Menene Pixels?

Shin ko ka san yanda screen din waya, da screen din computer, da kuma screen din talabijin na bango wanda ake cewa flat screen su ke kawo abubuwa da kaloli daban daban?

Screen din flat screen, da na manyan wayoyi, da kuma na computer a baya su na aiki da fasahar da ake kira 'Liquid Crystal Display' ko kuma 'LCD' a takaice. Amma a yanzu da sabuwar fasahar 'OLED' wato 'Organic Light Emitting Diode' su ke aiki. Wannan ya zo ne bayan da wasu masana su uku masu bincike a bangaren kimiyyar Physics su ka gano cewa ana iya ganin shudin haske a cikin screen a shekarar 2014. Wannan bincike da gano ana iya ganin shudin haske da su ka yi, ya sa aka basu lambar yabo ta Novel a bangaren kimiyyar Physics ta 2014.

Shin ko ka karanta bayanin bambacin manhajar Android OS, da manhajar iOS ta iPhone da iPad?

Sannan wayoyi da sauran na'urori masu amfani da fasahar LCD a screen din su, aka fara kerasu da fasahar OLED daga 2018. Bari dai mu dawo bayanin pixels, kafin mu yi nisa a bayanin, idan ka ji ance 'mega' ana nufin miliyan. Kenan idan aka ce 'mega pixel' ana nufin pixel guda miliyon. Idan mu ka lura za mu ga jikin kyamarorin wasu wayoyi za mu ga an rubuta 5MP, wato 5 Mega Pixels, wasu kuma 8MP, wato 8 Mega Pixels, a wayoyin zamani akwai masu 16MP, wato 16 Mega Pixels, da sauransu. Idan ka ga 5MP ana nufin kyamarar tana da pixel miliyan biyar, 8MP kuma pixel miliyan takwas, sannan 16MP shine pixel miliyan goma sha shida.

Pixel wani dan karamin abu ne a cikin screen din waya, ko flat screen. Pixel yana da matukar kankanta, domin gashi daya na mutum yana da girman micrometre sittin zuwa saba'in (60-70μm). Pixel kuma yanada tsayin micrometre daya da digo sha biyu (1.12μm), hakama fadinsa ya ke wato fadin micrometre daya da digo sha biyu (1.12μm). Kowane pixel yana da girman micrometre daya da digo dubu biyu dari biyar da arba'in da hudu (1.2544μm). Idan aka ce 'micro' ya na daidai da idan karaba abu daya zuwa gida miliyon daya, abun da kowane gida zai samu shine micro. Kenan idan aka raba tsayin metre daya zuwa gida miliyon, kowane gida zai samu tsayin micrometre daya.

Shin ko ka karanta bayanin menene manhajar Android OS ta kamfanin Google?

Pixel dan karamine sosai kuma yana cikin screen din waya. Duk kankantarsa kowane daya yana dauke da launuka guda uku - kuma sune ja (red), da kore (green), da kuma shudi (blue). Wadannan launuka guda ukun sune su ke kawo duk wani hoto ko launi da kake gani a jikin screen. Sannan kowane daga cikin kalolin yana da lamba 255. Idan ka hadasu su uku gaba daya a lokacin da lambobinsu suke 255 za su bayar da farin kala.

Misali, idan kuma kowane daga cikinsu ya na matakin lamba 85, su ukun za su hadu, su bayar da launin ruwan toka. Idan kuma ja yana da 225, kore ma 255, sai shudi kuma 50, launin zai bada ruwan dorowa (yellow). Idan kuma ja yana da 255, kore ma haka 255, sai shudin shine 25, za su bada launin rawaya mai haske (light yellow). Idan kuma ja ya na 50, kore da shudi kuma 255, za su bayar launin kore mai duhu (dark green).

Wadannan lambobin da ake bawa kowane launi a cikin launuka guda uku da suke cikin pixel, su na zuwane daga injin waya ko computer. Kowane pixel ya na samun karfin da ya ke nuna launi daga injin wayar ko computer. Saboda haka miliyoyin pixel ne su ke taruwa su hada hoto ko rubutun da mu ke gani a cikin screen. Kowane pixel akwai adadin karfin da ya ke samu sannan su hadu su bayar da hoton da mu ke gani a cikin screen.

Shin ko ka karanta bayanin menene manhajar iOS ta kamfanin Apple?

Domin ci gaba da samun cikakkun bayanai, ko karin haske akan fasahar zamani a ci gaba da kasance da shafin nan. Ina ga za mu dakata anan da fatan ana amfanuwa da darusan kimiyya da fasaha wadanda mu ke rubutawa a shafin nan - mun gode.

Sannan duk mai tambaya, sai ya yi kasa wajen comment ya rubuta ta. Mu kuma za mu amsa masa idan Allah ya sa mun sani. Daga karshe kuma mu na fatar sake ganinku tare da abokanku a shafin nan. Mun gode, a huta lafiya😀

No comments

Powered by Blogger.