Bambancin iPhone (iOS) da Android (OS)
Wayoyin iPad da iPhone na kamfanin Apple, da wayar Android ta kamfanin Google, su ne wayoyin da a yanzu aka fi amfani da su a duniya. Kaman yanda wani bincike ya nuna a yanzu daya bisa uku (⅓) na mutanen duniya su na amfani da manyan wayoyi daga iOS zuwa OS.
Android wayar tafi-da-gidankace wacce take aiki akan tsari ko fasaha ko manhajar operating system (OS) kaman iPhone da iPad. Sannan su Android kamfanin Google ne ya ke kerasu, yayin da iPhone da iPad kuma kamfanin Apple ne ya ke kerasu. Sannan akwai manyan wayoyin Android wadanda za a iya cewa abokan hamaiyar iPhone ne a yau. Wadannan wayoyin su ne Xperia X ta kamfanin Sony, da Nexus 5X, da Nexus 6 na kamfanin Google, da kuma Galaxy S7 ta kamfanin Samsung.
Shin ka karanta bayanin menene pixels?
Wayoyin iOS wato iPhone da iPad da kuma Android OS su na da wasu bangarori dadama da su ke kama da juna. Kaman wajen sarrafasu kowace a na taba glashinta ne idan za a shiga wani waje ko kuma za a futa daga inda aka shiga. Kowacce za ka samu screen dinta a cike ya ke da application. Sannan dukansu su na nuno sanarwa daga can saman screen dinsu a kusa da batirinsu. Sannan wajen kawo sanarwarsu a na iya jawoshi daga sama zuwa kasa domin karanta bayanin da ya shigo wayar.
Kamfanin Apple da Google su kan sabunta manhajojinsu ta hanyar kawo sabbin bangarori lokaci-bayan-lokaci. Wayoyin iOS da Android OS su na kara samun sabbin tsaruka da kuma fadada bangarori da manhajojinsu. Duk bayan wani lokaci kamfanonin nan su kan fito da sabuwar manhaja - kaman yanda Google su ka kawo sabuwar manhajarsu mai suna Marshmallow, wato version 6, a shekarar 2016, su ma haka Apple sun kawo sabuwar manhajarsu mai suna iOS 10 a watan satumba na shekarar 2016. Duk lokacin da kamfanonin nan su ka kawo sabuwar manhaja su kan sanar da masu amfani da wayoyinsu. Haka kuma sabuwar manhajar ta na maye-gurbin tsohuwar manhajar da ake aiki da ita.
Sannan kowace ta na da rumbun wasanni wanda ake samun application din ta a cikinsa. Misali, Android nata shine Play Store, su kuma iOS wato iPhone da iPad nasu rumbun shine App Store, kowace a cikinta za ka samu rumbunta. Sannan application din daya ba ya aiki a daya. Sai dai mu ce application din Android ya fi saukin samu akan na iPhone da iPad.
Shin ko ka san yanda karamin jirgi mara matuki (drone) ya ke aiki?
Wannan ya sa za a iya cewa iOS ba sa saurin samun kwayar-cutar na'ura wato virus, kaman yanda wayoyin Android su ke saurin kamuwa. Hakika virus ya na iya shafar iOS, kaman yanda ya ke shafar Android - sai dai an fi samun matsalar shafar virus a wayoyin Android akan iPhone da iPad. Shi ya sa ake so mutum ya saukar da duk application din da zai yi amfani dasu daga rumbun wasanni na wayarsa wanda ta zo da shi a hukumance.
Shin ko ka san menene computer?
Wayoyin kamfanin Apple su na da tsada fiye da wayoyin Android. Saboda haka a na iya cewa wayoyin iPhone da iPad sai 'yan boko 😂 ko da ya ke kowa ma zai iya amfani da su idan ya samu halin mallakarsu. Akwai wayoyin Android masu tsada kaman Samsung wadanda ake ganin cewa abokan hamaiyar iPhone ne wadanda mu ka kawo sunansu a sama.
Za mu dakata a nan - da fatan a na amfanuwa da darusan fasaha wadanda ake karantawa a shafin nan. Sannan kuma ku na iya rarraba wannan bayanin ga abokanku a shafukan sada zumunta da muhawara na internet.
Daga karshe kuma mu ke cewa duk wanda ya ke da tambaya, kofa a bude ta ke, sai ya yi kasa wajen comment, ya rubuta mana ita, zai samu amsa insha Allahu. Mu na godiya, da fatan za mu sake ganinku, a huta lafiya. ✋
Android wayar tafi-da-gidankace wacce take aiki akan tsari ko fasaha ko manhajar operating system (OS) kaman iPhone da iPad. Sannan su Android kamfanin Google ne ya ke kerasu, yayin da iPhone da iPad kuma kamfanin Apple ne ya ke kerasu. Sannan akwai manyan wayoyin Android wadanda za a iya cewa abokan hamaiyar iPhone ne a yau. Wadannan wayoyin su ne Xperia X ta kamfanin Sony, da Nexus 5X, da Nexus 6 na kamfanin Google, da kuma Galaxy S7 ta kamfanin Samsung.
