Yanda koyin wuta na lantarki ya ke aiki

Koyayen wuta na lantarki ababene wadanda mu ke amfani da su a cikin fitilar hannu, da fitilun mota, ko mashin, da kuma cikin gidaje, da shaguna domin samun haske a waje mai duhu, ko kuma idan dare ya yi. Akwai koyayen wuta kala daban daban kamansu LED (light emitting diode), da kyandir (incandescent) wadanda suke da matukar haske - wasunsu ana amfani da su domin haska filayen wasanni ko tituna da sauransu. To a yau da yaddar Allah Madaukaki za mu yi bayani akan light bulb wato koyin wuta na gargajiya wanda aka fi saninsa da filament lamp - tare da karin bayani game da bambancin voltage da current.

Yanda kwan ya ke aiki shine cikinsa akwai abun da ake kira 'filament' wanda shi ya ke kamawa da wuta sannan a samu hasken da ya ke haska mana hanyoyi. Filament za ka ganshi a nannade kaman spring a cikin tsakiyar koyin, kuma an kerashi da element din tungsten. Kafin mu yi nisa a cikin bayanin yana da kyau a sani cewa filament lamp kala biyune. Akwai babba wanda ake kunnashi da wuta mai karfi kaman wutar NEPA, ko generator, ko batirin mota. Sai kuma dan karami wanda ake kunnashi da wuta mara karfi kaman wutar batirin tocila, ko batirin waya. Gaba daya su biyun da fasaha daya suke aiki domin samar da haske.

Shin ko ka san menene internet?

Jikin filament akwai kafafuwa guda hudu wadanda su ke rike da shi. Daga cikinsu akwai karafuna guda biyu marasa tsayi a tsakiya wadanda su ke rike da shi yayin da su din ma wani glass ne ya ke dauke da su. Sai kuma sauran biyun masu tsayi daya kafar ta nanne wutar ta ke shiga cikin koyin, yayin da daya kafar kuma ta nanne wutar ta ke futa daga cikin koyin. Sannan cikin koyin akwai sinadarin iska (gas) kamansu krypton ko argon ko xenon ko kuma inert gas (wasu su na kiransu noble gas, wasu rear gas su ke kiransu). Sinadaran nan kowane akwai kalan hasken da ya ke futarwa idan aka yi amfani da shi a cikin koyin.

Sannan matsi wato pressure gas din a cikin glass din koyin batada yawa. Amma idan wuta ta yi yawa gas din zai yi zafi sosai. Idan gas din ya yi zafi zai kara pressure a cikin glass din kaman yanda ka'idar take (a gas law). To idan pressure ta yi yawa a cikin koyin, glass din koyin zai fashe! Shi tungsten yayin da ya ji wutar lantarki ta na wucewa takanshi ya na saurin kamawa da wuta fiye da sauran transition metal 'yan uwanshi.

Koyin wuta ya na bayar da haskene a lokacin da current ta shigo cikinsa daga batiri ko generator. Haka kuma light bulb kowace kafa a jikinsa positive ce, kuma kowace kafa negative ce. Ma'ana shi duk ta inda ka jona masa wayar lantarki (wire) zai kawo wuta. Amma koyin wuta na zamani wato LED yanada kafa mai daukar positive daban, mai daukar negative daban.

LED ya samo asaline daga diode. Diode kuma abune wanda wutar lantarki ta ke wucewa ta bangare daya kadai zuwa dayan bangaren a cikinsa. Misali, idan wuta ta zo daga bangaren dama zai bari ta wuce zuwa hagu, amma idan wutar ta zo daga hagu ba ya barinta ta wuce zuwa bangaren dama. Wannan shiyasa idan ka jona LED ba daidai ba, wato positve a kafar negative, ko negative a kafar positve ba ya kawo wuta.

Shin ko ka san menene battery, da kuma amfaninsa?

