Menene HOSTING?
Mun yi bayanin menene domain, da misalansa da kuma amfanoninsa ga website a darusan da su ka gabata. Saboda haka yanzu kuma za mu ci gaba da bayani akan hosting da amfanoninsa ga ko wane website.
Kaman yanda bayani ya gabata a cikin bayanan da su ka gabata akan menene domain. Mun ce domain gaba daya ya na nufin sunan website - shi kuma hosting a kansa komai da komai na website ya ke zama. Misali kaman rubuce rubucen da a ke yi, da kuma sauran abubuwan da a ke ɗaurawa a shafin duk a kansa su ke zama.
Shin ka na bukatar mallakar blog (WordPress), ko kuma ka na bukatar koyan yanda ake gina shi?
Hosting shine ya ke dauke da duk wani file da ake ɗaurawa a kowane website da ka ke gani. A takaice kuma mu na iya cewa gaba daya duk wani file na website a kansa ya ke zama. Hosting da domain ababe ne guda biyu abokan aikin juna, wadanda idan aka hadasu su ke samar da website.
Hosting wajene da za ka ajiye kayan website naka komai da komai, yayin da shi kuma domain shine sunan website naka, kaman yanda mu ka yi bayani a baya.
Ko ka san affiliate marketing?
Akwai kamfanoni daban-daban wadanda su ke samar da hosting na kyauta da na kudi - kaman yanda kamfanoni daban-daban su ke samar da domain. Wadannan kamfanonin farashin su ya dan banbanta, wasu su kan yi sauki kadan ko-da-ya-ke wannan dabara ce ta kasuwa, domin habaka kasuwarsu da kuma jawo ra'ayoyin sabbin abokan mu'amala.
Domin a baya mutum idan zai gina website sai ya siya hosting daban, domain ma daban sai ya zo ya hadasu, sannan website din sa ya kasance ya na aiki ko-da-yaushe. Amma a yanzu an samu sauki - domin za ka samu kamfanonin da za su samar ma domain da hosting a farashi mai sauki.
Misali, idan ada ne sai ka siya domain ₦2000, kuma ka zo ka siya hosting ₦3000, ka ga website naka ya tashi ₦5000 kenan. Amma a yanzu kuma za su samar ma domain a kyauta sai ka biya ₦3000 kudin hosting kawai. Wasu kuma su samar ma dukkansu kowanne akan ₦1500, kenan idan ka hada kudin akalla za ka kashe ₦3000, ko ₦3500 a maimakon ₦5000 da ake kashewa a shekarun baya.
Ko ka san menene WordPress?
Wannan farashin na sama da na yi misali da su, ba wai dole bane ka samu hosting da domain da su ba. Saboda a wani kamfanin baifi haka ba, yayin da a wasu kamfanonin ya fi haka, kenan watakila sai ka cika wani abu ko da kaɗan ne kafin ka samu domain da hosting. Domain da hosting su na da sauki a kuɗaɗen kasashen waje musamman kasashen turawa da amurka, wadanda kudadensu su ke da daraja sosai a duniya.
Kamfanin godaddy.com su na samar da domain da hosting a farashi mai rahusa. Yayin da 000webhost.com da byethost.com da infinityfree.net da wix.com su ke samar da hosting da domain a kyauta. Amma su din ma idan ka na so akwai na kudin, sai ka biyasu su samar ma da na kudin.
Shin ka karanta bayanin yanda ake harkar blogging kuwa?
Yawanci idan ka siya hosting, ko kuma ka bude hosting na kyauta, za ka ga su na baka domain nasu ko muce sub-domain nasu, wato domain din da zai kasance akwai sunan kamfanin a jiki. Misali, idan ka bude blog mai suna nltips a 000webhost.com za ka ga sun karama sub-domain nasu a gaba kaman haka nltips.000webhostapp.com, ko kuma nuload za ka ga ya koma nuload.byethost24.com da dai sauran makamantansu.
Shin ka iya bude Google mail da kan ka?
Kamfanonin da su ke samar da domain da hosting na kyauta, yawanci za ka ga domain din da su ke samarwa na kyauta ya na da wahalar haddacewa ga masu kawo ziyara shafin. Shi ya sa idan mutum ya bude hosting na kyauta za ka ga ya je ya nemi domain na kudi, saboda hakan zaifi masa kwanciyar hankali - domin su kansu masu kawo ziyara a shafin nasa za su fi jin dadin haddace sunan shafin.
Idan ba hosting babu website, domain kuma duk inda ka bude website ko blog nasu, za su samar ma ka shi a kyauta. Amma sai dai ya na da wahalar haddacewa. Shi ya sa ake amfani da custom domain maimakon default domain wato nasu na zuwa.
