Mene ne DOMAIN?
Assalamu alaikum. Masu bibiyarmu a wannan shafi, barkunmu da wannan lokaci. Muna fatan kuna cikin koshin lafiya. A darasin nan zamuyi muku bayani game da wani bangare mai matukar muhimmanci wajen gina shafi kamar irin wannan dake kuke karanta darusa masu amfani a cikinsa. Mutane dadama su kanyi tambaya akan yadda ake ginawa ko mallakar shafi irin wannan. Domin suma sunada nasu darusan da suke son wallafawa a wani fanni wanda zai kasance mai amfanar al'umma. Idan kana daga cikin wadanda suke bukatar mallakar shafi wanda zakake koyar da mutane darusa kaman yadda mukeyi, sai kabi wannan darasi da sauran darusa da zasuzo a wannan fanni.
Mene ne Domain?
A lokacin da zaka shigo shafin nan, sai da ka rubuta www.arewapot.com.ng a wayarka, kamar yadda kakeyi idan zaka karanta labarai a shafukan watsa labarai na intanet kamar BBC Hausa, wato kakan rubuta www.bbchausa.com a browser wayarka ko computerka. Wadannan harufa da kayi amfani dasu wajen shiga shafukan sune adreshin da kabi wajen shiga shafin nan ko wadanda kayi amfani dasu ka shiga shafin BBC Hausa, su ake kira domain. Domain suna ne kokuma muce adreshi ne da ake amfani dashi wajen shiga kowane shafi a intantet. Misali, idan kanaso ka shigo shafin nan ka karanta darusan da muke wallafawa, zaka rubuta www.arewapot.com.nga wayarka, sannan kake iya samun damar shigowa shafin nan sannan ka amfana da darusan da muke wallafa.Idan kana bukatar mallakar shafi kamar wannan, wato wanda acikinsa zakake rubuta darusan dakakeso wasu su shigo su karanta, ko kuma kanaso ka bude gidan jarida a intanet wanda zakake wallafa labarai acikinsa kamar BBC Hausa, kana bukatar domain da hosting da sauran kayan aiki. A takaice dai wannan adreshi da ake ziyartar shafi tahanyarsa shine domain. Kowane shafi dakake gani a intanet yana da nasa domain. Saboda haka idan kanaso ka gina shafi kamar wannan yana da kyau, ka tsaya ka yi tunanin saka sunan da bazaiyi wahalar haddacewa ga maziyarta ba.
Saka suna mai sauki wanda zaiyi saukin haddacewa na sanya maziyarta shafin yawan kawo ziyara shafin domin yanada saukin da zasu iya hadacewa. Sanya suna mai tsawo wanda yake da wahalar haddacewa na sanya mutane karancin kawo ziyara shafinka domin ko da mutum yana son ziyartar shafin bazai iya shiga shafinka ba saboda sunan yayi tsawon da zaiyi wahalar haddacewa.
Tayaya zan mallaki domain?
Domain shine suna ko adreshin shafin intanet wanda muke gani acikin browsers dinmu a lokacin da muke shiga shafukan intanet. Akwai kamfanoni daban-daban a intanet da suke samar da domain ga masu bukata. Idan muka lura zamuga sunayen wasu shafukan intanet yana karewa da .com ko .net ko .org da dai makamantansu - muna iya cewa kowane kamfani da sunan shi hakama domain nashi daban da wani kamfanin.Domain siyar dashi ake wato ba kyauta ake samunsa ba. Amma, akwai na kyautan ma, saboda haka duk inda kaga sunan shafi yakare da .com ko .net ko .org da .ng ko .com.ng ko .edu to wannan shafin siyan domain din yayi. Siyan domain lokaci ne - kana iya siyan na wata wata, kenan duk wata zaka biya kamfanin da ya samar maka da domain din. Akwai na shekara wannan shi akafi yawan siya duk bayan shekara sai mutum ya biya kudin domain din saboda expire yakeyi, idan lokacin yayi. Idan lokacin biya yayi mutum bai biya ba, domain din zaiyi expire ya dena aiki.
Domain na kyauta shine ake rajistarsa a shafin www.freenom.com. Zakayi rajistar domain naka a kyauta, ba tare da kabiya ko sisi ba. Sai dai idan domain naka yayi expire, wato lokacin daka zaba ya cika, dole sai ka biya indai kanaso ka cigaba da aiki da shi. Domain na kyauta sune zakaga sunan shafi yana karewa da .tk ko .ga ko .ml ko .gq da .cf da makamantansu.
Bayan mutum ya samu domain na kyauta ko kuma na kudi sai yazo ya saka shi a shafin sa. Domin idan kabude shafi domain na shafin zai kasance default wato wanda kamfanin hosting din suka baka. Sai kasa domain mai dauke da sunan da kakeso.
Wannan shine bayanin domain a takaice. Domain yana da amfani ga website domin shine sunan shafin daman idan mutum zai bude shafi a internet yana bukatan hosting da domain. Hosting anan ne kayan website din suke zama domain kuma shi ne hanyar da mutane zasu kai ziyara wannan shafin.
Anan zamu dakata sai kuma munzo da bayanin akan menene hosting, da amfanin sa ga website. Karin bayani domain da hosting suna amfani ga website domin sune shafin gaba daya. Fatan an amfanuwa da darusan da muke rubutawa a shafin nan mun gode!
Leave a Comment