Menene blog?
Bayan bayanai da su ka gabata game da menene domain, da kuma hosting da mahimmancin su - abu na gaba da mai bin wadannan darusan ya kamata ya sani shine blog, da blogging, da kuma blogger. Wadannan kalmomi guda ukun su na da alaka da juna - saboda haka sanin ma'anar guda daya zai baka karin haske domin fahimtar sauran.
Haka kuma su maziyartan su na iya rubuta nasu bayanin domin a karanta a baiyana ra'ayi akai. Bawai labarai ko bayanan rubutu kadai ake wallafawa a blog ba, akan bude blog domin domin nishadantarwa. Misalan blog su ne kaman shafin nan ko hausatop.com, da arewablog.com, da arewarulers.com, da arewasound.com, da nghausa.com da sauransu.
Shin ka na so, ka ko yi yanda ake bude blog?
Kaman ni mai wannan shafin da na ke rubuta bayanan nan da ake kawo ziyara a na karantawa, ni ma blogging na ke yi.
Shin ka na so, ka ko yi yanda ake harkar blogging?
Ko ka san matakan da ake bi domin samun kudi a YouTube?
Kaman yanda bayani ya gabata a kan hosting - idan ka na da hosting za ka iya bude blog kaman na WordPress, ko na Joomla da makamantansu. Indai ka mallaki hosting to a cikinsa za ka samu softwaren da za ta baka damar install din blog din da za ka yi blogging da shi. Wato softwaren da za ka yi install din WordPress, ko Joomla a kyauta, ka ga kenan kyauta ake bude blog.
Shin ko ka san menene WordPress?
Kudin da ka biya lokacin da ka ke bude hosting kadai ake bukata. Ma'ana idan za ka bude blog kaman WordPress ko Joomla ko wani website a cikin hosting naka ba sai ka biya ko sisi ba. Haka kuma akwai wani blog na kyauta wanda ya shahara a duniyar blogging, kuma mallakin kamfanin Google ne - wanda ina tunanin cewa shine na biyu bayan WordPress.
Blogger nau'ine na blog wanda kamfanin Google su ke samar da shi a kyauta ga masu harkar blogging. Shima blog ne da za ka yi rubuce-rubucenka tare da daura hotuna da bidiyo a cikin posting din ka. Wannan blog din gaba-daya komai da komai nashi kyauta ake yi - sai dai ko idan za ka sa custom domain a blog din. Bayan haka kuma akwai wadanda su ke hada template din blogger wadanda za ka siya template a wajensu, sai ka daurashi, ka yi aiki da shi a blog dinka.
Blog din da ake budewa na kamfanin Google, shine za ka ga sunan shi ya na karewa da blogspot.com. Misali, idan ka bude blog mai suna fasaha24, za ka ga ya koma fasaha24.blogspot.com. Idan kuma a shafin WordPress ka bude blog mai suna nuload, za ka ga ya koma nuload.wordpress.com wadannan blogspot.com da wordpress.com din su ake kira sub-domain. Idan ka bude blog a shafukansu sai ka siyo domain din da ranka ya ke so, ka sa a blog din.
Wato su na bada sub-domain da za ka yi aiki da shi, daga baya za ka iya siyan domain din ka ke so (custom domain) sai ka ci gaba da aiki da shi blog din ka. Domin idan ka siya domain mai saukin haddacewa zai sa maziyarta shafinka su ji dadin haddace sunan shafinka.
Idan ka bude blog a blogger, ko a WordPress za su baka template ko theme na kyauta wanda za ka fara aiki da shi a blog dinka, idan ka ga bai yi ma kyau ba sai ka canzashi ka sa wani. Idan kuma ka na bukatar masu kyau sai ka siyosu a internet.
Theme da template duk amfanin su daya, wato su ne su ke dauke da tsarin da blog naka zai kasance. Su ne su ke dauke da style na blog, kaman kala da salon rubutu. Su su ke sawa idan ka shiga wani website da waya, kuma ka sake shiga da computer za ka ga website din ya nuna maka style daban, wato style na waya daba hakama na computer daban.
Blog idan aka budeshi ana sakamasa domain kaman yanda ake sawa kowane website. Wannan shafin da kake karanta darasin nan shima blog ne.
Za mu yi bayanai daban-daban akan yanda ake bude blog nan gaba idan Allah ya so. Ku ci gaba da kasancewa da shafin nan tare da gaiyato mana abokai su ma su zo su karanta darusan da mu ke rubutawa a shafin nan. Daga nan mu ke cewa a huta lafiya, sai mun sake haduwa a wani darasin, mun gode! A huta lafiya!
Menene blog?
'Blog' website ne wanda ake ginawa domin watsa labarai, da ilimintar da al'umma, kuma ba kaman download portal da forum site ya ke ba. 'Blog' ya na nufin wajen da ake rubutu maziyarta su shiga su karanta rubutun da ake wallafawa a cikinsa. Sannan kuma maziyartan su na da daman baiyana ra'ayoyinsu ko kuma yin tambaya game da abun da su ka karanta a cikinsa.Haka kuma su maziyartan su na iya rubuta nasu bayanin domin a karanta a baiyana ra'ayi akai. Bawai labarai ko bayanan rubutu kadai ake wallafawa a blog ba, akan bude blog domin domin nishadantarwa. Misalan blog su ne kaman shafin nan ko hausatop.com, da arewablog.com, da arewarulers.com, da arewasound.com, da nghausa.com da sauransu.
