Menene Geostationary satellite?
Geosynchronous satellite su ne satellite din da su ke kawo sadarwa gidajen talabijin din da su ke watsa shirye shiryensu ta kafar satellite. Wadannan satellite din su na cikin sarari daga can nesa, kuma su na tafiya mara sauri saboda sun yi nesa da duniya sosai.
Geostationary satellite ya na wajen duniya a matakin da ake kira geosynchronous orbit, wato daidai nisan kilomita dubu talatin da shida tsakaninsa da duniya. Mutumin da ya ke cikin duniya idan da zai iya hango geostationary satellite zai iya cewa satellite din a waje daya ya ke a tsaye, wato ba ya motsawa. Wannan shiyasa ma ake kiransa geostationary satellite.
Duk wanda ya ke kallon geostationary satellite daga cikin duniya zai yi tunanin cewa satellite din ba ya tafiya. Saboda satellite din ya na tafiya da saurin da duniya ta ke juyawa akan axis din ta wanda ta ke gamawa a kwana daya. Shima haka ya ke zagaye duniya. Lokacin da duniya ta ke juyawa shima a lokacin ya ke kewayeta, hakan zai sa a gansa kaman kasa.
Shi kuma geostationary satellite kowane guda daya zai kawo sadarwa ga kaso daya cikin uku na duniya, wato guda kadai sun isa su kawo sadarwa ga duniya baki daya. Inda su ke shi a cewa geosynchronous wato wajen za ka ga duk satellite din da ya ke za ga ye duniya ba ya sauri, idan aka kwatanta da wadanda su ke matan LEO ko MEO.
Kowane satellite kaman su GPS satellite, da Geosynchronous satellite su na aika bayanan sadarwa ta hanyar hasken da idon dan Adam ba ya iya gani, wato Radiowaves. Radiowaves daya ne daga ciki electromagnetic radiation - wadanda su ke tafiya a cikin sarari, kuma su na iya ratsa abubuwa masu kauri su wuce. Electromagnetic radiation su na tafiya ne da saurin haske (speed of light). Wato su kan yi tafiya mai nisan mita miliyan dari uku a duk second daya (300, 000, 000m/s).
Za mu tsaya a nan sai kuma idan mun zo da wani bayanin akan wata fasahar kuma. Idan ku na so ku san menene satellite ku shiga nan. Mu na fata ana amfuwa da bayanan da ake karantawa a shafin nan.
Mun gode da kawo ziyara shafin nan sai mun sake ganinku!
Menene Geosynchronous satellite?
Geosynchronous satellite, ko kuma geostationary satellite, satellite ne wanda ya ke daidai equator amma ya na can sama kuma akwai nisan kilomita dubu talatin da shida (36, 000km) a tsakaninsa da equator bayan an cire radius. Satellite ne wanda ya ke gama orbit nasa a cikin kwana daya (24hrs). Wato ya na tafiya kaman yanda duniya ta ke tafiya.Geostationary satellite ya na wajen duniya a matakin da ake kira geosynchronous orbit, wato daidai nisan kilomita dubu talatin da shida tsakaninsa da duniya. Mutumin da ya ke cikin duniya idan da zai iya hango geostationary satellite zai iya cewa satellite din a waje daya ya ke a tsaye, wato ba ya motsawa. Wannan shiyasa ma ake kiransa geostationary satellite.
Duk wanda ya ke kallon geostationary satellite daga cikin duniya zai yi tunanin cewa satellite din ba ya tafiya. Saboda satellite din ya na tafiya da saurin da duniya ta ke juyawa akan axis din ta wanda ta ke gamawa a kwana daya. Shima haka ya ke zagaye duniya. Lokacin da duniya ta ke juyawa shima a lokacin ya ke kewayeta, hakan zai sa a gansa kaman kasa.
Shi kuma geostationary satellite kowane guda daya zai kawo sadarwa ga kaso daya cikin uku na duniya, wato guda kadai sun isa su kawo sadarwa ga duniya baki daya. Inda su ke shi a cewa geosynchronous wato wajen za ka ga duk satellite din da ya ke za ga ye duniya ba ya sauri, idan aka kwatanta da wadanda su ke matan LEO ko MEO.
Kowane satellite kaman su GPS satellite, da Geosynchronous satellite su na aika bayanan sadarwa ta hanyar hasken da idon dan Adam ba ya iya gani, wato Radiowaves. Radiowaves daya ne daga ciki electromagnetic radiation - wadanda su ke tafiya a cikin sarari, kuma su na iya ratsa abubuwa masu kauri su wuce. Electromagnetic radiation su na tafiya ne da saurin haske (speed of light). Wato su kan yi tafiya mai nisan mita miliyan dari uku a duk second daya (300, 000, 000m/s).
Za mu tsaya a nan sai kuma idan mun zo da wani bayanin akan wata fasahar kuma. Idan ku na so ku san menene satellite ku shiga nan. Mu na fata ana amfuwa da bayanan da ake karantawa a shafin nan.
Mun gode da kawo ziyara shafin nan sai mun sake ganinku!
Leave a Comment