Menene Affiliate Marketing?

Kasancewa a yanzu amfani da internet ya yi yawa, kuma ya zamo ko ina ana aiki da shi, hakan ya sa wasu harkokin su ka dawo kan internet kacokan. Wannan ya sa kwararru da masu amfani da internet su ka nemo hanyoyin da za a yi aiki da su a samu kudi a harkokin kan internet. Saboda duk wata harka ba ta yin dadi indai ba a samun riba da ita.

Internet wajene da ya hada al'ummomi daban guri daya. Mutane su kan yi mu'amalolinsu daga wurare mabanbanta a internet. Wani bai taba ganinka ba, kai ma ba ka taba ganinsa ba, amma kuna mu'amala ta internet. Harkokin internet harkokine da ake kashe kudi kafin ayi su, to saboda haka ya kamata a ce ana samun riba akan kudin da ake kashewa ta wannan fanni.

Shin ka karanta bayanin yanda ake neman kudi a shafin YouTube?

Neman kudi a internet ya na bisa doka da ka'ida. Domin a wasu kasashen ma gwamnatotinsu sun shiga wannan harka kuma sun taimaka da tsaro saboda su na samun kudin shiga ta hanyar karban haraji daga hannun 'yan kasa masu sana'a a internet.

Affiliate marketing hanyace ta neman kudi a internet. Wanda ana iya cewa ita ce hanya ta biyu ko ta uku bayan Google AdSense wanda ake amfani ita wajen samun kudi a internet. A inda ake amfani da internet sosai ana samun kudin shiga da ita, amma sai wanda yasan harkar.

Affliate marketing gaba daya ya dogara ne akan kamasho (commission). Yanda abun yake shine za ka je shafin wani kamfanin wanda ya ke sayar da kayaiyaki a internet kaman Amazon, da Flipkart, da Jiji.ng, da Jumia da makamantansu, sai ka yi rajista a matsayi mai yi musu talle. Bayan ka gama rajista da su, za su baka wani link wanda za ka rarrabashi a kafafen sadarwa na internet harma da blog ko website. Duk wanda ya shiga wannan link din zai kai shi cikin shafin Amazon.

Ko ka san yanda ake yin blogging?

Idan mutum ya shiga shafin Amazon ya siya wani abu ta hanyar link din ka, to kaima za su biyaka wani kaso a cikin abun da ya siya. Wato za su baka kamasho kenan. Ka ga haka zai sa ka dage ka na yi musu tallen kayansu a shafukan internet. Kuma mafi yawa kamfanonin nan su na biyane da kudin Amurka wato dala (dollar).

Ya ya abun ya ke?
Kaman yanda mu ka yi bayani za ka je shafin wani kamfani ka yi rajista a matsayin mai tallata musu haja haka abun ya ke. Bayan ka yi rajista sai ka shiga cikin shafin ka zabo abun da za ka yi tallensa, akwai abubuwa kala daban daban kaman wayoyi, da takalma, da riguna, da wanduna, da computer, da talabijin, da littattafai, da kyamarori, da rediyo da sauransu. Mu dau misali za ka tallata wani takalmi a shafinka.

Sai ka je, ka zabo takalmin da za ka tallata a shafinka, za su baka wani link sai ka kwafo link din. Bayan haka sai ka zo cikin shafinka, ko kuma inda za ka tallata wannan takalmin. Sannan ka rubuta sunansa, da amfanoninsa, da karkonsa, da dadewarsa yanda za ka sa duk wanda ya karanta bayanin zai yi sha'awar siyan takalmin. Bayan ka gama bayanin sai ka daura hoton takalmin da kuma link din da mutum zai shiga ya siya takalmin.

Mu dauka cewa takalmin farashinsa dala sittin ($60) ne, to duk wanda ya siya takalmin ta hanyar link din ka wanda ka rubuta za su baka dala uku zuwa biyar ($3-5). Sannan kuma idan ana yawan siyan abubuwa ta hanyar link din ka su kamfanin za su ragewa mutum farashin abun da zai siya idan ya biyo ta link din ka. Idan abun farashinsa dala talatin ($30) ne su na iya yi wa mutum ragi, su ce ya biya dala ashirin da shida zuwa da bakwai ($26-27).

Ka na bukatar koyan yanda ake bude blog kaman wannan da kanka?

Wadannan kamfanonin su na siyar da kayaiyakin amfanin yau da kullum kaman wadanda mu ka yi bayaninsu a sama kaman wayoyi, da kwamfutoti, da kayan sawa, da takalma, da agogo, da tabarau, da akwatunan talabijin da rediyo, da bidiyo, da receiver, da kwanukan zamani tare da tukwane da wadanda ba mu kawo sunansu ba - sannan su na siyar da wadannan kayaiyakin a farashi mai rahusa.

Irin wadannan kamfanonin akwai su a kowace kasa, kuma su na aiki, sai dai Amazon ana iya samun shi a kowace kasa. Domin sun zama kaman shafin Google, ko ina ana iya samunsu. Mu ma a nan Nigeria akwai Jiji.ng, da Jumia, wadanda sune su ka fi shahara kuma wadanda akafi sani.

A takaice affliliate marketing hanyace ta neman kudi a internet. Wacce a cikin ta mutum zai shiga shafin wani kamfani ya yi rajista a matsayin mai tallata musu hajarsu ga mabiyansa da abokansa a internet. Idan mabiyansa su ka siya abu ta hanyarsa to zai samu kamasho a cikin kudin abun da su ka siya.

Bari mu tsaya a nan sai kuma mun zo da ci gaban bayanin akan wasu hanyoyin na neman kudi a internet. Da fata ana amfanuwa da abubuwan da ake karantawa a wannan shafin. Mun gode da kawo ziyara wannan shafin a huta lafiya!

No comments

Powered by Blogger.