Menene Computer (na'ura mai kwakwalwa)?

Kama daga wasan na'ura, da kallon bidiyo, da sauraron wakoki, da daukar hotuna - zuwa aiyukan makaranta kaman karatun littafi, da lissafi, duk aiyukane da za ka iya yi da computer guda daya. Computer abace mai matukar amfani a fasahar zamani da harkokin rayuwar al'umma ta yau da kullum. Computer a zamanin nan ta yi yawa kuma ana samunta a bangarori dadama na harkokin rayuwa. Akwai computer kala kala, kaman ta girke (desktop), da ta kan cinya (laptop), da ta tafin hannun (palmtop) da sauransu.

Amfanin computer yana da yawa. Kaman a bangaren kiwo lafiya ana amfani da ita wajen dubawa da kuma daukar hoton cikin majinyaci. Likitoci da masana kiwon lafiya su na amfani da wata na'ura domin auna zafin jikin majinyata - da kuma na'ura auna jinin mutum da fitsari da sauransu. A bangaren sufuri ma ta na nan a fage dadama kaman tukin jirgin sama, da kuma mota mara matuki, da sadarwa tsakanin matukan jirgin sama da abokan aiyukansu na tashohin jiragen sama daban daban. Hakama a tashohin jiragen sama ana amfani da ita domin bincika kayan matafiya.

A fannin tsaro ma ana amfani da computer domin gano abubuwan ciki jaka, ko akwati. Akwai jiragen yaki marasa matuka (drone) wadanda ake amfani da su domin tattara bayanan sirri akan abokan hamaiya da 'yan ta'adda. Har ila yau wadannan jirage ana amfani da su wajen kai hare hare kan 'yan tada kayar baya.

Shin ko kasan menene manhajar Android (OS)?

Bayan nan akwai na'urorin da ake amfani da su wajen auna yanayin duniya, da auna nauyi, da kuma auna saurin tafiyar abubuwan sufuri kaman, babur, ko mota, ko jirgin kasa, ko na sama - da sauransu. A takaice dai computer komai da ruwankace. A zamanin nan computer ta kawo sauki wajen aika sakonni da kuma sada zumunci.

Computer a yau ana amfani da ita wajen bincike, da tsarawa ko rubuta littafi, tare da wallafashi. Kuma ana shiga internet da ita a yi karatu, ko a sada zumunci, ko a yi cinikaiya, ko kuma dai wasu hidimomin. Idan na ce computer ina nufin hadda waya, da na'urar lissafi (calculator), da game na talabijin ko na wasan yara.

Gaba daya wadannan aiyukan da mu ka lissafo wanda mu ka ce computer ta na yinsu, tabbas! ta na yinsu, da bangarorinta. Computer tana da bangarori guda biyu, kuma ga su nan kaman haka:
1. Software
2. Hardware

Shin ka na son koyan hada application din Android a waya da kanka?

1. Software
Kaman yanda mu ka yi bayanai a sama, computer ta na aiyuka masu matukar yawa da kuma amfani. Wasu aiyukan kaman yin game, ko kallon fim iyaka a cikin computer ake ganinsu, ba a ganinsu a zahirance wato kaman yanda ake ganin littafin da aka wallafa. Software bangarene na computer wanda ake ganinsa, kuma ake aiki da shi a cikin computer, sannan kuma ba a iya ganinsa a zahirance balle a tabashi. Misalin software shine kamansu Microsoft office, da su Adobe reader, da su Photoshop da sauransu.

2. Hardware
Hardware shine bangaren computer wanda ake iya gani a zahirance kuma a taba. Misalin hardware shine duk abun da za ka gani kuma ka tashi, sune keyboard, da printer, da scanner, da camera, monitor, da speaker da makamantansu.

Wadannan bangarori guda biyu na computer su na aiki da junansu. Ta yanda daya zai umarci daya ya yi aiki, kuma dole sai ya yi wannan aikin. Na ce daya ya na umartar daya ya yi wani aiki. Misali, idan ka rubuta littafinka, sai ka yi amfani da printer domin wallafa shi zuwa littafi wanda za a iya gani, a taba, kuma a karanta.

Misali na biyu kuma idan za ka dauki hoto, za ka yi amfani da hardware wato camera, sai ka dauki hoton da ita, sannan ta umarci wata software a cikin computer ta ajiye wannan hoton a cikin computer. Kun ga kenan aikin nasu cudeni in cudeka ne wato vice-versa a turance.

Shin ko ka san menene Battery?

Yawaitar computer a zamanin nan ya kawo sauki wajen yaduwar ilimin kimiyya da fasaha. Za mu tsaya anan da fatan ana amfanuwa da bayanan kimiyya da fasaha wadanda ake samu a shafin nan. Muna fatan za ku ci gaba da kasancewa da shafin nan domin bamu gwarin gwuiwa. Duk mai son yin tambaya, ya na iya rubuta mana ita a wajen comment da ke can kasa.

Mu kuma za mu bayar da amsa idan Allah yasa mun san amsar tambayar. Mun gode sai mun sake ganinku, a huta lafiya!

No comments

Powered by Blogger.