Yanda ake aiki da ka'idar BODMAS 02

A darasin da ya wuce mun yi bayanin BODMAS da ma'anarsa da matakansa tun daga matakin farko zuwa na karshe. Saboda haka a cikin darasin nan za mu cigaba da misalaine.

Misali, idan akace ka samo amsar wannan tambayar ya za ka yi?

2 + 3 × 4 = ?

Mutane dayawa rikicewa sukeyi domin wasu zasu ce 2 + 3 × 4 = 20 ne, amma ba hakabane. Amsar itace 2 + 3 × 4 = 14 ne.


Na san wani idan zai warware wannan tambaya cewa zai yi biyu a hada da uku sau hudu, wato biyu a hada da uku ya zama biyar, biyar sau hudu kuma ashirin ne.


To wannan amsar kuskurece ba haka take ba. Bari mu yi amfani da Photomath domin tabbatar da cewa wannan amsa kuskurece ko kuma daidai ce. Amma shi din ma ya nuna cewa not true, ma'ana wannan kuskurene.


Idan akabi ka'idar da mu kayi bayani a darasin da ya gabata. Idan za mu iya tunawa mun ce idan aka ba ka tambaya kaman haka 2 + 3 × 4 = ?. Za ka fara dubawa akwai bracket a tambayar, idan kuma babu sai ka duba akwai of, shima idan babu sai mu duba akwai division, idan babu shi sai ka duba akwai multiplication idan akwai sai ka fara lissafa shi - ko da shine a karshe.

Saboda haka tun da akwai multiplication za mu fara lissafashi kenan za mu ce uku sau hudu ya zama sha biyu. Sannan bayan multiplication sai mu duba akwai addition tun da akwaishi sai cigaba da lissafinmu da shi. Sai mu ce sha-biyu a hada da biyu ya zama sha-hudu.2 + 3 × 4 = 14.


Domin tabbatar da wannan amsa shin daidaice ko kuma akwai kuskure, za mu sake amfani da photomath idan aka duba ya true, wato amsar daidaice.


Saboda haka ya-na-da-kyau a lura duk lokacin da aka samu tambayar lissafi sai anbi wadannan matakan da mu ka yi bayaninsu a darasin da ya wuce na daya.

Sannan kuma ga tambaya a amsa mana idan har ana fahimtar darusanmu na koyan lissafi. Tambayar itace 2 - 3 + 4 × 5 ÷ 1 = ?.


Wannan tambayar dolene sai anbi matakan da muka nuna a darusan bayan kafin mu yi bayanin BODMAS sannan ake amsata.

5 comments:

  1. Kay Malam nura nan akoy aiki,

    Mungode

    ReplyDelete
    Replies
    1. 😂😂 Malam Usman akwai sauran bayani ya na nan zuwa

      Delete
  2. Amsarnan 0 ce
    Saboda Zai kasance
    213+5÷1=0
    Saboda Qaidar Bodmas Zai kasance Kamar haka.
    5÷1=5
    4×5=20
    3+4=7
    2-3=0
    Allah Yasa Na Heqe Amsar

    ReplyDelete
  3. 2-3+4*5/1
    -1+4*5/1
    4*5=20+(-1)/1=19 or -1+20/1=19
    gashi nan a duba min nayi daidai? Muna godiya ALLAH bada lada kuma Dan ALLAH aci gaba muna karuwa.sosai

    ReplyDelete

Powered by Blogger.