Yanda ake yin harkar blogging

Blogging harkace ta wallafe-wallafe ko rubuce-rubuce a shafukan internet. Wannan harka ta na bada gudunmuwa sosai wajen karantar da al'umma, da watsa labarai, da kuma tallace-tallacen hajoji a internet. Blogging a na yin sa ne da nufin rubuta abun da zai amfani al'umma a harkokin rayuwarsu ta yau da kullum. Mun yi bayanin yanda ake samun kudi a YouTube domin karanta wancan darasin sai a bincika darasin ya na cikin shafin nan.

Blogging harkace mai sauki, kuma ta na da saurin daukar hankalin mutane a shafukan internet. Domin bayanan da ake rubutawa sai an nutsu, an tsarasu, sannan ake wallafasu ta hanyar da kowai zai iya shiga ya karanta, kuma ya amfana. Duba da yawan adadin mutanen da su ke shiga shafukan internet, su karanta abubuwan da ake wallafawa a shafukan - ya sa aka yi amfani da hanyar tallata haja a shafukan internet domin samun kudi a internet.

Daga cikin darusan da su ka gaba a shafin nan mun yi bayanin wasu hanyoyin samun kudi a shafukan internet a lokacin da mu ka yi bayanin menene Google AdSense, da kuma Affiliate marketing wadanda su ne hanyoyi mafiya shahara.

Marubuta su kan bude blog domin su rubuta bayani akan wani abu na musamman - saboda kowane blog akwai dalili ko manufar budesa. Misali, akwai blog kaman wpbeginner.com wadanda su ke koyarwa akan yanda ake gina WordPress, da su androidauthority.com, da androidpolice.com, da beebom.com, da androidcentral.com wadanda su ke watsa labarai, da bayanai, da koyarwa akan fasahar zamani da wayoyin iPhone da Android.

Zaman yau akwai blog masu dumbin yawa a internet wadanda su ke koyar da mutane darusa daban-daban. Idan ka duba wasu blog din na watsa labarai ne, wasu blog din kuma koyarwa akeyi a cikinsu kaman yanda mu ka yi misali a sama. Sannan wasu blog din kaman naijaloaded.com, da hausatop.com, da arewablog.com, arewasound.com, da arewarulers.com, da gwariloaded.com da sauransu wadanda wakoki da kade-kade ake sakawa a cikinsu domin jawo hankalin mutane su zo su ga tallace-tallacen dake cikin shafukan.

Ana rubuta abun da zai dauki hankalin mutane a cikin blog domin shine zai sa a ko-da-yaushe jama'a su kasance da shafin. Duk lokacin da su ka shiga shafin za su ga wannan tallan da ka karbo a wajen Google AdSense, ko Amazon ka saka a blog naka. Idan su ka shiga kan tallar su ka sayi wani abu wanda ka tallata a shafinka, su kamfanonin da su ka baka tallace-tallacensu za su biyaka.

Abubuwan da za ka bukata domin fara blogging su ne:

1. Hannun jari
2. Blog da adreshin imel (email)
3. PC/Smartphone
4. Rubuta post
5. Samun lokaci
6. SEO
7. Account din social media
8. Hakuri da jajircewa

1. Hannun jari

Hannun jari shine kudin da kake bukata wanda za ka zuba domin siyan abubuwan da ake bukata tun daga mallakar layin waya, zuwa siyan wayar ita kanta, ko computer idan kuma ka na da su, ko kuma daya daga cikin su shikenan ya wadatar.

Bayan nan kuma ka na bukatar zuba kudi ko da kadan ne domin fara blogging. Kudin da mu ke magana a nan shine wanda za ka siya domain, tare da hosting da shi, wadanda za ka gina blog naka akansu. Wanda da shi ne za ka samu riba insha Allahu. Bayan hannun jari na kudi ka na bukatar hannun jari na fasaha ko dabara wajen rubuta abun da zai kasance ya na daukar hankalin masu kawo ziyara shafinka. Wadannan shafukan da na yi misali da su a can sama sun iya tsara rubutu mai kyau. Wanda shi ya sa su ka yi fintinkau ga sauran shafukan.


2. Blog da adreshin imel

Blog shine shafin da za ka gina wanda a cikinsa za ka na wallafa rubuce-rubucenka ko labarai domin masu karatu su shiga su karanta. Kafin ka samu damar mallakar blog ka na bukatan hosting wanda za ka gina blog naka akansa, bayan hosting kuma sai domain wanda shine sunan blog din naka. Wadanda abubuwa guda biyu su ne kanwa-uwar-gami wajen mallakar blog.

Adreshin imel (email) shine adreshin imel din da za ka yi amfani da shi domin rajistan account wai za ka samu domain da hosting tare da gina blog naka da shi. Bayan haka kuma da wannan adreshin email za ka iya karban sakonni daga mabiya da masu kawo ziyara shafinka. Wannan zai sa shafinka ya zamo ya na samun kulawa a wajen kuma hakan zai tabbatarwa masu shiga shafinka kana lura da abun da sukeso.