Shin ka karanta bayanin menene pixels?
Wayoyin iOS wato iPhone da iPad da kuma Android OS su na da wasu bangarori dadama da su ke kama da juna. Kaman wajen sarrafasu kowace a na taba glashinta ne idan za a shiga wani waje ko kuma za a futa daga inda aka shiga. Kowacce za ka samu screen dinta a cike ya ke da application. Sannan dukansu su na nuno sanarwa daga can saman screen dinsu a kusa da batirinsu. Sannan wajen kawo sanarwarsu a na iya jawoshi daga sama zuwa kasa domin karanta bayanin da ya shigo wayar.
Kamfanin Apple da Google su kan sabunta manhajojinsu ta hanyar kawo sabbin bangarori lokaci-bayan-lokaci. Wayoyin iOS da Android OS su na kara samun sabbin tsaruka da kuma fadada bangarori da manhajojinsu. Duk bayan wani lokaci kamfanonin nan su kan fito da sabuwar manhaja - kaman yanda Google su ka kawo sabuwar manhajarsu mai suna Marshmallow, wato version 6, a shekarar 2016, su ma haka Apple sun kawo sabuwar manhajarsu mai suna iOS 10 a watan satumba na shekarar 2016. Duk lokacin da kamfanonin nan su ka kawo sabuwar manhaja su kan sanar da masu amfani da wayoyinsu. Haka kuma sabuwar manhajar ta na maye-gurbin tsohuwar manhajar da ake aiki da ita.
Sannan kowace ta na da rumbun wasanni wanda ake samun application din ta a cikinsa. Misali, Android nata shine Play Store, su kuma iOS wato iPhone da iPad nasu rumbun shine App Store, kowace a cikinta za ka samu rumbunta. Sannan application din daya ba ya aiki a daya. Sai dai mu ce application din Android ya fi saukin samu akan na iPhone da iPad.
Shin ko ka san yanda karamin jirgi mara matuki (drone) ya ke aiki?
Shin iOS ta fi Android OS tsaro?
Tabbas! iOS ta fi Android tsaro. Idan aka kwatanta manhajoji ko fasahohi biyun a na iya cewa iOS tsarinta a rufe ya ke, yayin da na Android za a iya cewa a bude ya ke. Saboda ba za ka iya install din application a iPhone ko iPad wanda kamfanin Apple bai tabbatar da shi ba. Android ma ta na da irin wannan tsarin, amma ita a na iya install din application din da aka samo ba daga Play store ba. Sai dai kawai za su yi ma gargadin cewa wannan application din da za ka yi install dinsa, ba su san daga ina ya ke ba. Kenan duk illar da application din ya yi wa wayarka ba su da alhakinka.Wannan ya sa za a iya cewa iOS ba sa saurin samun kwayar-cutar na'ura wato virus, kaman yanda wayoyin Android su ke saurin kamuwa. Hakika virus ya na iya shafar iOS, kaman yanda ya ke shafar Android - sai dai an fi samun matsalar shafar virus a wayoyin Android akan iPhone da iPad. Shi ya sa ake so mutum ya saukar da duk application din da zai yi amfani dasu daga rumbun wasanni na wayarsa wanda ta zo da shi a hukumance.
Shin ko ka san menene computer?
Wayoyin kamfanin Apple su na da tsada fiye da wayoyin Android. Saboda haka a na iya cewa wayoyin iPhone da iPad sai 'yan boko 😂 ko da ya ke kowa ma zai iya amfani da su idan ya samu halin mallakarsu. Akwai wayoyin Android masu tsada kaman Samsung wadanda ake ganin cewa abokan hamaiyar iPhone ne wadanda mu ka kawo sunansu a sama.
Za mu dakata a nan - da fatan a na amfanuwa da darusan fasaha wadanda ake karantawa a shafin nan. Sannan kuma ku na iya rarraba wannan bayanin ga abokanku a shafukan sada zumunta da muhawara na internet.
Daga karshe kuma mu ke cewa duk wanda ya ke da tambaya, kofa a bude ta ke, sai ya yi kasa wajen comment, ya rubuta mana ita, zai samu amsa insha Allahu. Mu na godiya, da fatan za mu sake ganinku, a huta lafiya. ✋
Leave a Comment