Yanda ake install din plugin a WordPress

Ga yanda ake yi


1. Da farko ka shiga dashboard na WordPress din ka sai ka taba Menu, wanda ya ke can sama ta bangaren hagu.


2. Ka na taba wajen za ka ga ya budo ma ka zabukan cikin dashboard din sai ka yi kasa ka taba Plugins.


3. Ka na taba wajen za ka ga su Installed Plugins, da Add New, da kuma Plugin Editor, sai ka shiga Add New.


4. Ka na shiga Add New, sai ka yi kasa ka shiga Search plugins...


Sannan ka rubuta sunan plugin da ka ke so ka yi install din sa, za mu yi misali da Contact form 7.


5. Ka na gama rubuta sunan sai ka yi kasa za ka ga plugin din ya baiyana, sai ka taba Install Now, wanda ya ke gefen sunan plugin din.


6. Ka na taba wajen za ka ga rubutun ya koma Installing...


7. Lokacin da plugin din ya rubuta installing sai ka jira ya gama installing. Ya na gama installing din zai rubuta ma ka Activate, sai ka taba Activate din.


No comments

Powered by Blogger.