Menene WordPress?

Kafin mu fara wata harka - da farkon fari ya kamata mu san shin menene wannan abun, kuma menene fa'idarsa bayan mun yi wannan abun?

Dalilin haka ya sa za mu yi bayanin menene WordPress, sannan kuma a gaba mu yi bayanin wasu daga cikin dimbin fa'idodinsa da mu ka sani. Shafin WordPress ya na da saukin tafiyarwa a cikin manya da kananun wayoyi, kuma ya na budewa daidai girman screen din waya ko computer. Maziyarta za su kasance cikin farin a shafin saboda ba ya yi wa wayoyinsu nauyi, sabanin yanda wasu shafukan su ke nauyin budewa a wayoyin hannu.

A cikin darasin nan za mu yi bayanin menene WordPress, da kuma fa'idodinsa, sai kuma a wasu darusan na gaba masu zuwa mu yi bayanin wasu bangarorinsa da yanda ake aiki da su. Kafin mu fara bayanin menene WordPress, ya kamata mu fara sanin menene blog, wanda shi zai taimaka mana wajen fahimtar menene WordPress, tare da wasu amfanoninsa a harkar internet.

Menene blog?

Za mu yi bayanin menene blog a takaice, saboda a baya mun yi cikakken bayaninsa. A turance blog ya na nufin wani dan karamin shafi a internet da ake budewa, domin a rubuta labarai, ko wasu darusa ta yanda wani ko wasu za su shiga su karanta abun da ake rubutawa a cikinsa.

Blog shima website ne wanda ake budewa, kaman sauran website. Amma sai dai shi an takaita aiyukansa. Mun ce an takaita aiyukansa ne, saboda shi ba kaman sauran website din da ake shiga a saukar da wasu abubuwa kaman bidiyo, da waka, ko hotuna ya ke ba. Shi a na bude shine saboda yin rubuce-rubuce a internet, ko da ya ke shidin ma za a iya daura file a cikinsa ta yanda wani zai iya saukar da shi a wayarsa ko computersa.

Shin ko ka san yanda ake bude blog din WordPress?

Mafi yawa shi blog ana budeshi ne da manufar yin rubuce-rubuce don maziyarta su karanta. Kuma kowa zai iya bude blog idan ya tanadi kayan aiki - a na bude shi dan a rubuta labarai, ko tutorials, da darusan ilimi, da kasidu, da makaloli (articles) ko kuma tallata hajojinsu a cikinsa kaman yanda ake yi a sauran harkokin internet.

Menene WordPress?

WordPress wata software ce wanda ake amfani da ita a bude blog a online. Kuma wannan software an ginata akan yaren PHP, wato ilimin sanin yanda ake gina manhajoji, da website. Hakama WordPress CMS website ne, wato website din da za ka iya tsarashi yanda ranka ya ke so. WordPress ya na aiki da taimakon wasu abubuwa ko mu kirasu a matsayin bangarorinsa, kaman haka plugins, da widget, da theme da sauransu.

WordPress ya na da sauki, da kuma dadin aiki - idan ka iya aiki da shi. Sannan ya na da wasu bangarori da su ke bada gudunmuwa wajen tafiyar da shi, tare da taimaka masa ya yi aiki cikin sauki. Rubuta post daman ita ce babbar manufa da dalilin bude blog. Shima WordPress ya na da wannan fannin dauke da abubuwan kayatarwa, da kuma ban sha'awa fiye da sauran.

Shin ka karanta bayanin yanda ake install din plugin a WordPress?

WordPress ya na baka damar ganin bidiyo a cikin blog post din sa. Haka kuma za ka iya sauraron wakoki da sauran mp3 a cikin post din sa. Fannin hotuna shima akwaishi, za ka iya sauraro ko kallon wadannan Media file din a online. Ka na iya hada WordPress da sauran shafukan ka na sada zumunta, kaman Facebook da Twitter ta yanda ka na yin post a cikinsa, nan take za ka ganshi ya tafi cikin shafukan idan ka hadasu da shi.

Yaushe aka kirkiro WordPress?

Bari mu duba tarihin WordPress kadan. WordPress ya zamo gama duniya tun bayan da aka kirkiroshi a shekaru sama da goma sha shida da su ka gabata. Kaman yanda mu ka karanta, ko mu ka ji labari mafi yawa mun ji cewa a shekara ta dubu biyu da uku (2003) aka fara kirkiroshi, sai dai daman kafin nan a na ta kokarin tsarashi.

Bayan nan ne ya fara habaka da sannu-sannu har ya kai matakin da ya zama kusan ya zagaye duniyar internet. Kimiya da fasaha sun ginune tare da taimakon juna. Da farko za ka ga wani ya zo ya sa harsashi, ma'ana ya fara kirkiro wani abu, daga baya wani yazo ya kawo wasu canje-canje a cikin wannan abun. Wadannan canje-canjen za ka ga su ne su ke zamanantar da wannan abun da a ka kirkiro a baya. Misali, a shekarun baya idan ka ga yanda computer ta ke, kuma ka ga yanda ta ke a yau za ka ga cewa an samu ci gaba sosai.

Shin ko ka san yanda ake seta theme a WordPress?

Shima WordPress ya ginune da taimakon wasu abokan aiki. Akwai kamfanoni da mutane da su ka shahara a fannin yaren PHP, da sauran ilimomin programming wadanda su ka taimaka wajen ginuwar WordPress.

Kadan daga cikin fa'idodi, da amfanonin WordPress, shine ana samun kudi dashi, ana koyarwa dashi, ana tallace tallace dashi, ana koyo acikinshi, ana cinikaiya dashi, har shima kanshi ana siyar dashi. Duk wadannan abubuwan da mukace anayi dashi, darusa zasuzo akansu nan gaba idan Allah yasa muna raye, kuma da halinyi.

WordPress dai website ne mai matukar amfani, musamman aharkar internet. Hausawa sukace "dan riba ake kunun koko, bawai dan asha acika ciki ba". Shima WordPress dan riba ake ginashi, ribar itace ana samun sauki wajen mallakarshi da ginashi, da kuma gudanar dashi a wani bangaren ma kyauta ake bude shi. Mafi yawa masu kasuwanci a internet wato Online marketing, sunfi bada mahimmanci wajen amfani da WordPress, saboda ingancinsa, da tsaron da yake dashi.

Wasu hanyoyin da ake samun kudi da WordPress su ne AdSense da Affliate Marketing. Wadannan hanyoyi biyun ana samun makudan kudi da WordPress. Ko-da-ya-ke kusa su ne hanyoyin samun kudi a blog mafi shahara.

WordPress dai kaman yanda mukayi bayani a farkon darasin nan, munce gurine da'ake yin rubutu da wasu zasu shiga su karanta. Kamfanoni dadama a yanzu suna amfani da WordPress wajen tafiyar da harkonkinsu na online.

Duba da cigaban da'aka samu a fannin fasaha yasa a yanzu wasu harkokin sun koma gaba daya ta online. Ko da yake mafi yawa a kasashen da suka cigaba ne, wannan yasa WordPress yayiwa sauran abokansa fintinkau a internet.

Malamai, da sauran masana, da marubuta tuni suka rungumi WordPress ta hanyar bude shafukan blog nasa, suna rubuce rubuce tare da tallata fasaharsu da hajojinsu a interne.

Fatan daga karshe itace ana anfanuwa da darusan da muke rubutawa a shafin nan na taimakon kai da kai. Muna bukatan kugaiyato mana sauran abokanku suma suzo, su amfana da rubuce rubucen da suke shafin nan.

Mun gode a huta lafiya!

No comments

Powered by Blogger.