A cikin hosting za ka iya bude shafukan blog wadanda za ka na rubuce rubucenka a cikinsu. Wadannan shafukan su ake kira Content Management System ko kuma CMS a takaice. Shafukan dai su ne WordPress, da Joomla, da phpBB da makamantasu. Wadannan shafukan duk online software ne, ban da su ka na iya bude website wanda za ka tsarashi da code naka yanda kake so, amma idan ka iya programming.
Bayan nan za ka samu daman gina website wanda za ka iya ɗaura abubuwan da mutane za su shiga su saukar da su a cikin wayoyin su da kwamfutotinsu. Wannan website din da za ka gina a cikin hosting din naka shine download portal wato wanda za ka sa files da yawa a cikin sa - masu kawo ziyara za su saukar da su.
Domain da hosting su ne kanwa-uwar-gami wajen gina website, idan babu su ba website. Saboda haka duk wanda ya ke son gina website dolene ya tanade su. Duk wani website da ka gani a internet ya na da su, kenan kai ma dole ne website naka ya kasance ya na da su.
Mu ma a nan arewa akwai kamfanonin da su ke samar hosting a farashi mai rahusa kaman kanoweb.net, sai kuma wadanda su ka shahara a duniya wato su godaddy.com, da bluehost.com da kuma hostinger.com da sauransu, sai ka shiga daya daga cikinsu, idan ka na so ka na bukatar hosting.
Zamu dakata anan mu huta, mu sha iska, sai kuma munzo da wani darasi. Muna fatan ana anfanuwa da abubuwan da ake karantawa a shafin nan. Haka kuma kuna iyayin tambaya akan duk abun daya shige muku duhu wanda mukayi bayani a shafin nan, zamu baku amsa idan mun sani. A huta lafiya mun gode!
Kaman yanda bayani ya gabata a cikin bayanan da su ka gabata akan menene domain. Mun ce domain gaba daya ya na nufin sunan website - shi kuma hosting a kansa komai da komai na website ya ke zama. Misali kaman rubuce rubucen da a ke yi, da kuma sauran abubuwan da a ke ɗaurawa a shafin duk a kansa su ke zama.
Menene hosting?
Idan aka ce hosting, a saukake wata na'urace da ta ke samar da shafukan internet wacce wani kamfani ya kirkirota, ko kuma ya siyota, ya ke aiki da ita domin samar da muhallin gina yanar-gizo akanta ta yanda maziyarta za su iya ziyartar wannan shafin da aka buɗe akanta domin karanta bayanan da ake wallafawa a cikinsa.Shin ka na bukatar mallakar blog (WordPress), ko kuma ka na bukatar koyan yanda ake gina shi?
Hosting shine ya ke dauke da duk wani file da ake ɗaurawa a kowane website da ka ke gani. A takaice kuma mu na iya cewa gaba daya duk wani file na website a kansa ya ke zama. Hosting da domain ababe ne guda biyu abokan aikin juna, wadanda idan aka hadasu su ke samar da website.
Hosting wajene da za ka ajiye kayan website naka komai da komai, yayin da shi kuma domain shine sunan website naka, kaman yanda mu ka yi bayani a baya.
Ire-iren hosting
Hosting shine ya kunshi komai da komai na website, wato duk wani file da za ka sa ko rubutawa a website to a nan ya ke zama. Hosting shine matattara kuma masarrafar website ko blog. Sannan kaman domain shima hosting akwai na kyauta da kuma na siyarwa, wanda siyar da shi ake yi. Sai bayan tsawon wani lokaci kaman watanni ko shekara za ka sake biyan kamfanin da ya samar ma hosting din domin website naka ya ci gaba da aiki. Idan ba haka ba website naka zai dena aiki, wato babu dama maziyara su ziyarceshi.Ko ka san affiliate marketing?
Akwai kamfanoni daban-daban wadanda su ke samar da hosting na kyauta da na kudi - kaman yanda kamfanoni daban-daban su ke samar da domain. Wadannan kamfanonin farashin su ya dan banbanta, wasu su kan yi sauki kadan ko-da-ya-ke wannan dabara ce ta kasuwa, domin habaka kasuwarsu da kuma jawo ra'ayoyin sabbin abokan mu'amala.
Domin a baya mutum idan zai gina website sai ya siya hosting daban, domain ma daban sai ya zo ya hadasu, sannan website din sa ya kasance ya na aiki ko-da-yaushe. Amma a yanzu an samu sauki - domin za ka samu kamfanonin da za su samar ma domain da hosting a farashi mai sauki.
