Yanda ake bude Blog (WordPress)
Da farkon fari, kafin mu yi nisa a cikin darasin idan bakasan menene WordPress ba, ya na da kyau ka shiga wajen bincike da ya ke shafin nan, ka bincika domin sanin menene shi da kuma amfaninsa. Haka kuma idan baka san menene blog ba, ka shiga shi ma mun yi bayaninsa, domin sanin menene shi da amfaninsa sai ka bincika.
A darusan da mukayi na baya, mun bude hosting da domain sannan muka hada domain namu da hosting. Daga nan kuma zamu wuce mataki na gaba wanda shine zamuyi yanzu. Matakin da zamu duba yau shine zamu bude blog na WordPress wanda shine yafi kowane blog shahara a duniya.
WordPress blog ne dayake da dadin sha'ani, da saukin tafiyarwa, dauke tsari mai kyau. Baka bukatan ilimin programming domin tafiyar da WordPress. Haka kuma WordPress shine ya dace da kowane blogger wanda yake da kokari akan rubuce rubuce a shafinsa na internet.
1. Adreshin Email
2. Hosting
3. Domain
Wadannan abubuwan gaba daya mun nuna yanda zaka samesu kyauta, acikin darusan da mukayi a baya. Saboda haka ba tare da wani bata lokaci ba, sai muce a wayarka yana da kyau kayi tanadin wadannan abubuwa guda biyu da suke kasa - wadanda a baya ma dasu mukayi aiki.
Kayan aikin sune:
1. Adershin Email
2. FireFox
3. Chrome
Wadannan browser guda biyun wato Chrome, da FireFox duk amfanin su daya. Saboda haka idan kana da daya shikenan basai ka saukar da dayan ba. Idan kuma duk baka dasu sai ka saukar da guda daya. Shi kuma email dashi zamuyi amfani muyi rajistar blog namu, wanda zamuyi amfani dashi a duk lokacin da zamuyi login cikin dashboard na blog namu.
Ga yanda ake budewa
Bayan mun gama bude hosting, mun shigo control panel sai muka tsaya daga nan a wancan darasin. Yanzu kuma zamu cigaba daga inda muka tsaya. Bayan kabude domain da hosting na kyauta a darusan da mukayi a baya, sai muzo mu bude blog. Amma a wannan karon blog na WordPress zamu bude.
1. Da farko, ka shiga control panel na hosting din da kabude a baya. Kana shiga control panel din, sai kayi can kasa, kaje wajen SOFTACULOUS APPS INSTALLER. Acikin Softaculous ake installing na online software wanda zata baka daman bude blog ko CMS website. Kana zuwa wajen sai ka shiga Softaculous apps installer.
2. Kana shiga zakaga Top Scripts wato CMS website ko online software da ake installing na blog ko website dasu. Zakaga WordPress shine a farko, sai ka taba kanshi.
Kana taba kanshi zai nuna maka wasu zabubbuka guda uku a sama dashi. Zabukan sune Install, sai Demo, sai kuma Overview. Tunda install na WordPress zamuyi, kawai sai ka taba Install.
3. Kana taba installing zasu kawoka shafin da zakayi install na WordPress. Sai kayi kasa zakaga wajen da zaka cike bayanan da zakayi rajistar WordPress naka.
Kanayin kasa zakaga Choose the version you want to install. Kawai kabarshi a yanda yake. Amma idan kaga dama zaka iya zaban wani version din da kakeso, musamman tsohon version. Idan kabarshi a yanda yake shine zaisa kayi installing na version din WordPress da ake yayi a lokacin da zaka bude naka.
Kasa dashi kuma zakaga Choose protocol. Shima ka barshi a yanda yake wato a http:// kenan. Amma idan domain naka yana da SSL sai ka shiga wajen kazabi https:// sai kayi kasa.
Kasa dasu kuma sai wajen da zaka zabi domain. Zakaga anrubuta Choose Domain. Sai kashiga nan kazabi domain din da zakayi installing na WordPress din dashi.
Kana zaban domain din da zaka bude blog naka dashi sai kayi kasa.
Kana gama zaban domain din sai kayi kasa kazo wajen In Directory, sai kabar wannan wajen bakomai. Idan kuma kaga akwai rubutu a wajen, sai ka goge shi gaba daya. Idan kagoge rubutun, sai kabar wajen bakomai kadaka rubuta komai. Sai ka karayin kasa.
