Yanda Ake Samun Kudi A Shafin YouTube
Kaman dai yanda muka sani shafin YouTube, shafine na internet wanda a cikinsa ake daura bidiyoyi mabambanta. Hasashe ya nuna cewa bayan shafin matambayi baya bata wato Google, shafin YouTube shine shafi na biyu wanda yake samun maziyarta mafi yawa a fadin duniyan nan. Idan aka duba dumbin jama'ar da suke amfani da shafin YouTube duba da yawan al'ummar da suke shiga YouTube yasa aka samo hanyar samun kudi ko riba a shafin.
Sanin kowane cewa hanyar da akafi samun kudi da ita a internet ita ce hanyar tallace tallacen hajoji (advertisement) bayan ita kuma akwai wasu hanyoyin masu yawa. A shafin YouTube ma da wannan hanya ake samun dumbin kudaden shiga. Idan kai ma'abocin kallace kallace a YouTube ne, zaka samu wasu bidiyoyin idan ka shigesu kafin su fara, zaka ga suna nuna maka talle kaman tallen waya, ko tallen mota, ko tallan talabijin da kayan sakawa da dai makamantansu.
Wadancan tallace tallacen da kake gani tananne wadanda suke daura bidiyoyi suke samun kudi. Kuma idan ka lura lokacin da kake kallon bidiyon zaka samu wani link a jikin bidiyon ko kuma wani hoto ko link tare da tambarin wani kamfani, ko wata ma'akata a karkashin bidiyon. Idan mai kallon bidiyo ya shiga wannan link din wanda ya daura wannan bidiyon zai samu wani abu.
Akwai kuma wasu channel wadanda suke amfani da irin tsarin da gidajen talabijin suke samun kudi. Wannan tsari shine yayin da kake kallon wani bidiyo zaka ga an sako tallar wani channel ko website ko kuma dai wani talle na daban. A gidajen talabijin ma zaka samu lokacin da ake labarai, misali kaman labaran karfe tara da na dare da akeyi a gidan talabijin na kasa wato NTA sai kuna cikin kallon rahotanni zaka ga an sako talle bayan an gama tallace tallacen sai a ci gaba da nuna labarai da rahotonni. Ko kuma sai ana cikin yin shiri mai dadi sai anzo tsakiyar shirin, sai kaga an yanke an sako talle - da wadannan hanyoyin gidajen talabijin suke samun kudin shiga bayan shirye shiryen da aka dauki nauyi gabatar da su.
To idan mutum ya bude channel a YouTube, kuma ya cika ka'idojin da suka shimfida a shafinsu - zai samu kudi.
Tayaya Shafin YouTube Yake Samun Kudi?
Idan muka duba yau akwai miliyoyin channel a shafin YouTube daga gurare mabambanta kuma duk wata channel YouTube su kan biya masu wadancan channel din. Shin ko ka taba yin tunani akan tayaya su kamfanin YouTube suke samun kudi, har suke iya biyan miliyoyin mutane duk wata? Kowane channel ana biyansu duk wata bisa kokarinsu. Wani channel din idan ka ga abun da suke samu a wata sai ka kama bakinka.
YouTube dai mallakin kamfanin Google ne, shi kuma Google shafine wanda yake karban tallace tallace a ko ina a fadin duniyannan domin ya tallasu ga masu amfani da internet a shafukansa. YouTube dayane daga cikin shafukan da Google suke tallata hajoji a cikinsa.
Tayaya Ake Samun Kudi A YouTube?
Hanyar samun kudi a YouTube ita ce talle kaman yanda muka yi bayani a sama. Idan kana so ka fara samun kudi a YouTube sai ka kasance kanada channel, sannan kuma kanada mabiya masu yawa akalla sama da dubu daya sai kuma bidiyoyin da suke daukar hankalin al'ummar. Yawan mabiya channel naka, da kuma yawan kallon bidiyoyin kake daurawa a channel naka zai kawo maka makudan kudi a YouTube.
Kafin ka fara samun kudi a YouTube kana bukatar wasu abubuwa kaman haka:
1. Vidoes
2. Channel
3. Viewers
4. Subscribers
5. Kayan Aiki
1. Videos sune bidiyoyin da zakana daurawa a domin wadanda suke sha'awarsu su zo su kalla. Su na kallon bidiyoyinda kake daurawa kaikuma kana tallata musu tallan da Google suka baka. Domin jawo ra'ayoyin masu kallo wasu sukan daura bidiyon ban dariya, da bidiyoyin wakoki, da kade kade, da bidiyoyin wasanni da sauransu.
2. Channel wurine da zaka daura bidiyoyinka domin masu kallo su zo su kalla. Channel shine sashe ko taska da zaka bude kana daura bidiyoyi domin masu kallo wadanda za su zo su kalla da wayoyi ko computer. Yayin da za su fara kallon bidiyon da ka daura a channel naka tallen da YouTube suka baka zai baiyana.
3. Viewers yana nufin masu kallon bidiyoyinka. Ko da ka cika duk ka'idojin da YouTube suka sa a shafinsu idan adadin da suke bukata baikaiba, bazasu biyaka. Akwai adadin lokacin da akeso kasamu kafin a biyaka.
4. Subscribers sune mutane da zasu shiga channel naka suyi subscribe, wanda zai basu dama su samu sakon email a duk lokacin da ka daura sabon bidiyo a channel naka. Akalla sai channel naka yana da mutane dubu daya ko sama da haka wadanda su kayi subscribe kafin kafin YouTube su biyaka.
5. Kafin ka fara daura bidiyo kana bukatar Kayan Aiki wadanda zasu taimaka ma ka tsara bidiyoyinka, da kuma daurasu a YouTube. Kayan aiki kaman na'urar daukar hoto, da bidiyo (camera) zaka iya amfani da ita domin tsara bidiyonka.
Computer da waya zaka iya amfani da su domin tsara bidiyoyinka kafin ka daurasu a channel naka dake YouTube. Bayan ka tanadi abubuwan da ake bukata, yana da kyau ka nutsu ka tsara bidiyoyinka ta yanda zai dauki hankali masu kallo, wanda hakan zaisa ko yaushe su kasance da channel naka.
Za mu tsaya anan da fatan ana amfanuwa da abubuwan da muke wallafawa a shafin nan. Idan da mai tambaya zai iya ajiyeta a wajen comment dake can kasa. Zai samu amsa idan Allah yasa mun sani. Mun gode, sai mun sake ganinku.

Leave a Comment