Yanda Lithium ion battery ya ke aiki

Lithium ion battery shi ne batirin da ake aiki da shi a bangarorin fasaha daban daban kaman na'ura mai kwakwalwa, da wayar hannu da mota aiki da wutar lantarki, da satellite da sauransu. Wannan batirin ya na da kokari fiye da sauran, kuma bai cika daukan zafi kaman sauran ba.

Menene Lithium ion battery?

Lithium ion battery dayane daga cikin baturan da mu ke aiki da su a cikin na'urorin zamani. A kimiyyance akwai batura kala daban daban, wadanda ake aiki da su a bangarori daban daban na rayuwa. Wani batirin ana aiki da shi a mota da mashin, wani kuma a cikin agogon hannu da na'urar lissafi (calculator) ake aiki da shi, sannan kuma akwai wadanda ake aiki da su a cikin fitila, da rediyo, da agogon bango da sauransu.


Battery shine abun da ya ke samar da karfin lantarki (electrical energy) ta hanyar canza karfin sinadarai (chemical energy) da su ke cikinsa zuwa karfin lantarki. Lithium ion battery shine batirin da a yanzu babu wani batiri kamansa wajen aiki, da kokari, da kwari, da kuma karko. Haka kuma dayane daga cikin secondary cell, wato batirine wanda ake yi masa caji, kaman yanda ake yi wa sauran. Sannan kuma ba ya daukan zafi kaman yanda sauran baturan su ke yi.

Lithium ion battery shine batirin da za ka gani a cikin waya, da computer, da mota ko mashin na zamani mai amfani da wutar lantarki. Lithium ion battery ya na da nisan kwana fiye da sauran.


To amma ya ya lithium ion battery ya ke aiki?

Kafin mu fara bayanin yanda lithium battery ya ke aiki, za mu fara da bayanin sassansa.

Sassan jikin lithium ion battery

1. Aluminium foil
2. Copper foil
3. Cathode
4. Anode
5. Separator


1. Aluminium foil an hadashi da karfen dalma (aluminium) kuma shi ne ya ke aiki a matsayin bangaren positive na batirin din.


2. Copper foil shi kuma an hadashi da karfen copper, sannan shine ya ke aiki a matsayin kafar negative din batirin din.


3. Cathode shine positive, kuma shi ya ke bayan aluminium foil, sannan kuma an hada shi da sinadaran metal oxide da kuma sinadarin lithium.


4. Anode shine negative kuma ya na bayan copper foil, sannan an hadashi da sinadarin graphite wanda shima dayane daga cikin dangin sinadarin carbon.


5. Seperator shi ma wani foil ne wanda ya raba tsakanin cathode da anode. Kuma a lokacin da battery ya ke aiki ko caji electron ta cikinsa su ke wucewa, su yi sama, ko kasa.


Cathode da anode

Cathode shi ne bangaren positive charge, yayin da anode ya ke aiki a matsayin negative.


Yanda lithium ion battery ya ke karban caji

Lokacin da aka jona caji a jikin batir din electron za su fara zubowa daga bangaren metal oxide da lithium wadanda su ke bangaren aluminium foil su wuce ta cikin separator sannan su sauka a cikin graphite wanda ya ke bangaren copper foil. Duk electron din da ya sauka akan graphite sai graphite din ya rikeshi. Wannan aikin haka zai ta maimatuwa har sai adadin gurin zaman electron akan graphite ya cika, sannan batir din zai cika.

Bayan batirin ya cika, lokacin da aka fara amfani da shi electron din zai fara futowa daga graphite ya yi sama ya koma ya wuce ta cikin separator sannan ya futa ta metal oxide da lithium sannan ya tafi cikin waya ko computer ko wata na'ura da aka jona wannan batir din da shi.



Wannan shi ne bayanin yanda lithium ion battery ya ke aiki a takaice. Da fatan a na amfanuwa da darusan fasaha wadanda mu ke rubutawa a shafin nan. Domin ci gaba da samun bayanai game da fasahar zamani, sai a ci gaba da kasancewa da shafin nan.

Za mu dakata a nan da fatan za mu sake ganinku, duk mai tambaya sai ya yi kasa wajen comment ya rubuta. Mun gode, a huta lafiya.

No comments

Powered by Blogger.