Yanda ake kirkiro sabon page a WordPress

Page shine wani shafi daga cikin shafukan wani website ko blog. Kuma akan kirkiri page domin abubuwa daban daban kaman tallata hajoji ko rubuta wata sanarwa. Wasu page din kuma ana budesu kaman shaguna ta yanda wani shiga ya yi siyaiya a cikinsu.

Duk wani website akan so ya kasance akwai page mabanbanta a cikinsa domin rubuta manufarsu, ko ka'dojin aiki da su, da kuma rubuta adreshinsu ko kuma bayar da wajen rubutu wanda mai kawo ziyara zai iya tuntubar mai shafin ko masu shafin.

WordPress shi ma ana bude shafi a cikinsa ta yanda za a tafiyar da shi kaman yanda ake bukata.

Ga yanda ake kirkiron sabon page a WordPress

1. Wannan tutorial din kaman ci gabane akan yanda ake install din plugin a WordPress, saboda mun faro bayanin ne tun lokacin mu ka yi install din plugin a tutorial din da ya wuce. Bayan ka gama activating na plugin din, sai ka taba shi.


2. Ka na taba shi za ka ga an kawoka cikin plugin din, sai kasa ka shiga Settings.


3. Ka na shiga cikin Settings din za ka ga Edit da Duplicate a kasa da sunan plugin din. Sai ka shiga Edit.


4. Ka na shiga za ka ga wasu code kaman haka [contact-form-7 id="48" title="Contact form 1"], sai ka kwafo (copy) code din. Amma wajen da mu ka rubuta "48" misaline mu ka yi ka na iya samun wata lambar daban ba wanda mu ka rubuta ba.


5. Idan za ka yi copy din sai ka taba code din ka rike, za ka ga COPY, da SHARE, da SELECT ALL, da kuma WEB SEARCH sun baiyana, sai ka taba COPY, sannan sai ka sake taba Save.


6. Ka na kwafo wadancan code din sai ka dawo dashboard, ka taba Pages.


7. Ka na taba Pages, za ka ga All Pages, da Add New sun baiyana a karkashinsa, sai ka shiga Add New.


8. Ka na shiga Add New za ka ga an kawoka wajen da ake kirkiran sabon page. A wajen za ka ga Add title, da Start writing or type/to choose a block.


9. Daga nan sai ka shiga Add title, ka rubuta sunan page din. Daman za mu kirkiro page din contact us ne, misali mun rubuta Contact us. Sannan sai ka shiga Start writing or type/to choose a block ka rubuta bayanan da za ka rubuta a page din, amma tunda za mu yi misali da page din contact us ne sai ka taba wajen rubutun ka rike za ka ga PASTE ya baiyana sai ka taba shi.

10. Bayan ka taba PASTE din za ka ga wancan code din da ka kwafo a farko ya baiyana a wajen, sai ka yi sama ka taba Publish.


11. Ka na taba Publish din za ka ga Preview, da Publish... da kuma wani Publish din sun sake baiyana, sai ka taba Publish na ukun wato na kasan.


12 Ka na taba Publish na karshen sai ka dan jira ya gama loading. Ya na gamawa sai nuna maka Published, ka duba za ka ga Preview sai ka shiga domin ganin page.

Wannan su ne matakan da ake bi idan za a bude sabon page a WordPress, kuma hanyar babu wahala, indai ka nutsu.

2 comments:

Powered by Blogger.