Amma shi koyin wuta na gargajiya ya na barin wuta ta wuce ta ko wane bangare ta zo. Misali, idan wuta ta zo daga dama zai bari ta wuce ta hagu, hakama idan wutar ta zo daga hagu zai bari ta wuce ta je dama. Saboda shi ya na aikine kaman resistor. Bambancinsu anan shine LED ya na bukatar current kadan idan zai kawo wuta, yayin da koyin wuta na gargajiya ya ke bukatar current mai yawa kafin ya kawo wuta.

Koyin wuta na gargajiya ya na canza wutar da ta ke zuwa cikinsa gida biyu, wato zuwa zafi da haske. Kusan kaso casa'in (90%) na karfin wuta da ya ke samu ya na juyashi zuwa karfin zafi (heat energy) sauran kaso goma (10%) dinne kawai ya ke canzawa zuwa karfin haske (light energy).

Bambancin Voltage da Current
Idan aka ce 'voltage' ana nufin karfin wutar lantarki, ko kuma karfin lantarki. A phyisics kuma voltage ya na nufin karfin lantarki da ke jikin kowane charge. Ana auna voltage da wani ma'auni wanda ake kira 'voltmeter'. Idan kuma aka ce 'current' ana nufin adadin cajin (charges) da su ke wucewa a cikin wayar lantarki duk second daya. Sannan kuma ana amfani da 'ammeter' domin auna adadin wutar da ta ke wucewa duk second daya yayin da aka jona wani abu da batiri. Kuma ana rage current ta hanyar jona resistor a tsakanin batir da waya, ko kuma tsakanin koyi da batir. Electron wani abu ne mai matukar kankanta wanda ido ba ya iya ganinshi, kuma shine ya ke daukan adadin charge 1.6x10^-19C daga cikin sinadaran da ke kunshe a cikin batir, sannan ya shiga ta cikin wayar lantarki ya wuce zuwa cikin abun da aka jona wayar da shi kaman koyin wuta, abun caji (charger), ko fanka, ko talabijin da sauransu.

Ka karanta bayanin menene Electromagnetic radiation?

Lokacin da current ta ke wucewa akan filament a take za ka ga koyin ya kawo wuta. To abun da ya ke faruwa a lokacin shine current din ta na zuwa jikin filament nan take filament din zai yi zafi, ya canza, ya dawo kaman garwashi (ember) sai gas din cikin koyin musamman wadanda a lokacin su ke daidai kan filament za su fara konewa. Saboda haka sai electron din da ya dakko charge ya futar da kwayar haske guda daya wato 'photon' daga jikinsa. Daga nan ya bi ta daya kafar ya futa daga cikin koyin ya koma cikin batirin.

Daga nan sai photon din ya futo daga cikin koyin da matukar sauri fiye da saurin harbin bindiga. Photon shine ya ke dakko kwayar haske guda daya a cikinsa, ya shiga sarari, ya na tafiya, ya na haska waje har sai karfinsa ya kare. Electron kuma shi ya ke dakko charge daga cikin sinadaran cikin batir. Daga nan sai a fara ganin haske ya na futowa daga jikin koyin har sai lokacin da charge din batirin ya kare, ko kuma man generator ya kare, ko kuma aka dauke wuta sannan hasken koyin ya dauke. Wannan aikin cikin ikon Allah duk ya na faruwa a cikin kankanin lokaci wanda baikai kiftawar ido ba. Saboda haka dan Adam ba zai iya ganin yanda komai ya ke faruwaba.

Domin ci gaba da samun cikakkun bayanai, ko karin haske akan kimiyya da fasahar zamani a ci gaba da kasancewa da shafin nan. Za mu dakata anan da fatan ana amfanuwa da darusan kimiyya da fasaha wadanda mu ke rubutawa a shafin nan - mun gode.

Sannan duk mai tambaya, ya yi kasa ya je wajen comment ya rubuta mana ita. Mu kuma za mu amsa masa idan Allah ya sa mun sani. Daga karshe kuma mu na fatar sake ganinku tare da abokanku a shafin nan. Mun gode, a huta lafiya ;)

No comments

Powered by Blogger.