Misali, idan ada ne sai ka siya domain ₦2000, kuma ka zo ka siya hosting ₦3000, ka ga website naka ya tashi ₦5000 kenan. Amma a yanzu kuma za su samar ma domain a kyauta sai ka biya ₦3000 kudin hosting kawai. Wasu kuma su samar ma dukkansu kowanne akan ₦1500, kenan idan ka hada kudin akalla za ka kashe ₦3000, ko ₦3500 a maimakon ₦5000 da ake kashewa a shekarun baya.
Ko ka san menene WordPress?
Wannan farashin na sama da na yi misali da su, ba wai dole bane ka samu hosting da domain da su ba. Saboda a wani kamfanin baifi haka ba, yayin da a wasu kamfanonin ya fi haka, kenan watakila sai ka cika wani abu ko da kaɗan ne kafin ka samu domain da hosting. Domain da hosting su na da sauki a kuɗaɗen kasashen waje musamman kasashen turawa da amurka, wadanda kudadensu su ke da daraja sosai a duniya.
Kamfanin godaddy.com su na samar da domain da hosting a farashi mai rahusa. Yayin da 000webhost.com da byethost.com da infinityfree.net da wix.com su ke samar da hosting da domain a kyauta. Amma su din ma idan ka na so akwai na kudin, sai ka biyasu su samar ma da na kudin.
Shin ka karanta bayanin yanda ake harkar blogging kuwa?
Yawanci idan ka siya hosting, ko kuma ka bude hosting na kyauta, za ka ga su na baka domain nasu ko muce sub-domain nasu, wato domain din da zai kasance akwai sunan kamfanin a jiki. Misali, idan ka bude blog mai suna nltips a 000webhost.com za ka ga sun karama sub-domain nasu a gaba kaman haka nltips.000webhostapp.com, ko kuma nuload za ka ga ya koma nuload.byethost24.com da dai sauran makamantansu.
Shin ka iya bude Google mail da kan ka?
Kamfanonin da su ke samar da domain da hosting na kyauta, yawanci za ka ga domain din da su ke samarwa na kyauta ya na da wahalar haddacewa ga masu kawo ziyara shafin. Shi ya sa idan mutum ya bude hosting na kyauta za ka ga ya je ya nemi domain na kudi, saboda hakan zaifi masa kwanciyar hankali - domin su kansu masu kawo ziyara a shafin nasa za su fi jin dadin haddace sunan shafin.
Idan ba hosting babu website, domain kuma duk inda ka bude website ko blog nasu, za su samar ma ka shi a kyauta. Amma sai dai ya na da wahalar haddacewa. Shi ya sa ake amfani da custom domain maimakon default domain wato nasu na zuwa.
A cikin hosting za ka iya bude shafukan blog wadanda za ka na rubuce rubucenka a cikinsu. Wadannan shafukan su ake kira Content Management System ko kuma CMS a takaice. Shafukan dai su ne WordPress, da Joomla, da phpBB da makamantasu. Wadannan shafukan duk online software ne, ban da su ka na iya bude website wanda za ka tsarashi da code naka yanda kake so, amma idan ka iya programming.
Bayan nan za ka samu daman gina website wanda za ka iya ɗaura abubuwan da mutane za su shiga su saukar da su a cikin wayoyin su da kwamfutotinsu. Wannan website din da za ka gina a cikin hosting din naka shine download portal wato wanda za ka sa files da yawa a cikin sa - masu kawo ziyara za su saukar da su.
Domain da hosting su ne kanwa-uwar-gami wajen gina website, idan babu su ba website. Saboda haka duk wanda ya ke son gina website dolene ya tanade su. Duk wani website da ka gani a internet ya na da su, kenan kai ma dole ne website naka ya kasance ya na da su.
Mu ma a nan arewa akwai kamfanonin da su ke samar hosting a farashi mai rahusa kaman kanoweb.net, sai kuma wadanda su ka shahara a duniya wato su godaddy.com, da bluehost.com da kuma hostinger.com da sauransu, sai ka shiga daya daga cikinsu, idan ka na so ka na bukatar hosting.
Zamu dakata anan mu huta, mu sha iska, sai kuma munzo da wani darasi. Muna fatan ana anfanuwa da abubuwan da ake karantawa a shafin nan. Haka kuma kuna iyayin tambaya akan duk abun daya shige muku duhu wanda mukayi bayani a shafin nan, zamu baku amsa idan mun sani. A huta lafiya mun gode!
Leave a Comment