3. PC/Smartphone

Kalmar 'PC' ta na nufin Personal computer, wato computer ta daban wacce ka ware domin yin aikin blog naka. Smartphone kuma ita ce babbar waya wacce za ka yi aiki da ita domin tafiyar da blog naka idan ba ka da computer. Wadannan abubuwa guda biyu su na matukar mahimmanci domin idan ba ka da su, ba ka da daman aiki a blog naka. Computer ko babbar waya za ka iya amfani da su idan za ka gina blog naka, haka kuma za ka na amfani da su duk lokacin da za ka wallafa wani rubutu a blog naka.


4. Rubuta post

Rubuta post ko wallafa rubutu mai daukar hankali a blog naka shine zai jawowa shafinka yawan mabiya. Post shine rubutun da ka ke rubutawa sannan ka wallafa a blog naka wanda zai kasance ana shiga ana karantawa. Ana so rubutunka ya kasance ya na da matukar daukan hankalin ta yanda duk wanda ya karanta, zai yi sha'awar sake karantawa, saboda fasaha da kwarewa dake cikin rubutun naka. Ana so ka samu lokaci ka nutsu ka tsara taken rubutunka tare da tsara sauran bayanan da ya kunsa ta hanyar yin bayani filla-filla.


5. Samun lokaci

Samun isashshen lokaci wanda zai baka dama ka yi kyakkyawan tunani akan abun da zaka rubuta ga mabiya shafinka abune mai matukar mahimmaci. Domin nutsuwa da kuma yin tunani da rubutu mai kyau a shafinka zai karawa blog naka farin jini a wajen al'umma. Sannan kuma sai ka samu lokaci ka tsaya kayi bincike akan abunda zaka rubuta kafin ka rubutashi. Bayan ka gama rubuta abun da kakeso ka wallafa yana da kyau ka samu lokaci ka sake duba wannan rubutun naka, domin gyara duk wani kuskure da kayi a cikinsa. Bayan ka wallafa wannan rubutun yanada kyau ka sake dawowa ka duba comment saboda sanin abun da mutane suke cewa akan rubutunka.


6. SEO

SEO ya na nufin searching engine optimization, wato wata hanyace da shafinka ya ke samun karin maziyarta a kullum daga shafuka ko injin bincike kaman Google da Bing. Akwai wasu shafuka da su ka shahara a internet kaman guda biyun nan da mu ka yi misali da su wadanda su ke samun miliyoyin masu zuwa su yi bincike a cikinsu. Wadannan shafukan ana samun dubbai, ko daruruwan maziyarta daga wajensu, amma idan ka yi rajistar shafin naka a cikinsu.


7. Social media accounts

Social media kasancewa ka na da account a shafukan sada zumunta na internet ya na da matukar amfani domin za ka na sharing na post din da su ke cikin blog naka zuwa abokanka na shafukan sada zumunta.

Mallakar account din Facebook, da Twitter, da Instagram ya na taimakawa mai website wajen habaka maziyarta shafinsa. Domin idan ka rubuta wani bayani a shafinka ka na da damar da za ka turo wannan bayani zuwa Facebook, da Twitter saboda abokanka da mabiyanka na Facebook ko Twitter su shiga, su karanta bayanin da ka rubuta.


8. Hakuri da jajircewa

Hakuri dabi'ace mai matukar mahimmanci ga dan Adam. Hakuri haline da ya ke jagorantar mutum zuwa ga cimma nasara akan burinsa. Bahaushe ya ce Mai hakuri shi ya ke dafa dutse, har ya sha romonsa wannan magana akwai hikima a cikinta. Idan ba mu mantaba Ubangiji Madaukaki ya na cewa Allah ya na tare da masu hakuri wannan ya zo a cikin wata sura a Al-Kurani mai girma.

Hakuri dayane daga cikin hanyoyin cinma nasara. A lokacin da ka fara blogging za ka ga ka cire kudi, ka siya hosting da domain, ga kuma kudin da ka ke kashewa na siyan data a kullum, ga lokacin da ka ke batawa - amma kusan watanni biyu ko sama da haka ba ka samu ribar ko sisi ba.

To a nan mutane (bloggers) da yawa sun gudu sun bar ladansu, domin idan ka kai wannan lokacin hakuri kadan za ka kara, sannan ka fara amfanuwa da abunka watakila ka yi aiki kaso saba'in a cikin dari, amma ka kasa jurewa kaso talatin din da ya rage maka. Watakila ma idan da ka kara hakuri za ka samu amfanin abunka a nan kusa amma ba ka sani ba.

Ina ga ya kamata mu tsaya a nan domin bayanin ya kammala. Da fatan a na jin dadin kasancewa da shafin nan. Duk wanda ya ke da tambaya akwai wajen comment da ya ke can kasa sai a shiga a rubuta tambayar za a samu amsa idan Allah ya sa mun sani.

Mu na godiya akan ziyara da da ku ke kawowa shafin nan, sai mun sake ganinku, a huta lafiya!

No comments

Powered by Blogger.