zamu shiga dashboard na WordPress din muyi aikin da zamuyi aciki. Theme kuma shi zamu saka domin canza kala da salon WordPress din. Sai kayi kasa ka cigaba da karanta yanda zakayi.
Ga Yanda Akeyi
1. Da farko, kaje WordPress naka kayi login.
2. Bayan kayi login, zasu kai ka cikin WordPress naka, sai ka taba alamun menu, wanda yake daga sama ta bangaren hagu.
3. Kana taba alamun menun nan take zakaga sun nuno maka wasu zabuka ta bangaren hannunka na hagu. Sai kayi kasa ka taba Appearance. Kana taba Appearance, zakaga wasu zabuka sun futo a kasa da shi. Sai ka duba cikin zabukan ka shiga Theme.
4. Kanayin haka zasu kawoka cikin Themes na WordPress naka, sai ka taba Add New.
5. Kana shiga Add New, sai kayi searching na Theme din da kakeso. Zamuyi misali da Theme mai suna Shamrock. Sai ka rubuta sunan Theme din da kakeso.
6. Kana gama rubuta sunan Theme din, zakaga atake Theme din zai futo. Sai kaje ka taba kansa.
7. Kana taba kan Theme din, zai budo maka shi. Ka duba daga bangaren hannunka na dama ta sama, zakaga wajen da aka rubuta Install sai ka taba wajen.
Kana taba Install, zakaga Theme din yafara installing... sai ka dan jira yagama.
8. Yana gama installing na Theme din, sai ka taba Activate, shima yana can sama ta bangaren hannunka na dama a wajen da da farko aka rubuta Install.
9. Kana taba Activate, nan take zasu nunama New theme activate kusa dashi an rubuta Visit site. Sai ka taba Visit site din domin ganin sabon Theme dakasa a blog naka.
10. Kana taba Visit site zakaga sun nuno maka cikin sabon blog naka na WordPress daka bude.
Wadannan matakan da muka nuna su akebi a saka theme a shafin blog na WordPress. Wannan itace mafi sauki, kuma kusan kowama da ita yake aiki domin saka theme a shafinsa. Theme din da muka yanzu mun sakashi a kyauta ba tare da mun biya ko sisi ba.
Akwai wasu theme din masu yawa acikin shafin WordPress masu kyau, kuma na kyauta. Haka kuma akwai wasu masu kyau sosai da wasu bangarori na daban wadanda na kudi ne. Wato na siyarwane idan kanaso sai kabiyasu sannan sukaba daman yin amfani da wannan theme din nasu.
Theme yana canza kala da salon blog wanda shine kekara jawo hankalin masu kawo ziyara a shafinka. Sannan yana daidaita blog naka komai yayi daidai yanda akeso. A gaba zamuzo da bayanin yanda ake goge theme.
Zamu dakata anan sai munzo da wasu bayanan agaba. Fatan za kucigaba da kasancewa da shafin nan! Mun gode!

Leave a Comment