Mu koyi joni darasi na daya
Daga cikin darusan da su ka gabata mun yi bayanin yanda ake gyara waya idan ta fada ruwa, da mun bayanin yanda ake ragewa waya wahala, da kuma bayanin menene GPS satellite, da sauran darusan fasaha.
Lokacin yarinta yara su kan yi karambanin jone-jone wanda hakan ya kan jagorancesu koyan gyare-gyaren kayan lantarki kaman rediyo, da tocila. Fasahar jone-jone ta gargajiya ita ce matakin farko ta gina fasahar zamani.
Kusan mu na iya cewa joni ba sai an koyawa mutum ba, shi da kansa idan ya samo kayan aiki zai iya yin komai da kansa, amma ga wadanda ba su iya ba idan su ka bi darasin nan za su ga yanda ake yi.
Shin ko ka san menene lithium battery, da kuma amfaninsa?
Amma kafin mu shiga bayanin yanda ake yi sai a tanadi kayan aiki, kuma ga sunayensu a kasa mun lissafo.
2. Battery
3. Switch
4. Wire
Shin ko ka san menene satellite, da kuma yanda ya ke aiki?
Kafin mu fara koyan joni, mu na bukatar abubuwa guda biyar din nan wadanda mu ka kawo sunansu a sama. Light bulb shine koyin wutar lantarki wanda za mu jona ma sa battery ya ba mu haske. Battery kuma shine ya ke dauke da sinadaran da su ke samar da wutar lantarki. Shi kuma switch shine makunna da za mu jonashi tsakanin battery da koyin wutar. Ita kuma wire ita ce za mu jonata daga jikin battery zuwa makunna ko zuwa jikin koyin wuta, kuma amfaninta shine daukar wutar lantarki daga wani waje zuwa wani wajen.
2. Bayan ka fere bakin wayoyin sai ka jona daya wayar a bakin batirin, sai kuma ka sake jona daya wayar a karkashin batirin.
3. Sannan sai ka zo ka jona wayoyin a jikin koyin wutar. Ka na jona wayoyin a jikin koyin za ka ga koyin wutan ya kawo wuta.
Shin ko ka san power bank, da kuma amfanoninsa ga wayar hannu?
4. Bayan ka yi haka koyin ya kawo, wato an gama aiki. To mataki na biyu kuma shine wanda za mu jona switch, wato makunna. Jonin ya na cikin sai ka dakko rezarka, ka raba waya daya.
5. Ka na raba wayar sai ka dakko switch din ka jona ma sa wayar da ta fito daga jikin batirin, hakama sai ka jona wayar da ta fito daga jikin koyin da switch din.
6. Daga nan sai ka kunna switch din za ka ga koyin wutan ya kawo wuta.
7. Kaman yanda bayani ya gabata a sama, mun ce waya ita ta ke daukan wuta ko karfin lantarki daga batirin zuwa koyin wutar.
Idan a ka bi wadannan matakan za a koyi joni cikin sauki.
Wadannan matakan su za ka bi wajen koyan joni, da fatan ana amfuna da darusan da mu ke wallafawa a shafin nan na kimiyyar zamani da fasaha. Za mu dakata a nan sai kuma wani lokaci idan mun zo da wani darasin. Kafin nan kuma duk mai tambaya sai ya je can kasa wajen comment ya rubuta, zai samu amsa idan Allah ya sa mun sani.
Mu na godiya akan ziyarar da ku ke kawo wa shafin nan, a huta lafiya, sai mun sake ganinku.
Lokacin yarinta yara su kan yi karambanin jone-jone wanda hakan ya kan jagorancesu koyan gyare-gyaren kayan lantarki kaman rediyo, da tocila. Fasahar jone-jone ta gargajiya ita ce matakin farko ta gina fasahar zamani.
Kusan mu na iya cewa joni ba sai an koyawa mutum ba, shi da kansa idan ya samo kayan aiki zai iya yin komai da kansa, amma ga wadanda ba su iya ba idan su ka bi darasin nan za su ga yanda ake yi.
Shin ko ka san menene lithium battery, da kuma amfaninsa?
Amma kafin mu shiga bayanin yanda ake yi sai a tanadi kayan aiki, kuma ga sunayensu a kasa mun lissafo.
Kayan aiki su ne:
1. Light bulb.2. Battery
3. Switch
4. Wire
Shin ko ka san menene satellite, da kuma yanda ya ke aiki?
Kafin mu fara koyan joni, mu na bukatar abubuwa guda biyar din nan wadanda mu ka kawo sunansu a sama. Light bulb shine koyin wutar lantarki wanda za mu jona ma sa battery ya ba mu haske. Battery kuma shine ya ke dauke da sinadaran da su ke samar da wutar lantarki. Shi kuma switch shine makunna da za mu jonashi tsakanin battery da koyin wutar. Ita kuma wire ita ce za mu jonata daga jikin battery zuwa makunna ko zuwa jikin koyin wuta, kuma amfaninta shine daukar wutar lantarki daga wani waje zuwa wani wajen.
Ga yanda ake yi
1. Da farko, ka tanadi kayan aikin da mu ka lissafo a sama, sai ka ajiyesu. Daga sai ka samo abu mai dan kaifi kaman reza (razor blade), sai ka raba wayar gida biyu sannan ka fere bakin wayoyin.2. Bayan ka fere bakin wayoyin sai ka jona daya wayar a bakin batirin, sai kuma ka sake jona daya wayar a karkashin batirin.
3. Sannan sai ka zo ka jona wayoyin a jikin koyin wutar. Ka na jona wayoyin a jikin koyin za ka ga koyin wutan ya kawo wuta.
Shin ko ka san power bank, da kuma amfanoninsa ga wayar hannu?
4. Bayan ka yi haka koyin ya kawo, wato an gama aiki. To mataki na biyu kuma shine wanda za mu jona switch, wato makunna. Jonin ya na cikin sai ka dakko rezarka, ka raba waya daya.
5. Ka na raba wayar sai ka dakko switch din ka jona ma sa wayar da ta fito daga jikin batirin, hakama sai ka jona wayar da ta fito daga jikin koyin da switch din.
6. Daga nan sai ka kunna switch din za ka ga koyin wutan ya kawo wuta.
7. Kaman yanda bayani ya gabata a sama, mun ce waya ita ta ke daukan wuta ko karfin lantarki daga batirin zuwa koyin wutar.
Idan a ka bi wadannan matakan za a koyi joni cikin sauki.
Wadannan matakan su za ka bi wajen koyan joni, da fatan ana amfuna da darusan da mu ke wallafawa a shafin nan na kimiyyar zamani da fasaha. Za mu dakata a nan sai kuma wani lokaci idan mun zo da wani darasin. Kafin nan kuma duk mai tambaya sai ya je can kasa wajen comment ya rubuta, zai samu amsa idan Allah ya sa mun sani.
Mu na godiya akan ziyarar da ku ke kawo wa shafin nan, a huta lafiya, sai mun sake ganinku.
Leave a Comment