Shin ka na so, ka ko yi yanda ake bude blog?
Menene blogging?
'Blogging' ya na nufin yin harkar blog a takaice. Wato harkar rubuce rubuce a shafukan internet domin amfanar da al'umma akan abubuwan da ba su sani ba, ko kuma karin haske akan wasu abubuwa da darusa da su ka sani. Wannan harka ta na kawo kudi ga masu rubuce-rubuce a shafukan internet.Kaman ni mai wannan shafin da na ke rubuta bayanan nan da ake kawo ziyara a na karantawa, ni ma blogging na ke yi.
Shin ka na so, ka ko yi yanda ake harkar blogging?
Menene blogger?
'Blogger' kuma shine wanda ya ke harkar rubuce-rubuce a shafukan internet. Wanda ya bude blog, kuma ya ke tafiyar da shi a na kiransa blogger. Hatta ni da na bude shafin nan na ke tafiyar da shi ni ma blogger, haka kuma ko da kai mai karanta bayanin nan idan ka bude blog, ka na tafiyar da shi kai ma blogger za a kira ka. Ya-na-da-kyau mu sani cewa shi blog kusan kyauta ake budeshi.Ko ka san matakan da ake bi domin samun kudi a YouTube?
Kaman yanda bayani ya gabata a kan hosting - idan ka na da hosting za ka iya bude blog kaman na WordPress, ko na Joomla da makamantansu. Indai ka mallaki hosting to a cikinsa za ka samu softwaren da za ta baka damar install din blog din da za ka yi blogging da shi. Wato softwaren da za ka yi install din WordPress, ko Joomla a kyauta, ka ga kenan kyauta ake bude blog.
Shin ko ka san menene WordPress?
Kudin da ka biya lokacin da ka ke bude hosting kadai ake bukata. Ma'ana idan za ka bude blog kaman WordPress ko Joomla ko wani website a cikin hosting naka ba sai ka biya ko sisi ba. Haka kuma akwai wani blog na kyauta wanda ya shahara a duniyar blogging, kuma mallakin kamfanin Google ne - wanda ina tunanin cewa shine na biyu bayan WordPress.
Blogger nau'ine na blog wanda kamfanin Google su ke samar da shi a kyauta ga masu harkar blogging. Shima blog ne da za ka yi rubuce-rubucenka tare da daura hotuna da bidiyo a cikin posting din ka. Wannan blog din gaba-daya komai da komai nashi kyauta ake yi - sai dai ko idan za ka sa custom domain a blog din. Bayan haka kuma akwai wadanda su ke hada template din blogger wadanda za ka siya template a wajensu, sai ka daurashi, ka yi aiki da shi a blog dinka.
Blog din da ake budewa na kamfanin Google, shine za ka ga sunan shi ya na karewa da blogspot.com. Misali, idan ka bude blog mai suna fasaha24, za ka ga ya koma fasaha24.blogspot.com. Idan kuma a shafin WordPress ka bude blog mai suna nuload, za ka ga ya koma nuload.wordpress.com wadannan blogspot.com da wordpress.com din su ake kira sub-domain. Idan ka bude blog a shafukansu sai ka siyo domain din da ranka ya ke so, ka sa a blog din.
Wato su na bada sub-domain da za ka yi aiki da shi, daga baya za ka iya siyan domain din ka ke so (custom domain) sai ka ci gaba da aiki da shi blog din ka. Domin idan ka siya domain mai saukin haddacewa zai sa maziyarta shafinka su ji dadin haddace sunan shafinka.
Idan ka bude blog a blogger, ko a WordPress za su baka template ko theme na kyauta wanda za ka fara aiki da shi a blog dinka, idan ka ga bai yi ma kyau ba sai ka canzashi ka sa wani. Idan kuma ka na bukatar masu kyau sai ka siyosu a internet.
Theme da template duk amfanin su daya, wato su ne su ke dauke da tsarin da blog naka zai kasance. Su ne su ke dauke da style na blog, kaman kala da salon rubutu. Su su ke sawa idan ka shiga wani website da waya, kuma ka sake shiga da computer za ka ga website din ya nuna maka style daban, wato style na waya daba hakama na computer daban.
Blog idan aka budeshi ana sakamasa domain kaman yanda ake sawa kowane website. Wannan shafin da kake karanta darasin nan shima blog ne.
Za mu yi bayanai daban-daban akan yanda ake bude blog nan gaba idan Allah ya so. Ku ci gaba da kasancewa da shafin nan tare da gaiyato mana abokai su ma su zo su karanta darusan da mu ke rubutawa a shafin nan. Daga nan mu ke cewa a huta lafiya, sai mun sake haduwa a wani darasin, mun gode! A huta lafiya!
Wan nan ya yi ma a na sosaiy
ReplyDeleteOK, mu na godiya
Delete