Daga nan kanayin kasa sai kazo wajen Site Settings. Shima sai ka shiga wajen Site Name, zakaga anrubuta My Blog. Sai ka goge shi gaba daya, kasa sunan blog naka. Shima wajen Site Description haka zakayi masa, zakaga an rubuta My WordPress Blog. Nan din ma sai ka goge shi gaba daya, sannan ka rubuta description na blog naka.
Sai ka danyi kasa zakaga Admin Account. Ka shiga wajen Admin Username, zakaga an rubuta admin. Sai kagoge shi, ka rubuta username naka, wanda zakana rubutashi idan zakayi login cikin dashboard na WordPress din naka.
Kasa dashi akwai wajen da aka rubuta Admin Password. Wajen da zaka password naka zaka samu an rubuta pass. Shima ka goge shi, sai ka saka password naka wanda zakayi amfani dashi duk lokacin da zakayi login cikin WordPress naka.
Daga nan kuma sai wajen Admin Email. Anan zakaga an rubuta admin@sunanwebsite.com zaka da admin da sunan website naka. Misali, a sama mun zabi nurablog.ga a matsayin domain namu wanda zamu bude blog din dashi. Shiyasa zakuga a hoton nan an rubuta admin@nurablog.ga - to duk email din da kagani an rubuta a wajen sai ka goge shi, ka rubuta email naka, wanda ana turo maka sako zaije cikin email din. Sannan idan zaka shiga dashboard naka username ko email zakasa sai password, kafin kayi login cikin dashboard na WordPress naka.
Daga nan sai wajen Choose Language wato wajen zaban yare. Shima kabarshi a yanda yake wato a turancin English. Sai wajen Select Plugin(s) shima ka kyale shi a yanda yake. Amma idan akwai plugin din da kakeso a wajen sai kayi tick akansa - ko kuma kawai kabarsu idan kagama komai sai kayi installing nasu a dashboard.
Daga nan sai Advanced Options, da Select Theme, suma kabarsu a yanda suke sai ka karayin kasa.
Kanayin kasa anan kada kataba komai, sai ka sakeyin kasa kashiga inda aka rubuta Install.
Kana shiga inda aka rubuta Install zakaga nan take WordPress naka zai fara installing, sai kajira kadan. Gaba daya bazai kai minti daya ba zai gama maka installing na WordPress naka.
4. WordPress din yana gama installing zakaga sun rubuta maka Congratulations, the software was installed successfully. Wato suna tayaka murna akan bude sabon WordPress da kayi.
5. Bayan sun gama maka congratulations, daga kasa kadan zakaga URL wanda zaka shiga kaga sabon Wordpress naka. Misali, http://nurablog.ga sai kuma zakaga Administrative URL, wato URL Address din da zaka shiga WordPress naka a matsayin Admin. Misali, http://nurablog.ga/wp-admin/ kana shiga zakaga dashboard na sabon WordPress din naka.
Alhamdulillah! Aiki yakammalu! Karin bayani duk lokacin da zaka shiga WordPress naka a matsayin admin, sai ka shiga wajen saka URL Address na browser ka - ka kara rubuta /wp-admin/ a gaban URL Address na WordPress naka.
Misali, URL Address na WordPress dina, shine http://nurablog.ga idan zan shiga dashboard, sai na kara /wp-admin/ a gaban URL Address din blog dina. URL Address din zai zama kaman haka http://nurablog.ga/wp-admin/ to tanan ake iya shiga dashboard. Idan ya bude maka wajen login sai ka saka email ko username naka, sai password, sai kayi login.
Idan kabi wadannan matakan da muka nuna a sama, zaka mallaki blog naka na kanka, kuma da kanka zakayi komai. Daga nan sai ka cigaba da rubuce rubucen ka, kaman yanda mukeyi a shafin nan.
Zaku iya tambaya akan abun da baku gane ba. Idan mun sani zaku samu amsa. Fatan an amfanuwa da abubuwan muke rubutawa a shafin nan.
A huta lafiya, sai mun hadu a wani darasin na gaba!

Shin ka na aiki da waya kirar Android, ko iPhone, ko iPad? Ko ka san yanda ake aiki da Photomath kuwa? To yi kokari ka karanta bayanin yanda ake aiki da Photomath.Idan zaka bude blog, kana bukatan wasu abubuwa kaman haka:

Mungode da ilmantarwa
ReplyDeleteMuma muna godiya da zuwa shafin man
Delete✋
Amma please nayi nayi in hada domain nawa da cpanel amma yaki, kuma nabi hanyar da ka koyar, ta yanda zaka bude domain da host a kyauta duka nayishi amma wajen hadawa abin sai ya gagara, please ya zanyi? Thanks
ReplyDelete