Menene Power Bank?

Idan mu ka yi la'akari da yanda mu ke amfani da wayoyinmu, za mu ga cewa su na bukatan abun caji na tafi da gidanka - wanda zai kasance ka na tare da shi a ko da yaushe. Domin yin wayarka caji kai-a-kai zai sa batirin wayartaka zai kasance ya na samun isashshen caji. Ka ga kenan batirinka zai kasance mai lafiya na tsawon lokaci kafin ya dena rike caji.

Idan batiri ya na samun isashshen caji zai kasance ya na rike caji. Sannan kai kanka hakan zai sa ka yiwa batirinka ganin sabo wanda bai jima ba. Kasancewa za ka yi wata tafiya ko za ka je wani waje wanda za ka bukaci waya a zamanin nan na kimiya da fasaha. To amma abun haushi ne lokacin da za ka yi wannan tafiya wayarka ta kasance a rufe, saboda babu caji.

Ko ka san yanda ake kula da batirin waya?

Ko ba komai idan ka isa wajen da za kaj e, za ka kira wanda ka je wajensa saboda ya sanar da kai yadda za ku hadu da sauran bayanai. Ko kuma yanayin aiki zai iya sawa wani lokaci mutum kasancewa a inda babu wutar lantarki wanda zai yi cajin wayarsa da ita. Domin magance wannan bukata da sauran irinta ka na bukatar 'power bank'.

Menene Power Bank?
Power bank wata karamar na'urace wanda nauyin ta baifi nauyin matsakaicin sabulu ba. Hakama girman ta baifi girman wayar smartphone ba. Power bank na'urace wanda ta kunshi karfin lantarki wanda ake cajin waya da shi ko da yake daga jin sunanta ana iya fahintar aikinta. Wannan na'ura ana amfani da ita wajen yiwa wayoyi caji yayin da babu watar lantarki a kusa.

Power bank shima caji ake masa kaman yanda ake yiwa waya. Sai dai shi daga baya cajin da aka yi masa za a dawo ayiwa waya caji da shi. Kunga kenan sunan shi ya yi daidai da aikin shi. Daman ance 'power' wato karfi, sannan kuma aka ce bank, wato asusu, a takaice ya na nufin asusun ajiye karfi (wato caji).

Ka karanta darasin menene compass kuwa?

Power bank ya na da amfani sosai ga masu amfani da wayoyi musamman a lokacin da babu wutar lantarki, ko kuma mutum ba ya cikin gari. Power bank bai da tsada idan aka duba amfaninsa, kuma yanada saurin cika waya idan mai kyaune. Sai dai shi baya cika da wuri idan aka sakashi a caji - saboda sai ya tattaro karfin da zai yi cajin wasu wayoyi.

Akwai power bank wanda ya ke amfani da hasken rana (sunlight) ya ke yiwa kansa caji. Daga baya sai ayiwa waya caji da shi. Bayan shi power bank din ya samu isashshen caji daga hasken rana. Kasancewa akwai power bank mai caja kanshi da hasken rana ko da babu wutar lantarki, wannan yanada dadi, saboda ko ba komai za ka na yin cajinshi a kyauta, kuma ka yi wayarka da shi.

Power bank na yanzu za ka samu mafi yawa su na zuwa da fitilar hannu (torch light) ko fitilar girke (lamp). Wacce ake amfani da ita a cikin duhu domin haske haske. Ka ga wannan ya na da amfani sosai, idan mutum ya na aiki a wajen da babu haske ko kuma duhu ya yi yawa.

Shin ko ka san yanda ake gyara waya idan ta fada ruwa?

A takaice dai power bank na'ura ce wanda ake yi mata caji domin ayi cajin wayoyi da ita a gaba. Kuma tanada amfani ga masu wayoyi musamman smartphones. Akwai power bank kala daban daban wato girma girma ne. Wani ya na iya yiwa wayoyi biyu caji, wani kuma waya daya kawai ya ke iya yiwa caji. Wani kuma ya na cajin wayoyi fiye da haka, wato dai ya danganta da karfinsa tare da kokarinsa.

Ya na da kyau a duk lokacin da ka saka power bank naka a caji ka barshi sai ya cika. Haka kuma dazarar ya nuna maka cewa ya cika, sai ka cire shi a cajin ka ajiyeshi, ya samu ya huta kuma ya yi sanyi.

A yau amfani da kayan lantarki ya zama jiki ga al'umma. Saboda haka ya na da kyau a kiyaye ka'idojin yanda ake amfani da su. Shiyasa kamfonin da su ke kera wadannan abubuwan su ke rubuta ka'idojin yanda ake aiki da su. Idan ka lura a jikin kwalin abun za ka ga ka'idojin a rubuce. Amma ma fi yawa za ka samu wata takarda ta musamman wanda take kunshe da bayanan yanda ake aiki da wannan abun.

Bari mu tsaya anan musha ruwa, sai kuma wani darasin. Mu na fatan za ku cigaba da kasancewa da wannan shafin domin samun sabbin bayanai akan kimiyya da fasahar zamani.

Mun gode, sai mun sake ganinku.

No comments

Powered by Blogger.